Duniyarfatawa.com™: Tambayoyin musulunci

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Showing posts with label Tambayoyin musulunci. Show all posts
Showing posts with label Tambayoyin musulunci. Show all posts

Wednesday, 8 August 2018

Tamabaya da Amsa :- Shin yana hallatta macce budurwa tashafa turaree Sannan tafito waje dashi??

*|```Assalamu alaikum*```
*```Malam ko ya hallatta macce budurwa tashafa turaree Sannan tafito waje dashi??*```



_*AMSA:*_
*******

وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،


Haramun ne mace ta sanya turare ta fita inda wasu maza zasuji kamshinsa. Dalili kuwa shine:


ﺛﺒﺖ ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺃﻧﻪ ﻗﺎﻝ: ﺃَﻳُّﻤَﺎ ﺍﻣْﺮَﺃَﺓٍ ﺍﺳْﺘَﻌْﻄَﺮَﺕْ ﻓَﻤَﺮَّﺕْ ﻋَﻠَﻰ ﻗَﻮْﻡٍ ﻟِﻴَﺠِﺪُﻭﺍ ﻣِﻦْ ﺭِﻳﺤِﻬَﺎ ﻓَﻬِﻲَ ﺯَﺍﻧِﻴَﺔٌ.
ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺃﺣﻤﺪ‏(19212‏) ﻭﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ ‏(5126‏) ﻭﺣﺴﻨﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ.

_Ya tabbata daga *Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam)* yace idan mace ta sanya turare ta wuce ta gaban mutane (Maza) domin suji kanshin turaren ta, toh ita mazinaciya ce._
*Imam Ahmad ya ruwaito shi a hadisi mai lamba 19212.* da *Nisaa'i hadisi mai lamba 5126.*
_Albani ya inganta shi Cikin sahihul jami'i._


ﻋَﻦْ ﺯَﻳْﻨَﺐَ ﺍﻣْﺮَﺃَﺓِ ﻋَﺒْﺪِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺑﻦ ﻣﺴﻌﻮﺩ، ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ﻭﻋﻦ ﺯﻭﺟﺎ، ﻗَﺎﻟَﺖْ: ﻗَﺎﻝَ ﻟَﻨَﺎ ﺭَﺳُﻮﻝُ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ: ﺇِﺫَﺍ ﺷَﻬِﺪَﺕْ ﺇِﺣْﺪَﺍﻛُﻦَّ ﺍﻟْﻤَﺴْﺠِﺪَ ﻓَﻠَﺎ ﺗَﻤَﺲَّ ﻃِﻴﺒًﺎ.
ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ ‏(443).

_An karbo daga *Zainab* matar *Abdullahi Ibn Mas'ud* (radiyallahu anha Wa zaujaha) tace: *Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam)* yace damu; Idan dayanku zata tafi masallaci kada a shafa turare._
*Muslim ya ruwaito shi a hadisi mai lamba 443.*



والله أعلم،

***********************************


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.


_*🌙Tambayoyin*_ _*Musulunci🌙*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_
_*+2347068043652*_
_*+2348164884055*_
Share:

Thursday, 28 June 2018

Tambaya da Amsa :- Shin yana halatta ga Mutum bayan yayi zina da mace, kuma ya Aureta ??

*```Assalamu alaikum Malam yana halatta ga mutum bayan yayi zina da mace, yana halatta ya aure ta?*```


_*AMSA:*_
*******

وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ


A shari'ance baya halatta ga mutum ya auri wacce yayi Zina da ita har sai sun tuba _*(Taubatan Nasuuhan)*_ su biyun.

*TUBA* yana tabbatuwa ne idan mutum yayi nadama akan abinda ya aikata da yin kyakkyawar niyyar bazai sake aikatawa ba.

Saboda haka idan sun tuba kuma sunyi nadamar abinda sukayi kuma sunyi alwashin bazasu sake aikatawa ba, to yana halatta agaresu suyi aure abisa ra'ayin mafi yawan malamai.

