DUNIYA MAKARANTA
Fitowa ta 15
71. Da dare kowa yana rufe kofarsa ne don tsoron mutane. A lokacin ne kuma Allah ya ke bude kofofinsa don karbar mutane. Ko kana kwankwasa kofarsa ta hanyar salloli da zikiri daa addu'oi da tilawa a wannan lokaci?
72. Kada jin dadin wani ya tsone ma ido. Ba ka saan abin da ya rasa ba kafin Allah ya ba shi ni'imar da yake cikin ta. Kada damuwarka ta tada hankalinka. Ba ka san alherin da za ta jawo ma ka ba. Hakuri maganin zaman duniya.
73. Idan ka makara wajen aiki kana jin kunyar shugabanka. Idan ka makara zuwa masallaci ko kana jin kunyar Allah?
74. Idan yaro ya yi wayo kyawonsa a sa shi makaranta. Idan ya girma kyawonsa a gan shi a masallaci. Macce ita kuma kimarta idan ta girma tana a gidan mijinta.
75. Kamilin mutum shi ne wanda ya tara ababe guda uku: Ga kyauta, ga dadin zama, ga kuma yawan ibada.
Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto
20/10/1438
14/7/2017
» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743

0 comments:
Post a Comment