~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Friday 7 July 2017

*HUKUNCIN SALLAR QASRU-4!!!???*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Taken Lekca........
.
*SALLAR QASRU!!!!??*
.
Wannan shine bayani na hudu****
.
Cigaba***
.
_Ibn Nasir Assa,ady acikin tafsirinshi yace: Idan aka duba wancan sabanin nafarko damukayi magana na cewa shin qasru dole ne ko ba dole bane? Sa'ady yace: Abinda yafi dacewa shine duk wanda yayi yafiya kawai yayi kasaru, wannan yafi dacewa da sunnah, saboda kakaf malamai da masu cewa dole ne, da wayanda suke cewa ba dole bane toh kansu ya hadu bakidayansu akan cewa Annabi muhammad (s.a.w) har yamutu qasru yakeyi duk sanda yayi tafiya toh tunda dukkansu sunyarda cewa idan Annabi yayi tafiya  qasru yakeyi, toh wannan yana nuna mana cewa lallai ayi qasrun shine abinda yafi***_
.
_sannan yasake komawa kan wancan hadisin na Ya,ala wanda Annabi (s.a.w) yace: ita qasru sadakace ta Allah gareku, dan haka ku karbi sadakar Allah***_
..
_cewa mukarbi sadakar Allah wannan yana nuna lallai mafi kyawun abinda yadace ga matafiyi shine yayi qasru****_
 .
_malamai suna bada misalin wannan hadisin, sukace kamar misali ace sarkin garinkune ya aika akiraka, dakazo fadarshi seyace dama wata kyautace yakeso yayi maka, seya dauko wani abu yabaka kyauta, shin idan kace bazaka karba ba, kana ganin kuwa shi sarkin garin naku zaiji dadi??? Na tabbata bazeji dadiba, toh ina kuma ga ace Allah yaimaka kyauta amma kaki karba dan uwa?? Saboda haka mafi dacewa shine duk sanda mutum yayi tafiya toh yayi qasru***_
 .
_sallolinda akeyi musu qasru, guda uku ne, sune: Azahar, La,asar da Isha'i, wato duk sallah me raka,a hudu itace ake maida ita raka,a biyu, amma sallolin magriba da Asubahi su ba,ayin musu qasru, cikasu akeyi asubahi ko ahalin tafiya ko zaman gida raka,a biyu akeyi, hakanan itama magriba raka,a uku akeyinta ko ahalin tafiya ko zaman gida***_
.
.
_Sekuma cewa da wasu malamai sukayi wai sekayi tafiyar mita kaza ko kilo mita kaza sannan zakayi qasru, toh itama wannan maganar me raunice, ko ace seka wuce gonaki, kokuma ka wuce gidajen garinku duk wayannan kawai maganganune na malamai, sedai muroki Allah ya yafe musu***_
.
_Amma waccan ayar ta suratun Nisa'i ayat 101, Allah kawai cewa yayi babu laifi akanku idan kunyi tafiya kuyi qasru, kunjifa Allah cewa yayi idan kunyi tafiya abayan qasa toh kuyi qasru, kunjidai Allah baice mita kaza ko kilo mita kaza ba, kuma Allah baifadi gonakiba kokuma inka wuce gidaje***_
.
_Ashe kenan tunda Allah mai shari,a yace idan kunyi tafiya kuyi qasru, toh waye kuma ya isa ya iyakance yace se tafiya takai nisa kaza ko kawuce gonaki kaza kafin kayi qasru?? Dan Allah inaso kugayamin wanene ya isa ya iyakance abinda Allah da manzonshi basu iyakanceba????***_
.
_Kafin mucigaba bari mudan ratse mukawo wata magana ta Albani, acikin muqaddimar *BID'UL JANA'IZ*, yace daga cikin hanyoyinda ake samun bidi,a tana shigowa cikin al,umma akwai: Idan Allah da manzonshi sukabar kofar wata ibada asake basuyi mata iyakaba, se wasu mutane suzo suyi mata iyaka da wani kaidi, kamar sukebance wani waje, ko wani lokaci kowata siffah***_
.
_Toh gashi Allah yace idan munyi tafiya abayan kasa toh babu laifi muyi qasru,  toh sekuma wani yazo yace amma karmu wuce sati biyu munayin qasrun, wani kuma yace karmu wuce kwanaki uku, wani kuma yace karmu wuce salloli kaza, wani kuma yace bazamu fara yin qasrunba harse munwuce gidaje ko gonaki, ko kilomita, toh kunga ashe wayannan maganganun dukansu fahimtane tasu su malaman dan haka semubar musu kayansu mudawo mubi Abinda Allah yace mana kawai mutsaya anan, sukuma ba zaginsu zamuyiba, Aa zamu roka musu Allah ne akan yayafe musu***_
.
_Toh Alhamdulillahi gama wani hadisinan na shurahbil bin samdin, wanda shine zeraba gardama, shurahbil yace: lokacin Sayyadina Umar yana khalifa, sai yataso daga cikin madina zuwa Zulhulaifah, sekawai yazo zeyi sallah sai akaga yayi qasru***_
..
_Duk wanda yasan garin madina ai yasan ko inane zulhulaifah, toh nan wajenfa umar yazo, wanda itama zulhulaifa cikin madina take itacema mikatinsu na hajji, toh anan wajenfa umar yazo sekuma akaga yayi sallah qasru, sai shurahbil ya tambayeshi, ya sarkin musulmi yanaga haka kuma kayi qasru anan wajen?? Sai kawai Umar yace Nayinefa kamar yanda naga Annabi yayi****_
.
_Kunji umar yace haka yaga Annabi yayi, toh a inakuma aka samo cewa se ankai kilomita kaza kafin ayi qasru?? Toh gashi umar unguwace yaje acikin madina kuma  yayi qasru sannan yace haka Annabi yayi***_
.
_toh dan Allah ku dauki wannan hadisin ku hadashi da waccan ayar kugani shin akwai bambanci?? Allah yace idan kunyi tafiya, baice sekunkai nisan kaza  ba, toh gakuma umar kunga dai 'yar tafiyar dayayi, kuma kunji abinda yace toh ashe kenan batun kuma ace saika wuce gonaki ko gidaje, ko kilomita, toh wannan maganar ashema sam batama tasoba, kawai rikicin malaman fiqhu ne, kuma suma sunyi sabani tsakaninsu, duk wanda ka dauka aciki toh kaga kayi watsi da maganar wasu,  toh mafi dacewa shine mu ajje musu sabaninsu mudauki Qur,ani da hadisin Annabi muhammad (s.a.w)***_
.
_wannan kuma itace fatwar ibn taimiya acikin majma,u fatawa, hakanan dawudu azzahiri, da Ibn qudama Alhambali acikin Almugni, da Ibn qayyum acikin zadul ma,ad***_
.
_Ibn qudama yace idan da zaka tattaro fahimtocin dukkan malaman ka hadasu waje daya toh zakaga hujjarda tafi karfi itace wayanda sukace inkayi tafiya kawai kayi qasru, batareda iyakance nisan tafiyarba kuma basu qayyade yawan kwanaki ba****_
.
.
_zan dakata anan sekuyi hakuri musake haduwa acikin bayani nagaba in Allah yaso***_
.
.
.
_Almajirinku kamar kullun_
.
```Jameel Alhassan Haruna Kabo```
_(Abu khausar)_
 .
.
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
https:/t/m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Subhanak Allahumma wabi hamdika nash hadu anla ila ha illah anta nastagfiruka  Wanatubu ilaika
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support