Menene hukuncin mutumin da akabashi ajiyar kudi sai yake kasuwanci da kudin yana samun ribah ?? ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Thursday 6 July 2017

Menene hukuncin mutumin da akabashi ajiyar kudi sai yake kasuwanci da kudin yana samun ribah ??

     
*_Tambaya ta (324)_*
:
_Menene hukuncin Mutumin da akabashi *ajiyar kuɗi* sai yake kasuwanci da *kuɗin yana samun ribah??*_
:
*_Amsa:_*
:
_Asalidai a *Shari'ance* idan akabawa Mutum ajiyar wasu *Kuɗaɗe* kokuma kadarori to wajibine akansa yakiyaye wannan amanar da'akabashi, Sannan kuma bazaiyi amfani da'itaba dole sai in yanemi izinin mai ita, to amma idan har Mutum yayi amfani da *Kuɗin ajiya* yana Kasuwanci dasu yana samun riba, anan sai *Malamai sukayi Saɓani dangane da hukuncin wannan ribar da'aka samu,* Mazhabin *Malikiyya da Shafi'iyya* sunaganin cewa wannan riba da'akasamu ta shi Mutumin da yajuwa *Kuɗin ne* wato wanda akabawa ajiyar Kuɗin kenan, sukace wanda yabada ajiya za'amayar masa da asalin Kuɗinsane da yabayar a ajjemasa, amma wanda akabawa ajiyar Kuɗin shine zaidauki abinda yakaru aciki, domin shine yayi wahala wajen yin kasuwanci da'ita, duk dacewa *yayi amfani da Kuɗaɗenne* ta hanyar ta'addanci batare da izinin maisuba,_
:
_*Hujjarsu anan itace,* tunda haryayi ta'addanci nayin amfani da *Kuɗaɗen ajiya* wanda kuma inda wadannan *Kuɗaɗen zasu salwanta to wajibine akansa sai yabiya,* danhaka kenan tunda ramuwa tana kansa idan akayi asara to hakanan kuma idan akasamu riba shine zairiketa, kamar yadda *Ƙa'idarnan ta Fiƙ-hiyya* datake cewa:_
               *(الخراج بالضمان)*
_Saidai *Mazhabin Hanabila* suntafine akancewa wannan riba da'akasamu ta mai asalin wanda yakawo ajiyar *Kuɗinsane domin da Kuɗaɗensa ne akasamu wannan riba danhaka tasace,* amma Mazhabin *Hanafiyya* suntafine akan cewa da wanda yabada ajiyar da wanda akabawa ajiyar dukkaninsu babu wanda zaidauki wannan riba ta Kuɗi da'akasamu, danhaka saidai ayi *Sadaƙa da Kuɗin kawai,* Saidai wasu daga cikin Malamai sukace a'a, *kawai za'araba wannan ribar Kuɗaɗen da akasamune gida biyune* sai suraba atsakaninsu, kowa yadauki rabi,_
:
_Danhaka kenan asali *Haramunne amma akwai Malaman dasukace Makaruhine* Mutum yayi amfani da dukiyar da'akabashi ajiya batareda izinin mai'itaba, to amma idan har ya aikata hakan batareda izinin mai'ita ɗinba meye hukuncinsa? Malamai sukace yayi ƙoƙari yanemi afuwa da yafiya daga wajen mai asalin dukiyar shikenan magana taƙare,_
:
*_o(шαʟʟαнυ- тα'αʟα α'αʟαмυ)o_*
:
*_ωαηαη sнιηε gωαяgωαdoη ɗαη αвιηdα ιʟιмιη мυ dαкυмα вιηcιкεηмυ үαкαι zυωα gαяεsнι, dαηнαкα ιdαη αηgα ωαηι кυsкυяε αcιкιη αвιηdα мυкα яυвυтα тo αηα'ιүα ғαɗαкαя dαмυ мυgүαяα, тαяεdα кαωo нυננα мαι ƙαяғι:_*
:
*_Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:_*
                 *_↓↓↓_*
:
*"مغني المحتاج" (3/363)*
:
*"المغني لإبن قدامة" (5/159)*
*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
              *Daga Zaυren*
             *Fιƙ-нυl-Iвadaт*
                *(فِقْهُ الْعِبَادَاتِ)*
*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
              *_→AMSAWA←_*
           *Mυѕтαρнα Uѕмαи*
              *08032531505*
*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
_*Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾*_
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support