*Ibn Qudaamah (rahimahullah)* yace: Idan mace tayi Zina, to baya halatta ga Wanda yasani ya aureta har sai an cika sharudda biyu;
*1.* Ta gama iddarta.
*2.* Ta tuba daga Zinar da ta aikata
      Idan wadannan sharuddan sun cika, to ya halatta a aureta abisa ra'ayin lafiya yawan malamai, wannan shine ra'ayin Abubakar Al-siddiqu, Umar ibn Khaddab, Ibn Umar, Ibn Abbaas, Jaabir, Sa‘eed ibn Al-Musayyab, Tawoos, Jaabir Ibn Zayd, Ata’, al-Hasan, Ikrimah, Az-Zuhri, ath- Thawri, Ash-Shaafa‘i, Ibn Al- Mundhir da Ashaab ar-ra’y.
_*(All-Mughni , 7/108.)*_


والله أعلم،

***********************************


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.


_*🌙Tambayoyin*_ _*Musulunci🌙*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_
_*+2347068043652*_
_*+2348164884055*_
Share:

Tambaya da Amsa:- Menene Hukuncin mata masu huda Hanci ??

*```ASSALAMU ALAIKUM!!!*```
*```MENENE HUKUNCIN MATA MASU HUDA HANCI??*```



_*AMSA:*_
********


وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ


An tambayi _*Shaykh Muhammad Saalih Al-Uthaymeen (Rahimahullah)*_ gameda Huda Hanci da Huda kunnuwa da ake yiwa yara mata saboda suyi kyau? Sai yace:
Ra'ayin da yake daidai shine babu laifi akan Huda kunne, saboda daya daga cikin dalilan huda kunne shine sanya halatattun kayan ado (Yan Kunne). An san cewa mata sahabbai sunada yan kunne da suke sanyawa a kunnuwansu.

Zafin ciwon hudawar mai sauki ne, kuma idan anyi huduwar ne a lokacin da yarinya tana karama, yafi saurin warkewa.


Abinda ya shafi *HUDA HANCI* kuma bazan iya tina cewa malamai sunce wani abu akan Huda Hanci ba, amma dai wani nau'in ne na canza halitta da gurguntawa idan muka kalli fuskar daga wajenta, duk dayake wasu basa kallonsa ta wannan fuska.

Idan mace tana acikin kasa ko gari Wanda sanya kayan ado a Hanci ana kallonsa wani nau'i ne na kwalliya da ado, to, babu wani abin laifi ga huda Hanci.
_*(Majmu'ul Fataawa Ibn Uthaymeen, shafi na 11, tambaya ta 69).*_



والله أعلم،

***********************************


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.


_*🌙Tambayoyin*_ _*Musulunci🌙*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_
_*+2347068043652*_
_*+2348164884055*_
Share:

Tuesday, 26 June 2018

Tambaya da Amsa :- Idan mutum ya rasu ya bar Mata guda daya1 da 'ya'ya maza guda uku 3 da 'ya mace guda daya1, kuma ya bar dukiya ta miliyan takwas da dubu 'dari biyar (8.5million). Ya Kason kowa zai kasance?

*```Assalamu alaikum*```
*```Tambaya na shine:*```
*```Idan mutum ya rasu ya bar Mata guda daya1 da 'ya'ya maza guda uku 3 da 'ya mace guda daya1, kuma ya bar dukiya ta miliyan takwas da dubu 'dari biyar (8.5million). Ya Kason kowa zai kasance?*```




_*AMSA:*_
*******

وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،



Abu Na farko daza'a aiwatar akan dukiyar mamaci shine biyan bashi da wasiyya, kafin a shiga gundumar rabon gado.


Idan namiji ya rasu yabar mata daya da yara maza uku (3) da 'ya mace daya.
Idan wadannan sune magadansa kadai wadanda ya bari.

To anan kason matar zai kasance 1/8 (Sumuni) Na dukiyar da yabari, 'yarsa daya mace za'a bata Rabin kason namiji daya.
Kamar yadda Allah ya fada acikin Suratun Nisaa'i ayah ta 11 da 12.

