Hukuncin qasru 6 ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Friday, 7 July 2017

Hukuncin qasru 6

*HUKUNCIN SALLAR QASRU-6!!!???*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Taken Lekca........
.
*SALLAR QASRU!!!!??*
.
Wannan shine bayani na shida****
.
Cigaba***
.
.
_Idan baku mantaba acan baya nakawo muku yanda aka tafka sabani gameda adadin kwanakinda mutum zeyi yana yin qasru, daga ciki nakawo fahimtar Imamu malik da shafi,i da Laisu bin sa,ad da dabary wayanda sukace kwanaki uku akeyi, kuma nace wannan maganar abarta batada inganci, toh cewa danayi ba kwanaki uku bane adadi qasru hakan yaharzuwa wasu masu da,awar bin mazhabar malikiyya, wanda har hakan yasa nadan tsawaita harshe akansi abayaninda yagabaci wannan***_
.
_Toh Imamul qurdubi shima dan malikiyyane toh aduba tafsirinshi mujallad na biyar shafina 258 yakawo sabanin malamai sosai gameda adadin kwanakinda akeyin qasru, toh yanzu misali incemuku kwanaki uku kawai akeyi ana qasru,  shin toh inakuma batun su Sa'idu bin musayyib wanda shikuma malamin malaman imamu malik ne, gakuma Abu hanifa da imamus sauri wayanda sukace kwanaki 14 akeyi ana qasru kenan idan nace kwana uku, ai kunga nawatsarda maganarsu, bayan kuma sunfi imamun malik daraja dan su tabi,aine wato Almajiran sahabbai***_
.
_Toh idan zamu dauka kamar yanda kukace, kin amfanida fatwar imamu malik kukace cin mutuncinshine kokuma zaginshi, toh shikuma imamu malik din menene hukuncinshi daya bada fatwarda ta sabama tasu Abuhanifa da sa'id nin musayyib?? Kenan shima ya zagesune kokuwa yaci mutuncnsu??***_
.
_cewa dakukayi 'yan salafiyya wai mazhabar Albani sukebi toh ashe Saleem Ibn ed Alhilali bashi bane yatattaro dukkanin muwaddodin wayanda akai ruwayarsu awajen imamu malik yahadasu waje guda?? Kuma ai saleem Almajirin Albanine, shin idan Albani bayason imamu malik har za,a samu dalubanshi suna wannan aiki na tattara muwaddodinnan awaje guda???***_
.
_toh wallahi kaunar imamu malik mu awajenmu aqeedace kuma duk wanda baya son imamu malik toh dan bidi,a muke daukarshi, amma wannan baya hukunta semunbi malik a inda yayi kuskure***_
.
_hakanan itama wannan maganar tasu Abu hanifa dasu Ibn musayyib dasukace qasru ba,a wuce sati biyu, itama wannan maganar me raunice mu ajjeta***_
.
_gakuma su Ahmad bin hambal wayanda sukace salloli 21 kamar yanda kukaji abaya***_
.
_toh yanzu dan Allah jama,a muyi adalci, gadai wayannan malaman sunyi sabani, kuma duk wanda muka ajje mabiyanshi zasuce mun wulakantashi, toh kenan dan Allah ya zamuyi???***_
.
_mafita kawai guda dayace, kamar yanda Allah ta,ala yace: idan kunyi jayayya gameda wani abu toh kumaidashi zuwaga Allah da manzonshi***_
.
_kafin mukai can ma toh gama wata riwaya daga imamu malik tana cikin muwadda daga Nafi'u yace: Abdullahi dan umar ya zauna amakka tsawon kwanaki goma yana qasru***_
.
_Imamul Qurdubi shima dan malikiyya ne, kuma yakawo wani asari dayace Anas dan malik yaje garin naisabur yakwashe kwanaki 60 acan yanayin qasru***_
.
_sannan shi qurdubin yakawo ruwayar  Abu mijlaz daya tambayi Ibn umar cewa zanje garin madina saboda wata bukata kuma zan zauna acan tsawon watanni bakwai ko takwas shin yaya zanyi sallah? Sai yace: kaita yin qasru***_
.
_Awata Ruwaya ta Anas dan malik (Ra) yace: Allah ya farlanta sallah akan harshen Annabinku, ahalin zaman gida raka,a hudu hudu, ahalin tafiya raka,a biyu biyu, ahalin tsoro kuma raka,a daya***_
.
_gakuma hadisin sayyadina umar yace: Sallar matafiyi raka,a biyune, sallar juma,a itama raka,a biyune, sallar idi karama raka,a biyune, babbar sallah itama raka,a biyune, kuma haka haka suke acike ba ragesu akayiba, dama can haka suke akan harshen Annabinku, wanda kuma yayiwa Annabi karya toh ya tabe***_
..
_kunji wayannan hadisan, wayanda suma masu ganin cewa dolene natafiyi yayi qasru, toh suna kafa hujjah da wannan hadisin na umar, wanda shima daliline akan cewa matafiyi asali gameda sallarshi dama can raka,a biyune, kuma umar yace wanda yaima Annabi karya toh ya tabe***_
.
_nan kusa kusa jama,a kuduba ALWAJIZ FI FIQHUS SUNNAH, wayannan hadisanfa sunanan aciki, bama se anje da nisaba***_
.
_Gakuma hadisin Anas dan malik yace: lokacinda muke dawowa daga makka zuwa madina tareda Annabi muhammad yakasance yana mana raka,a bibbiyune har muka iso gida, sai wani ya tambayeshi: shin Annabin ya zauna acan makka dinne?? Sai Anas yace eh ya zauna kwanaki goma acan kuma qasru yakeyi****_
.
_Toh ga dungurun gum kenan: Annani muhammad yazo makka wacce mahaifarshice amma ya kwashe kwanaki goma yana qasru****_
.
_Ibn taimiya acikin majmu,ul fatawa yace idan mutum yayi tafiya toh yarika yin sallah raka,a bibbiyu wannan shine sunnar Annabi muhammad, da khulafa,ur rashidun***Ibn taimiya yace Annabi (s.a.w) har yabar duniya duk sanda yayi tafiya qasru yakeyi, hakanan Abubakar da umar, da usman afarkon lokacin khalifancinsa***_
.
..
_zan dakata anan sekuma bayani nagaba idan Allah yakaimu***_
.
.
.
_Almajirinku kamar kullun_
.
```Jameel Alhassan Haruna Kabo```
_(Abu khausar)_
 .
.
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
https:/t/m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Subhanak Allahumma wabi hamdika nash hadu anla ila ha illah anta nastagfiruka  Wanatubu ilaika
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support