*MENENE BANBANCI TSAKANIN GIRMAN KAI DA KUMA JIJI DAKAI MEYE MATSAYIN MAIYINSU A MUSULUNCI.*
الحمد الله الذي هدان للإسلام وما كنا لنهتدي لولا أن هدان الله، والصلاة والسلام على محمد وآله وصحبه وسلم.
Girman kai da kuma jiji dakai, dukansu dabi'une munana wanda musuluci ya yakesu, kuma dabi'u ne ababen zargi masu kai mutum ga halaka, cikin kankanin lokaci, banbaci dake tsakanin su kadanne shine:
Shi girman kai shine kadunga ganin fifiko akan wani, kadunga jin kafi wane kai abu kaza kafi karfin ko kawuce matsayin wane kafi karfin saurarensa dadai makamantan haka.
Shima jiji dakai shine kadunga jin kana da wani abu da waninka bashi dashi.
Dukansu munane wadanda suke dauke bawa daka godewa Allah, zuwa godewa kai dajin wayanka ko iyawarka sukema abu, suna hanaka yaban Allah dagode masa ka koma yaban kanka, dakuma qin kankantar da kanka ga mahalicci, da ruduwa dakai dakin girmama mutane da sanin matsayinsu izuwa hantarar su, da danne hakko qinsu.
yana daka illolin jiji dakai suke haifarwa akwai rusa ayyuka kyawawa da kuma boye masu kyau, dakuma janyo zarge zarge.
Hukuncin jiji dakai haramunne domin nau'ine na shirka,shaikul islam ibnu taimiyya yace : ( Sauda yawa riya tana kusanci da jiji dakai, ita riya tana babin shirka da halittu, shikuma jiji dakai yana babin shirka dakai, wannan shine halin mai girman kai, Mai riya bai tabbatar dafadin Allah madaukakin sarki ba
إياك نعبد،
Mai jiji dakai kuma bai tattabatar, da fadin Allah madaukin sarki,
وإياك نستعين،
duk wanda yatabbatar da fadin Allah إياك نعبد zaifita daka riya
wanda yatabbatar da fadin Allah
وإياك نستعين،
zai futa daka jiji dakai.
Jiji dakai abun zargine acikin alqur,ani da sunnah Allah madaukakin sarki yace: ( ويوم حنين إذ أعجبتم كثرتكم فلم تغن عنكم شيئا )
Daranar yakin hunaini lokacin dayawanku ya burgeku kuma bai tsinana muki komai ba yawan naku.
Abdullahi dan masu' ud yace halaka tana cikin ababe biyu, debe tsammani daka Allah dakuma jiji dakai.
jiji dakai yakan kai maiyinsa zuwa ga kafirci da futa daka musulunci kamar yanda shaidan yai alfahari da asalinsa da ibadar sa, yaiwa Allah girman kai.
Ibnu qudama yace: kasani jiji dakai yakan kawo girman kai domin yana cikin dalilan dake kawo girman kai, acikin girman kai kuma akwai masifu dayawa akwai tsakanin haittu da kuma tsakaninka da mahaliccinka
Ababen dazaka gane maijiji dakai sune
•Kin gaskiya mayar da ita da hantarar mutane
•Raina kowa
•Rashin shawartar masu hankali da manya acikin al'amura
•Rangwada atafiya ji da isa
•Ganin girman biyayyar da kakewa Allah dakuma ganin yawanta
•Alfahari da ilimi da gori dashi
•Alfahari da dukiya da dangi da kyawun halitta
•Raina kokarin maluma masu tsoran Allah
•Dawwama akan kuskure
•Karancin sauraron ilmi ko mika wuya ga masu shi dalazimtarsu
•Hantarar masu sabo
•Manta zunubai da rainasu ganin karancin su
•Sabawa mutane dagangan danjin isa
Abubuwan da suke janyo jiji dakai
√Jahilci
√karancin tsantseni da tsoran Allah
√Raunin jin cewa Allah yana tare dakai yana kallanka
√Karancin wadanda zasuyiwa mutum nasiha
√Mummunar niyya
√Yawan jindadin yabon mutane koyin abun dan samun yabonsu dakuma taimakon shaidan Akan haka
√Fitunwa dasan duniya dabin san zuciya
√Karancin tunani
√Karancin godewa Allah
√Karancin Ambaton Allah
√ Rashin tadabburin Alqur'ani da kuma hadisai
√Amintuwa da azabar Allah da dogara da Afuwarsa da gafarar sa kadai.
Maganin sa shine tuna ni'imomin Allah dakuma tuna yanda mutum yake abaya kafin yakai matsayin dayake na yanzu, dakuma tuna tarihin Al'ummatan da suka shude da karanta rayuwar manzan Allah salallahu Alaihi wasallam da sahanbansa.
والله أعلم،
***********************************
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.
_*Tambayoyin*_ _*Musulunci*_
_*WhatsApp*_ _*Group*_
0 comments:
Post a Comment