ﻳُﻮﺻِﻴﻜُﻢُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻓِﻲ ﺃَﻭْﻟَﺎﺩِﻛُﻢْ ۖ ﻟِﻠﺬَّﻛَﺮِ ﻣِﺜْﻞُ ﺣَﻆِّ ﺍﻟْﺄُﻧْﺜَﻴَﻴْﻦ

Allah yana yimuku wasiyyah acikin 'ya'yanku, namiji yanada rabon mata biyu.........(Nisaa'i 11)


ﻭَﻟَﻬُﻦَّ ﺍﻟﺮُّﺑُﻊُ ﻣِﻤَّﺎ ﺗَﺮَﻛْﺘُﻢْ ﺇِﻥْ ﻟَﻢْ ﻳَﻜُﻦْ ﻟَﻜُﻢْ ﻭَﻟَﺪٌ ﻓَﺈِﻥْ ﻛَﺎﻥَ ﻟَﻜُﻢْ ﻭَﻟَﺪٌ ﻓَﻠَﻬُﻦَّ ﺍﻟﺜُّﻤُﻦُ ﻣِﻤَّﺎ ﺗَﺮَﻛْﺘُﻢْ ﻣِﻦْ ﺑَﻌْﺪِ ﻭَﺻِﻴَّﺔٍ ﺗُﻮﺻُﻮﻥَ ﺑِﻬَﺎ ﺃَﻭْ ﺩَﻳْﻦ

........Kuma (Su Matan) sunada rubu'i daga abinda kuka bari (Na dukiya) idan reshe ('ya'ya) bai kasance ba gareku, to, idan kuwa reshe ya kasance gareku, to sunada sumuni (1/8) daga abinda kuka bari, daga bayan wasiyya wanda kukayi ko kuma bashi (debt)............(Nisaa'i 12).

Reshe acikin ayah ta 12 yana nufin 'ya'ya. Idan miji ya mutu yabar mata ita kadai babu 'ya'ya, to rabon ta shine 1/4.

Idan kuma akwai 'ya'ya to rabonta shine 1/8 kamar yadda ya tabbata a ayar.

A tambayar mu ta sama. Namiji ya rasu yabar masu gadonsa kamar haka:
1. Mata daya
2. Yara Maza uku (3)
3. Yarinya daya

Sannan yabar kudi naira miliyan takwas da dubu dari biyar:
N8,500,000

Ga yadda kason kowa zai kasance:

MATA
******
Za'a bata 1/8 Na N8,500,000
Shine ya kama miliyan daya da dubu sittin da biyu da naira dari biyar.

====N1062500


Idan an cire rabon matarsa, za'a bar N7,437,500.

Anan maza uku ne, kowanne kashi biyu za'a bashi, mace kuma kashi daya.

Idan ka hada kashi biyu sau uku zai baka kashi shida.
       (2×3)=6

Sannan a tara da kashi daya Na mace zai bamu kashi bakwai
6+1=7

Yanzu zamu raba N7,437,500 zuwa gida bakwai

(N7,437,500/7)==N1062500.

Mace kashi daya
Kowanne namiji kashi biyu.

Kashi biyu zai bamu
1062500+1062500
      ==N2,125,000


YARA MAZA
**************
Kowannensu zai samu " Naira Miliyan biyu da dubu dari da ashirin da biyar"

======N2,125,000


'YARSA MACE
***************
Zata samu "Naira miliyan daya da dubu sittin da biyu da naira dari biyar"

======N1,062,500.




والله أعلم،

***********************************


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.


_*🌙Tambayoyin*_ _*Musulunci🌙*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_
_*+2347068043652*_
_*+2348164884055*_
Share:

Tuesday, 15 May 2018

Tambaya/Amsa:- Shin ya halasta ayiwa mutum Allurar Zazzabi a lokacin Azumi??


*```Assalamu alaikum*```
*```Malam shin ya halasta ayiwa mutum allurar Zazzabi lokacin da yake azumi? nagode*```


_*AMSA:*_
*******

وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،


Ya halatta ga mai azumi ayi masa allura a lokacin da yake azumi da rana.

Amma bai halatta ba ayiwa mutum allurar abinci da rana lokacin da yake azumi. Domin wannan yana daukar hukuncin cin abinci ne da shan abin sha. Yin haka zai zama sanadin karya Azumin Wanda aka yiwa allurar (Allurar abinci ko abinsha). Saboda idan za'ayi allurar da daddare shine mafi a'alaa.

_*(Al-lajnatu al-da'imah lil buhuusil ilmiyyat wal ifta'a, 10/252).*_



والله أعلم،

***********************************


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.


_*🌙Tambayoyin*_ _*Musulunci🌙*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_
_*+2347068043652*_
_*+2348164884055*_

Allah yasa mudace.
Share:

Friday, 3 November 2017

MENENE HUKUNCIN WANDA YAYI SALLAH ALHALI YASAN YANA CIKIN JANABA??

