Duniya makaranta (fitowa ta 28) dr.mansur ibrahim sokoto ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Thursday 27 July 2017

Duniya makaranta (fitowa ta 28) dr.mansur ibrahim sokoto

DUNIYA MAKARANTA

Fitowa ta 28

136. Karatu akwai wuya, ilimi akwai dadi. Nema akwai wuya, arziki akwai dadi. Zama da jahilci ba wuya, rashin ilimi akwai takaici. Haka duniya take, yaro bata hankalin dare ka yi suna!

137. Allah ya ya mana kunnuwa biyu da idanu biyu amma ya yi mana baki guda daya saboda ya fi son mu yi kallo, mu yi saurare fiye da yadda mu ke magana

138. Idan na kwarai da mugu suka hadu kowa ma yana iya gane banbamci. Amma a tsakanin na kwarai da wanda ya fi shi, da mugu da wanda ya fi, wannan sai masu hankali ke iya rarrabewa.

139. Ba a sanin matsayin saurayi sai ya yi aure. Ba a sanin halin talaka sai ya wadata. Ba a sanin gaskiyar dan Siyasa sai ya kai ga mukami.

140. Ba kowane wayayye ne mai ilimi ba. Ba kuma kowane mai ilimi ne yake da wayewa ba. Idan Allah ya ba ka ilimi nemi sanin duniya da zamanin da kake cikin sa, sai ya zama kana daa haske a kan haske. Idan kuma kana da wayewa da sanin duniya matsa kusa da malamai ka kara sani, sannan ne wayewarka za ta amfane ka.

Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

2/11/1438
26/7/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support