Alamimin shafar aljanu - Zauren fiqhu ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Wednesday 11 October 2017

Alamimin shafar aljanu - Zauren fiqhu

ALAMOMIN SHAFAR ALJANU
********************************
Yadda zaka gane cewa Aljanu sun shafeka, ko kuma sun shafi waninka.

Duk wanda yake biye da ZAUREN FIQHU zai ga wani lokacin muna yin zurfafan bayanai game da lamarin Shaitanun Aljanu masu shiga jikin Bil Adama, har wasu suna ganin kamar ba haka bane.

Amma daliban ZAUREN FIQHU na whatsapp sun sha saurarar Audio na wasu rukiyyoyin da aka gabatar anan..

Yau kuma in sha Allahu zaku ji bayanin alamomin da ake gane shafar Aljanu ajikin mutum.

Wadannan alamomin sun kasu zuwa gida biyu. Akwai na fili, akwai kuma wadanda bassu faruwa sai alokacin barci.

ALAMOMIN 'BOYE:
********************
1. Bushewar idanu : Zaka ga mutum ya kwanta akan shimfidarsa amma barcin ba zai zo masa ba, sai Chan tsakiyar dare ko kuma wajen Asubah.

2. Yawan farkawa daga barci A FIRGICE!! . Wani zaka ga kusan duk minti talatin sai ya farka, ko Qasa da haka.

3. DANNAU: Mutum yana kwance zai ji wani  BAQIN ALJANI yazo ya danneshi. Zai yi ta EEHU!!. Amma babu mai jinsa.. Wani lokacin wasu sunfi yinsa da safe bayan sallar asubah.

4. MAFARKAI MASU FIRGITARWA: Kamar kayi mafarkin an biyoka za'a yanka ka, ko kuma mafarkin fadowa daga wani tsauni, ko kuma kaga hallaka Qarara, idan ka farka zaka ji jikinka duk zuffa!.

5. MAFARKIN NAMUN DAJI : Ganin miyagun dabbobi amafarki kamar macizai, Karnuka, Kyanwa, Rakumi mai fada, Damusa, Saniya, 'Bera, suna bin mutum zasu kamashi. etc.

6. Tauna acikin Barci. (kaji mutum yana barci amma yana taune-taune).

7. Dariya ko Kuka, ko Eehu acikin barci.

8. Kaga mutum yana barci amma ya tashi tsaye yayi tafiya, sannan ya dawo ya kwanta alhali ko farkawa bai yi ba.

9. Mafarkin afkawa cikin ruwa, ko Jini, ko wani mummunan rami.

10. Mafarkin Matattu, ko ganinka a MAQABARTA, ko wajen yanka dabbobi, ko kwata, ko Juji, ko tsakiyar Daji mai duhu.

11. Mafarkin Gajerun Mutane, ko dogaye tsola-tsola. Ko farare Sol, ko bakake WULUK, masu ban-tsoro.

12. Mace ta rika yin Mafarkin wani namiji yana zuwa yana saduwa da ita, bisa siffar Mijinta, ko saurayinta, ko mahaifinta, ko dan uwanta, etc.

13. Namiji ya rika mafarkin wadansu mata suna zuwa masa suna kwanciya dashi.

ALALOMI NA FILI
*******************
1. CIWON KAI : Marar jin magani. Ko an sha magani ba zai dena ba. Kuma gobe ko jibi ma sai ya dawo.

2. FADUWAR GABA : Kaji Qirjinka yana bugawa FAT! FAT!! FAT!!! (kamar zai fashe).

3. JUYARWA daga bin Allah ko duk wani abinda ya shafi addini kamar Zikirin Allah, karatun Alqur'ani,  da sauran abinda Allah yake so, kai kuma sai kaji baka so.

4. BAQIN CIKI : Haka kawai babu wani dalili sai kaji ranka yana ta baci, kana jin haushin kowa da kowa ba tare da wani dalili ba.

5. RIKICEWAR TUNANI: Kaji kamar komai ya chabe maka. Ka rasa yadda zakayi.

6. Rashin lafiyar wata ga'ba.  Amma likitocin zamani sun gama bincike sun kasa ganowa ko magance chutar.

7. Rikicewar Jinin haila.  Rashin zuwansa akan lokaci ko kuma zuwansa fiye da kima.

8. Yawan zubewar Juna-biyu. Ko kuma rashin samunsa kwata-kwata.

9. Jin tafiyar kiyashi ajikinka ko yaushe.

10. Jin maganganu masu tsoratarwa ba tare da kaga mai maganar ba.

11. Jin tsananin sha'awar aikata sabon Allah. Kaji kamar ana ingizaka.

12. Yawan mantuwar karatu, ko rashin fahimtarsa. Wato toshewar basira, alhali da chan ba haka kake ba.

13. Yawan jin waswasi ko kokonto ayayin tsarki ko alwala ko Sallah.

14. Yawan Kuka ko dariya ba tare da wani dalili ba.

15. Jin Kasala mai tsanani tare da nauyin jiki.

16. Tsoron shiga cikin jama'a, ka rika jin kamar zasu hallaka ka, alhali kuma ba haka bane.

17. Idan kina tafiya ki rika jin kamar wani yana binki a baya.

18. Yawan Qiyayyar juna atsakanin ma'aurata. Idan mijinki baya nan kiji kina mutukar sonsa. Amma da zarar ya dawo sai ki rika ganinsa kamar dodo, ki rika jin baki son ganinsa ko jin maganarsa.

19. Ciwon ciki ko baya, ko Qafa duk alokaci guda kaji kamar ciwon yana yi maka yawo ajikinka. Kuma ko anyi scanning ba za'a ga komai ba.

20. Kaikayin farji, ko Kuraje, ko fitar farin ruwa. Amma ko an sha magani ba ya denawa.

21. Jin zafi alokacin saduwa, ko daukewar Ni'ima, bushewar gaba, etc.

22. Son zama acikin BANDAKI, ko agaban dustbin, ko Juji (bola) ko kuma wani wajen Qazanta.

Idan kana fama da alamomi guda biyu ko uku ko sama da haka, kuma kana bukatar taimako, zaku iya tuntubar ZAUREN FIQHU kai tsaye don samun shawarwari ko magunguna ta wannan lambar 07064213990, 08163621213


Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support