*MENENE HUKUNCIN WANDA YAYI SALLAH ALHALI YASAN YANA CIKIN JANABA??*

الحمد لله رب العالمين.

Amsa: Abune sananne awajan musulmi cewa tsarkin  hadasi babba ko karami, wajibine, kuma sharadine na ingancin sallah, duk wanda yai sallah bashi da tsarki da gangan koda mantuwa sallarsa batacciyace bataiba, saiya sake, idan daganganci yayi hakika ya aikata babban laifi cikin manyan laifuka dakuma zunubi mai girma.

Shaikul islam ibnu taimiyyah rahimahullah yace:

"Musulmi kada yayi sallah a inda ba alkibla bane, kada yayi sallah batare da alwala ko ruku'u ko sujjada ba, wanda ya aikata haka yacancanci zargi da uquba,
Min hajussunnah (5/204).

Hakika gargadi mai tsanani yazo gawanda ya aikata haka;

Hadisi daga Abdullahi dan mas'ud yardar Allah takara tabbata agareshi daka Annabi sallallahu Alaihi wasallam yace: (Anyi Umarni ayiwa wani bawa daka cikin bayin Allah bulala dari acikin kabarinsa, bai gusheba yana tambayar dalilin bulalar dakuma rokon asassauta masa harsaida ya rage saura bulala daya, sai aka karasa masa dayar, aka cika kabarinsa da wuta, lokacin da'aka dauke masa azabar bayan yafarfado sai yace kusanar dani sabo dame akaimin bulala? sai akace dashi kayi sallah ne sau daya batare da tsarki ba, kawuce tawajan azzalumi kuma baka taimakeshiba) Addahawi yaruwaitoshi acikin mushkilil Ãàsaar Albani ya hassanashi acikin silsila saheeha (2774).

Malamai sunyi ittifaqi akan duk wanda yai sallah batare da tsarki ba yana mai halatta hakan, ko saboda isgili, hakika yakafirta, za'a nemi yatuba, idan bai tubaba za'a kasheshi.

Amma idan mutum yai sallah batare da alwala kawai dan wulakanta sallah, bai halatta hakan ba kuma ba izgili yakeba,  Imamu Ahmad yatafi akan cewa mutum yakafirta, jamhurdin malamai kuma sukace: bai kafirta ba, saidai abunda yayi babban laifine cikin manyan laifuka.

Imamun nawawi rahimahulla yace:

Idan mutum yasan yanada hadasi kuma yasan sallah batsarki haramunne, abunda yayi laifine babba cikin manyana laifuka, baya kafirta awajanmu, saidai idan yahalatta sallah batsarki ne, Abu hanifa yace yakafirta saboda izgilinsa.

Abunda yake wajibi akan wanda yai sallah babu tsarki shine yatuba, yayi istigfari, yakuma kuduri niyyar bazai sake aikata hakan ba, sannan saiya sake sallar daya sallata batare da alwala ba, Allah madaukakin sarki yana karbar tuban wanda yatuba yakoma gareshi.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.

Tambayoyin musukunci
Watsapp group
Share:

Saturday, 30 September 2017

Miyasa idan an dauko gawa zakaga mutane nakan hanya suna tashi tsaye ??

```Assalamu alaikum
Malam tambayana shin wai meyasa in an taho da gawa zakaga mutane nakan hanya suna tashi tsaye```



_*AMSA:*_
*******

وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،



ﻋَﻦْ ﻋَﺎﻣِﺮِ ﺑْﻦِ ﺭَﺑِﻴﻌَﺔَ ﻗَﺎﻝَ: ﻗَﺎﻝَ ﺭَﺳُﻮﻝُ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ: ﺇِﺫَﺍ ﺭَﺃَﻳْﺘُﻢْ ﺍﻟْﺠَﻨَﺎﺯَﺓَ ﻓَﻘُﻮﻣُﻮﺍ ﻟَﻬَﺎ ﺣَﺘَّﻰ ﺗُﺨَﻠِّﻔَﻜُﻢْ ﺃَﻭْ ﺗُﻮﺿَﻊَ.
```(ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ،  958‏)```

