```HUKUNCIN MAI WASA DA SALLAH A MAHANGAR MUSULINCI``` ............................................... _Allah madaukakin sarki acikin Suratu Maryam aya ta 59 yana cewa "Sai waɗansu 'yan bãya sukazo a bãyansu suka tõzarta sallah kuma suka bi sha'awõwinsu. To, da sannu a hankali za'a jefasu cikin Gayyah" Allah ta'ala yace "Sai dai wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai" suratu Maryam 60_ . _Babban sahabin nan Ibn Abbas Allah ya kara masa yarda yace "Ba wai sun wulakanta sallah bane ta hanyar barin ta ba, aa kawai dai sun kasance ne suna jinkirta yin ta ne akan lokacin ta" kunga kenan da wannan fassara na Ibn Abbas zamu fahimci cewa lallai wadanda suke jinkirta sallah akan lokacin ta wato basuyin ta sai lokacin da suka ga dama to wannan ayar dasu take magana, wadanda suka kasance suna wulakanta sallah da sannu a hankali zasu afka cikin wutar gayyah bayan mutuwar su, lallai kuma zamu fahimci cewa wancan ayar fa ba wai tana magana akan kafirai bane aa tana magana ne akan wadanda suke ikirari cewa lallai fa su musulmi ne! Dan uwa mai karatu yaya kake ganin yanda rayuwar mu ta kasance a yau?_ . _Sa'ed Ibnul Musayyib Imamt-Tabi'een Allah yayi masa rahama yana cewa dangane da wancan ayar sai yace "Sune wadanda basuyin sallar Azahar har sai lokacin sallar la'asar, kuma basuyin sallar la'asar har sai lokacin maghriba yayi, kuma basuyin sallar maghriba har sai lokacin sallar Isha'i yayi kuma basuyin sallar Isha'i har sai lokacin sallar asuba yayi, kuma basuyin sallar Asuba har sai rana ta fito, kuma lallai ku sani duk wanda ya mutu yana acikin masu irin wannan hālin alhali bai tuba ba to alkawarin Allah a tattare dashi itace wutar gayya! Wato gayya wani kwari ne acikin wutar jahannama wanda yake da zurfi mai nīsa kuma zasu dika cin wani mummunan abinci mai wari da daci da uqūba"_ . _Allah ta'ala yana cewa فَوَيْلٌ لِّلْمُصَلِّينَ ma'ana "To, bone (rijiyar azaba) ta tabbata ga masallata" amma sai ya kara da cewa الَّذِينَ هُمْ عَن صَلَاتِهِمْ سَاهُونَ ma'ana "Waɗanda suke masu shagala daga sallar su" wato abinda ake nufisuna shagala daga sallarsu ana nufin suna jinkirtata daga yinta akan lokaci, dan uwa kaduba fa nan maganar Allah ta'ala ne akan masu jinkirta sallah har yace masu Rijiyar azaba ta tabbata akan su, anya kuwa muna tsoron Allah! Gamu da rayukan mu bazamu hankalta ba kuma bazamu tunani ba tun kafin Allah yace wa mala'ikan mutuwa Emergency Operation aje a dauko masa rayukan mu, lallai'yan uwa kada mu kuskura mu dika jinkirta sallah domin lallai ita sallah barinta yakan fitar da mutum daga musulunci_ . _Babban Sahābin Annabi saw Sa'ad Ibn Abī-Waqqas Allah ya kara masa yarda yace: Na tambayi Annabi saw dangane da fadar Allah ta'ala wadanda suke masu shagala ne daga sallolin su, sai Annabi saw yace "Sune wadanda suke jinkirta yinta akan lokacin ta" wato suna jinkirta yin sallah akan lokaci saboda shagala da kuma raina ta, kuma suna kin yinta akan lokaci to hakika alkawarin Allah a tattare dasu itace wani kwari wato wani rami ne wanda ake tsananta azaba acikin sa, wato kwari ne da Allah ta'ala ya tanade shi acikin wutar jahannama wanda rami ne mai tsayin gaske kuma ga tsananin zafi acikin sa kuma hakika wannan kwari an tanadeshi ne ga wadanda suke jinkirta sallah basuyin ta akan lokacin ta, sai dai wadanda suka tuva zuwa ga Allah madaukakin sarki kuma sukayi nadama akan abinda suka aikata, to wadannan sune masu rabauta in shaa Allah ta'ala_ . _"Yan uwa wallahi idan mukace zamu bayyana dukkanin abinda yazo dangane da hukuncin masu jinkirta sallah to tabbas acikin rubutun nan ko kwata bamu bayyana ba, to amma su waye masu jinkirta sallah? Billahi suna da yawan gaske! . *
