Hukuncin qasru 7 ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Friday, 7 July 2017

Hukuncin qasru 7

*HUKUNCIN SALLAR QASRU-7!!!???*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Taken Lekca........
.
*SALLAR QASRU!!!!??*
.
Wannan shine bayani na bakwai****
.
Cigaba***
.
.
_Kamar yanda kukaji abaya cewa Annabi har yabar duniya duk sanda zeyi tafiya qasru yakeyi, ba,a taba samun inda yacika sallah ba, kuma baice inkayi tafiya tawuce kwanaki kaza ba kacika sallah, ballantana ma gakuma wannan shahararren hadisin na yakin tabuka, inda Anas yace Annabi (s.a.w) yakwashe kwanaki 20 yanayin qasru***_
.
_Gakuma hadisin bukhari wanda yana cikin Bulugul maram wanda Anass yace manzon Allah ya kwashe kwanaki 19 agarin makka yana yin qasru****_
.
_saboda haka mafi ingancin magana shinw sallar qasru batada wani adadin kwanakinda ake denewa***_
.
_Kuma abinda ya tabbata a qur,ani da sunnah shine kawai duk sanda kayi tafiya toh yahalasta kayi qasru, koda tafiyar bata addini bace**_
.
_Matar aure wacce tayi aure awani gari wanda ba nasuba toh duk sanda zatazo ganin gida qasru zatayi duk da cewa gidan iyayenta tazo toh qasru zatai tayi harse takoma gida koda kwanaki nawa zatayi****_
.
_Dalubai wayanda suka zuwa makarantar kwana kuma qasru zakuyitayi harse kundawo koda kuwa shekaru nawa zakuyi acan, abinda Allah yace kawai inkunyi tafiya babu laifi kuyi qasru toh ga tafiya kunyi kunzo makaranta dan haka sekucigaba dayin qasru har zuwa lokacinda zaku koma gida****_
.
_Alhazai wayanda suke zuwa aikin hajji da masu umura kuma qasru zakui tayi harse kundawo***_
.
_Yan kwallo wayanda suke zuwa wata kasa domin sana,ar kwallo toh kuma qasru zakui tayi harse kundawo*****_
.
_Barawo wanda zaije wani gari domin yayi sata, toh kaima qasru zakaitayi har sekadawo, hakama dan fashi wanda zaije ya tare hanya kaima qasru zakayi harse ka dawo*****_
.
_karuwa wacce zataje wani gari danufin tayi zina kema qasru zakiyi tayi harse kindawo***_
.
_Kana aikine a ofishin jakadanci wata kasa, toh kaima qasrun zakaitayi harse ka dawo***_
.
_Abinda Allah yace kawai shine idan kunyi tafiya babu laifi kuyi qasru, amma Allah baice banda tafiya iri kaza, banda iri kaza ba, toh duk wanda zezo yacire mana wata nau,in tafiya yace mana ita ba,a yin qasru toh yazama dole yabamu aya ko hadisinda yace hakan, kukaranta tafsirin qurdubi jama,a cikin mujallad na biyar shafina 256***_
.
_Amma kamar wanda yake aiki awani gari aiki irinna zama, kamar soja ko dan sanda da sauran irin wayannan, toh wancan garinda aka kaika shine garinku ayanzu dan haka awannan garin kai bazakayi qasruba, cika sallah zakayi domin kai ba matafiyi bane, amma sanda kakoma garinku dan ganin gida da iyayenka toh anan kuma qasru zakayi tunda yanzu bakone kai, amma idan anturaka wani gari na wucin gadi kamar kunje aikin wanzarda zaman lafiya wata kasa akace zakuyi shekara daya acan kokuma fiyeda haka, wato andai qayyade lokacinda zakuyi kafin kudawo gida toh qasru zakui tayi harse kundawo gida koda shekaru nawa akace zakuyi***_
.
_shima mutuminda yakeda mata biyu misali amma ba a gari daya sukeba, wannan tana nan waccan tana can, toh shima babu qasru akanshi, duk inda kake yanzu gidane dan haka cika sallah zakayi, matukar ba wani akine yakawoka wani garinba wanda kake nufin inka gama zaka koma gida***_
.
_Na,am ansamu jumhurin malamai suna suna cewa wai tafiya inhar ta sabon Allah ne, wai baza,ayi qasruba toh wannan maganar tasamu kai tsaye basuda hujjah, kawai qiyasi sukeyu kuma irin kiyasinda ake cewa ma,al fariq***_
.
_Amma Allah duk idan yatashi yin sauki ga Al,umarsa zaka samu baya warewa, ko awajen azumi cewa yayi inkunyi tafiya ku ajjiye azumi, baice banda tafiya iri kaza da iri kaza ba, hakama sallah cewa yayi in kunyi tafiya abayan qasa kuyi qasru amma baice banda tafiya iri kaza da iri kaza ba, hakama manzon Allah bai ware wata tafiya yace banda itaba har yabar duniya***_
.
_kawai duk tafiyarda kayi kowacce irin tafiyace koda sata zakaje kayi ko karuwa zataje tayi zina, duk ya halasta suyi qasru harse sundawo, kuma wannan itace fahimtar Abu hanifa da auza,i da sufyan Assaury, kai shi kanshi imamu malik ansamu ruwaya daga wajenshi inda yake cewa duk tafiyarda zakayi toh yahalasta kayi qasru koda kuwa tafiyar ta haram ce***aduba Almuhalla ko Almugni na ibni qudama, kokuma Majmu,ul fatawa ta ibn taimiya***_
.
_Sukuma wayanda suke cewa wai banda tafiyar sabon Allah suna kafa hujjah ne da ayoyinda suke cikin suratul ma,ida da wacce take suratul baqara gameda hukuncin cin mushe sukace ai Allah daya halasta cin mushe ga masu larura, bai halastashi ga mutanen banzaba, toh shine suka dauko hukuncin cin mushe sukayi kiyasinshi da sallah, amma ibn taimiya yai musu raddi acikin majmu,ul fatawa mujallad na 24, ya raunana wannan maganar tasu***_
 .
_hakama ibn qayyum acikin zadul ma,ad yayi raddin maganar***_
.
_Amma babu shakka sharadinda Allah yaimana shine idan munyi tafiya abayan qasa babu laifi muyi qasru, amma duk wanda zaice banda dan fashi, banda karuwa banda kaza banda kaza, toh wannan maganar tana bukarar dalili nassi qur,ani ko hadisi ba wani kiyasiba, yan uwa***_
.
_Amma babu wata hujjah ta alqur,ani ko hadisi wacce tace me tafiya ta haramun bazeyi qasruba, babu wannan A qur,ani kuma babushi a hadisan Annabi muhammad, shin ko kuna gani Allah da manzonshi basusan akwai mutanen banza masu yin tafiya bane??***_
.
.
_zamu dakata anan sekuma fitowa tagaba idan Allah yakaimu***_
.
.
.
_Almajirinku kamar kullun_
.
```Jameel Alhassan Haruna Kabo```
_(Abu khausar)_
 .
.
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
https:/t/m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Subhanak Allahumma wabi hamdika nash hadu anla ila ha illah anta nastagfiruka  Wanatubu ilaika
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support