_An karbo daga *Aamir Ibn Rabee'ah* yace: *Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam)* yace; Idan kunga Janaza (Gawa ana Wucewa da ita) Ku tashi tsaye gareta har sai ta shige gabanku ko an sanyata (a kabari)._
_*(Muslim, 958)*_


ﻋَﻦْ ﺍﺑْﻦِ ﺃَﺑِﻲ ﻟَﻴْﻠَﻰ: ﺃَﻥَّ ﻗَﻴْﺲَ ﺑْﻦَ ﺳَﻌْﺪٍ ﻭَﺳَﻬْﻞَ ﺑْﻦَ ﺣُﻨَﻴْﻒٍ ﻛَﺎﻧَﺎ ﺑِﺎﻟْﻘَﺎﺩِﺳِﻴَّﺔِ، ﻓَﻤَﺮَّﺕْ ﺑِﻬِﻤَﺎ ﺟَﻨَﺎﺯَﺓٌ ﻓَﻘَﺎﻣَﺎ، ﻓَﻘِﻴﻞَ ﻟَﻬُﻤَﺎ: ﺇِﻧَّﻬَﺎ ﻣِﻦْ ﺃَﻫْﻞِ ﺍﻟْﺄَﺭْﺽِ، ﻓَﻘَﺎﻟَﺎ: ‏(ﺇِﻥَّ ﺭَﺳُﻮﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ﻣَﺮَّﺕْ ﺑِﻪِ ﺟَﻨَﺎﺯَﺓٌ ﻓَﻘَﺎﻡَ، ﻓَﻘِﻴﻞَ: ﺇِﻧَّﻪُ ﻳَﻬُﻮﺩِﻱٌّ؟ ﻓَﻘَﺎﻝَ: ﺃَﻟَﻴْﺴَﺖْ ﻧَﻔْﺴًﺎ)
```ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ ‏(960)```

_An karbo Daga Inn Abi Lailah cewa: Lalle Qais ibn Sa'd da Sahla ibn Hunaifi sun kasance (suna Zaune) a Qaadisiyyah, sai aka wuce da gawa a gabansu, sai suka miqe tsaye, sai wasu sukace musu: "Cewa ita (wannan gawar) ta mutanen kasa ne (kafuran garin)" sai sukace *"(Lalle Manzon Allah sallallahu alaihi Wa sallam, an wuce da gawa saiya tashi tsaye, wasu sukace: Shin shi (gawar) ba bayahude bane??? Sai (Manzon Allah) yace: Toh shi ba rai bane??)*._
_*(Muslim, 960)*_

An so ga mutum idan aka wuce da gawa, ya tashi tsaye gareta, domin Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) yayi Umarni da haka, kuma ya aikata, sannan ya bari (ya daina tashi tsaye). Aikata tashin da kuma rashin tashi, rashin tashin domin ya bayyana cewa tsayuwar ba wajibi bace.

_*(Majmu'ul Fataawa Wa Rasaa'il na Ibn Uthaymeen, 17/112)*_




والله أعلم،

***********************************


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.


_*🌙Tambayoyin*_ _*Musulunci🌙*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_
Share:

Monday, 11 September 2017

Menene hukuncin mata masu huda hanci A musulunchi ??