(1) MATA a gidajen su suna wasa da sallah yanda suka ga dama, kuma suna wulakanta ta matan aure da 'yan mata wallahi da ace zakaga yanda mata suke wulakan ta sallah abin sai ka zubar da hawaye kayi kuka saboda irin bala'in da suke sanya kansu aciki,* . _lallai 'yar uwa ga kisani kulawa da sallah wajibi ne a gareki ki sani Allah ta'ala yace "Mu bamu kasance muna yiwa kowwa azaba ba har sai mun aika masa da dan sako" Nahli don haka wallahi sakon Allah yazo maki ta hanyar wayar salulan ki da take a hannun ki kuma idan sakon Allah ta'ala yazo gareki wajibi ki kar6e shi koda ace kuwa yazo maki ne ta hanyar school on air, Wajibi ki umarci 'ya'yan ki da cewa suyi sallah akan lokaci haramun ne kuma babban bala'i ne jinkirta sallah idan kuwa kika juya baya nasiha bata wadatar dake ba to hakīka wutar gayyah tana nan tana jira, Allah ta'ala ya tsare mu kuma ki sani wajibi ne ki umarci mijinki crwa yayi sallah kuma aksn lokaci domin kuwa kakaf dinku ababen tambaya ne akan ahlin ku Allah yashiryar damu_ . *
(2) DIREBAN MOTO yana wulakanta sallah yanda yaga dama sai kadan daga wadanda Allah ta'ala ya shiryar* . _Lallai dan uwa kasani kada ka yarda neman duniya yasanya ka ka kauce daga kan karaga na mun tsira kafada kangin wahala lallai wajibi ne direbobi kuji tsoron domib kada wancan ayoyin da hadisai suyi aiki akan ku, Allah ta'ala ya tsare mu_ . *
(3) SAMARI wallahi abin dai saidai muce Lā Haula Walā Quwwata Illā Billāh wato 'yan uwa yanda samari muke yin wasa da sallah kai kace hujha ce ta lasisi da muka samu daga littafin Allah ko sunnar Annabi Muhammad data tabbatar mana da cewa lallai samari idan sunyi wasa da sallah basu da laifin komai! Lallai wannan musība tayi mūni!* . _Wajibi samari muji tsoron Allah muyi tanadi tun kafin lokacin mu yayi wanda kuwa ya mutu baya sallah kafiri ne, baza'ayi masa sallah ba kuma baza'ayi masa wanka ba kuma baza'a bitne shi a makabartan musulmi ba arne ne!!!, akwai dalilai masu yawa akan haka, 'yan siyasa kuji tsoron Allah ku nisanci yin wasa da sallah, kuma sarakuna kuji tsoron Allah ku nisanci yin wasa da sallah, yāku musulmin duniya kuji tsoron Allah ku daina wasa da Allah, Allah ta'ala yana cewa, "Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada dũkiyõyinku da 'ya'yanku su shagaltar da ku daga ambaton Allah. Kuma wanda ya yi haka, to, waɗannan sũ ne mãsu hasãra" Munafiqun,_ . _Wannan Nasīhā ce zuwa ga daukacin Al'immar musulmi daga zauren Sa'adatul-Muslim da fatan anyi shagulgulan sallah lafiya, Allah ta'ala ya kar6a mana kuma ya gafarta mana kurakuran mu anan zamu dakata Allah yasa mudace_ .
*Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga* .
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb . → Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp

0 comments:
Post a Comment