DUNIYA MAKARANTA
Fitowa ta 14
66. Sirri kamar dafi yake a cikin zuciyar Macce. Idan ba ta fito da shi sai ya kashe ta.
Yana da kyau ka san inda za ka boye asirinka!.
67. 'Yan uwan Annabi Yusuf sun yi niyyar kashe shi, Allah bai kashe shi ba. Sun so su kaskanta shi, Allah ya daukaka shi. Su ka batar da shi don mahaifinsu ya manta da shi, ya daina son sa, amma sai Allah ya kara masa son sa. Aka sayar da shi a matsayin bawa amma ya zama Sarki. Kada ka damu da sharrin dan Adam. Allah gatan Bawa.
68. Akwai miliyoyin halittun ubangiji wadanda ba su da aljihu, ba asusun ajiya a gida ko a banki. Amma ba su daina cin arziki ba. Kwantar da hankalinka. Arzikinka yana nan ba zai wuce ka ba. Nemi halaliya, don ba ka wuce arzikinka. Saurin nema ba ya kawo samu.
69. A Hotel ake rubuta cewa, "idan mun burge ka ka fada ma duniya. Idan mun bata ranka ka fada mana". Wannan shi ne yadda ya kamata ka yi hulda da kowane musulmi dan uwanka.
70. Abu daya ne kyakkyawa wanda ko makaho yana iya ganin sa. Shi ne kyawon hali. Ka zama mai kyawon hali ba sai ka fadi ba mutane da kansu za su yabe ka.
Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto
19/10/1438
13/7/2017
» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743

0 comments:
Post a Comment