```ASSALAMU ALAIKUM!!!```
```MENENE HUKUNCIN MATA MASU HUDA HANCI??````



_*AMSA:*_
********


وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ


An tambayi _*Shaykh Muhammad Saalih Al-Uthaymeen (Rahimahullah)*_ gameda Huda Hanci da Huda kunnuwa da ake yiwa yara mata saboda suyi kyau? Sai yace:
Ra'ayin da yake daidai shine babu laifi akan Huda kunne, saboda daya daga cikin dalilan huda kunne shine sanya halatattun kayan ado (Yan Kunne). An san cewa mata sahabbai sunada yan kunne da suke sanyawa a kunnuwansu.

Zafin ciwon hudawar mai sauki ne, kuma idan anyi huduwar ne a lokacin da yarinya tana karama, yafi saurin warkewa.


Abinda ya shafi *HUDA HANCI* kuma bazan iya tina cewa malamai sunce wani abu akan Huda Hanci ba, amma dai wani nau'in ne na canza halitta da gurguntawa idan muka kalli fuskar daga wajenta, duk dayake wasu basa kallonsa ta wannan fuska.

Idan mace tana acikin kasa ko gari Wanda sanya kayan ado a Hanci ana kallonsa wani nau'i ne na kwalliya da ado, to, babu wani abin laifi ga huda Hanci.
_*(Majmu'ul Fataawa Ibn Uthaymeen, shafi na 11, tambaya ta 69).*_



والله أعلم،

***********************************


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.


_*🌙Tambayoyin*_ _*Musulunci🌙*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_
Share:

Tuesday, 5 September 2017

MU KYAUTATAWA JUNA ZATO

*MU KYAUTATAWA JUNA ZATO*

*_WANI DAGA CIKIN SALAF (MAGABATAN FARKO NA KWARAI) YANA CEWA:_*

_*Idan naga ruwan giya suna zubowa daga gemun mutum, to zance giyar ta zubar masa ne*_  Wato abinda yake nufi anan tunda dai bai ganshi yana shan giyar ba a zahiri ba to lallai ba zaice ya ganshi yana shan giya ba.

*HAKA KUMA YA QARA DA CEWA:*

*_Haka kuma idan na ganshi a saman tsololuwar tsauni yana cewa_; " *NI NE UBANGIJINKU MAFI DAUKAKA* " ( *ANA RABBUKUMUL A'ALA* ). *_Anan kuma zance wannan yana karanta_* *AYA CE DAGA AL-QUR'ANI MAI GIRMA*

Kaji *swalihan* bayi kenan, duk fa wannan yana yine akan tsananin kyautatawa musulmi zato, yi masa uzuri da kuma gujewa yin shaidar zur.

Yanzu mutanen wannan zamanin wa zaiga giya na zuba daga gemun mutum yace wai ba giyar ce ya gama sha ba? Haka kuma wa zai ga mutum saman qololuwar tsauni yana kwala ihu yana fadar *_NI NE UBANGIJINKU MAFI DAUKAKA_* Har yace bawai kansa yake kira Allah ba, ai ayar qur'ani ce yake karantawa?

Kuma wannan itace dabi'ar da ake son musulmai su dabi'antu da ita ta kaucewa yin shaidar zur, kyautatawa juna zato da kuma gujewa munanawa musulmi zato kamar yanda dimbin ayoyin Al-qur'ani da ingantattun hadisai suka hore mu.

*Allah ya bamu ikon kyautatawa junanmu zato. Ameen*

*TAMBAYOYIN MUSULUNCI*


Share:

Wednesday, 23 August 2017

Shin yana halatta ladan ya rinqa amshi acikin sallah (wato yarinqa kwaikwayon liman??)

```Assalamu alaikum
Tambayata shin ya halatta ladan ya rinqa amshi acikin sallah wato yarinqa kwaikwayon liman??```


_*AMSA:*_
*******

ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ


Liman zaiyi kabbarar harama da sauran kabbarori acikin murya da mamunsa zasuji kabbarorin sa.

Idan kuma masallacin babba ne, kuma muryar Liman bazata riski kunnuwan duk masu binsa sallah dake bayansa ba, wata kil saboda rashin lafiyarsa ko rashin karfin muryarsa ko kuma yanayin halittar sa kenan. A wannan yanayi, daya daga cikin mamunsa zai daga muryarsa ya jiyar da sauran masu bin sallar.

Dalili shine hadisi ya inganta cewa _*Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam)*_ ya jagoranci sallah a lokacin da baida lafiya, sai *Abubakar (radhiyallahu anhu)* ya jiyar da mutane kabbarori (Ta hanyar daga sautin muryarsa).

Idan sautin muryar Liman yana riskar duk mutanen dake bayansa, to anan bidi'ah ne wani mutum daga cikin mamu ko Ladan ya daga sautinsa sama da sautin muryar Liman a kabbarori.

Mai Neman karin bayani ya duba
_*(Mawaahibal Jaleel, 2/196)*_ ko
_*(Al-Taaj wal ikleel 1/532).*_




والله أعلم،

***********************************


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.


