*WANE NE YA KARYATA HADISIN SIHIRI?*
Rubutun: Dr. Mansur Sokoto
12 Shawwal 1438H
5 ga Yuli 2017
*Bismillahir Rahmanir Rahim*
Babu shakka magabata sun yarda da Hadisin Uwar Muminai A'isha (RA) cewa, Labid bayahude ya yi ma Annabi (S) sihiri. Kuma wannan ya yi tasiri a kan sa har yana ganin kamar ya yi wani abu alhalin bai yi shi ba. Ko kuma ya ga kamar ya zo ma iyalansa alhalin bai zo masu ba. Kuma Allah ya yi masa maganin wannan daga baya, ya ba shi lafiya sannan ya nuna masa inda aka rufe sihirin.
Daga cikin malaman da suka ruwaito Hadisin daga uwar Muminai akwai:
*Imam Ahmad a Musnad* (24741, 24804, 24851, 24852 da 25851)
*Imam Al-Bukhari a Sahihinsa* (3268, 5763, 5765, 5766 da 6391)
*Imam Muslim a Sahihinsa* (5667)
*Ibnu Majah a Sunan* (3545)
*Ibnu Hibban a Sahihinsa* (6703 da 6704)
*Abu Ya'la a Musnad nasa* (4757)
*Imam Al-Baihaqi a Dala'il An-Nubuwwa* (3018).
Ban da ta hannun Nana A'isha (R) kuma Hadisin ya zo ta hanyar Sahabi *Zaid bn Arqam (R)* a cikin littafin *Musnad na Imam Ahmad* (19481) da *Sunan na Nasa'i* (7/103) dss.
Malaman nan duk da suka ruwaito shi babu wanda ya yi suka ga maruwaitansa ko abinda suka ruwaiton. Wadanda ba su ruwaito shi ba ma - kamar Imam Malik, wanda ya takaita Muwaddarsa ga wani rukuni kebantacce na Hadisai - babu wanda ya yi suka gare shi daga cikin su. Amma *_"Mutakallimun"_* yan hauragiya su ne suka soke shi, malaman Sunna kuma ko waiwayarsu ba su yi ba.
Ibnul Qayyim (RH) ya hikaito maganar *Mutakallimun* - wadanda suka hada da Mu'utazila da yan Falsafa masu bin son zuciya da jefa nassi daga Manzon Allah (S) a *Bola*. Suka ce wai, ba su yarda da Hisham bn urwa da ya riwaito shi ba. Ga ta'alikin da Ibnul Qayyim ya yi a kai:
"وهذا الذي قاله هؤلاء مردود عند أهل العلم ؛ فإن هشاماً من أوثق الناس واعلمهم ، ولم يقدح فيه أحد من الأئمة بما يوجب رد حديثه ، فما للمتكلمين وما لهذا الشأن ؟! و قد رواه غير هشام عن عائشة ، وقد اتفق أصحاب الصحيحين على تصحيح هذا الحديث ، ولم يتكلم فيه أحد من أهل الحديث بكلمة واحدة ، و القصة مشهورة عن أهل التفسير و السنن و الحديث و التاريخ و الفقهاء ، وهؤلاء أعلم بأحوال رسول الله و أيامه من المتكلمين.
Ya ce: "Wannan maganar da wadancan suka fada ba abar karba ba ce a wurin masu ilimi. Domin Hisham (Ibn Urwa; wanda ya ruwaito Hadisin) yana daga cikin mafi amincin mutane kuma mafi ilimi a cikin su. Babu kuma wani shugaba a fagen ilimi da ya soke shi da abinda zai sa a mayar da Hadisinsa. To ina ruwan yan hauragiya da wannan lamari! Sannan kuma ba Hisham ne kadai ya ruwaito shi daga A'isha (RA) ba. Shaihunan Hadisi masu littafai biyu ingantattu ma (Bukhari da Muslim) sun hadu a kan inganta wannan Hadisi. Babu kuma wani malamin Hadisi da ya taba furta wata kalma daya ta sukar Hadisin. Ban da wannan kuma, labarin ya shahara a wurin malaman Tafsiri da masu littafan Sunan (Irin su Tirmidhi da Nasa'i dss) da sauran malaman hadisi da na Tarihi da na Fiqihu. Wadannan kuwa sun fi yan hauragiya sanin yanayin Manzon Allah (S) da tarihinsa.
Duba: Bada'i' At-Tafsir (5/407).
*Maganar Ibnu Uyayna* (RH) da ya ce:
"وهذا أشد ما يكون من السحر إذا كان كذا"
Wadda Dr. Gummi yake ganin Allah ya tayar da shi a wannan zamani don ya fassara ta bayan duk daruruwan shekarun da suka gabata ba a fassara ta ba, a wurin malamai masanan Harshen larabci ba jumla mai rikitarwa ba ce. Abinda take nufi: "Wannan shi ne mafi tsananin yanayin da sihiri ke sa mutum, idan ya kai haka".
_*Sufyan ba ya shakkar Hadisin*_ kamar yadda sauran malamai tsararrakinsa da magabatansa da na bayansa - wadanda hankulansu suke daidai da Shari'a - ba su shakkar Hadisin kuma ba su ganin wata aibantawa ga darajar Manzon Allah (S) a cikin sa.
*Allah ya yi mana garkuwa daga bata da bin son zuciya.*

0 comments:
Post a Comment