_*🌙Tambayoyin*_ _*Musulunci🌙*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_

KARKU MANTA DA GAYYATO MANA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.
Share:

Thursday, 17 August 2017

yaya hukuncin yin lalle ga mace mai niyyar yin laiya? Hukunci daya ne dana kitso in watan Zhul hijjah ya tsaya?

```Assalamu alaikum
Akaramukallah, ina da tambaya yaya hukuncin yin lalle ga mace mai niyyar yin laiya?  Hukunci daya ne dana kitso in watan Zhul hijjah ya tsaya?  Ko ko banda lalle?  Ya abin yake ne Allah ya kara lafiya```



_*AMSA:*_
*******

وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،


Ya halatta mace mai niyyar yin laiya tayi lalle acikin kwanaki goma na farkon watan Zhul Hijjah. Saboda lalle baya cire wani abu daga jikin mutum misali kamar gashi ko akaifa da sauransu.

Haka kuma ya halatta ta sanya turare ko sabuwar sutura da sauransu.

Haramcin ya takaita ne ga duk wani abu da zai zama sanadin cire wani abu daga jikin Dan Adam.



والله أعلم،

***********************************


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.


_*🌙Tambayoyin*_ _*Musulunci🌙*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_

Karku manta gayyato mana abokananku zuwa wannan shafin mun gode.
Share:

Monday, 14 August 2017

Shin wacce addu'a ce idan karoki Allah da ita yake gaggawar amsawa ???

```ASSALAMU ALAIKUM
Tambaya ta itace wacce addu'a ce idan karoki Allah da ita yake gaggawar amsawa.```



_*AMSA:*_
*******

وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،


A iya karamin ilimin mu bamu san wata kebantanciyar addu'a ba wacce *Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wa sallam)* ya koyar a karanta domin samun biyan bukata Cikin gaggawa. Sannan kuma bai halatta ga musulmi yayi addu'a yace yana son Allah ya biya masa da bukatarsa nan take, ko kuma a lokaci qayyadadde. Saboda Shi Allah ba'a sanya masa lokaci a biyan bukatar mai addu'a.

Amma mutum zai duqufa yana rokon Allah ya biya mass bukatunsa na alkhairi.

Addu'a itace makami mai kaifi da mumini/mumina zai/zata yi amfani wajen yanke duk wata matsala dake a gabansu.

Allah madaukakin sarki yana cewa acikin Al-qur'ani:

ﻭَﻟِﻠَّﻪِ ﺍﻷَﺳْﻤَﺎﺀُ ﺍﻟْﺤُﺴْﻨَﻰ ﻓَﺎﺩْﻋُﻮﻩُ ﺑِﻬَﺎ.

_*Allah yanada sunaye kyawawa Ku rokeshi dasu.*_

Manzon Allah ya koyar damu yadda zamu roki Allah da sunayensa kyawawa.  Kamar yadda yazo a ingantaccen hadisi kamar haka:

ﺃﺳﺄﻟﻚ ﺑﻜﻞ ﺍﺳﻢ ﻫﻮ ﻟﻚ ﺳﻤﻴﺖ ﺑﻪ ﻧﻔﺴﻚ، ﺃﻭ ﺃﻧﺰﻟﺘﻪ ﻓﻲ ﻛﺘﺎﺑﻚ، ﺃﻭ ﻋﻠﻤﺘﻪ ﺃﺣﺪﺍً ﻣﻦ ﺧﻠﻘﻚ ، ﺃﻭ ﺍﺳﺘﺄﺛﺮﺕ ﺑﻪ ﻓﻲ ﻋﻠﻢ ﺍﻟﻐﻴﺐ ﻋﻨﺪﻙ

Akwai wasu lokuta idan bawa yayi addu'a Allah na karba masa kai tsaye. Misali kamar sulusin dare na karshe kamar yadda ya tabbata a hadisi.

Yana daga cikin sharadin addu'a musulmi ya kasance *babu haram* a cikinsa (baici abincin haram ko abin sha na haram ba), musulmi ya kasance *bai yanke zumunta ba,* ya kasance *baiyi gaggawa ba,* kuma ya kasance ya *zabi kyakkyawan lokacin yin addu'a,* sannan ya nisanci *Neman gaggawar karbawa.* ya tabbata a hadisi cewa;

عن أبي هريرة قال، ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ: ﻳﺴﺘﺠﺎﺏ ﻷﺣﺪﻛﻢ ﻣﺎ ﻟﻢ ﻳﻌﺠﻞ، ﻳﻘﻮﻝ: ﺩﻋﻮﺕ ﻓﻠﻢ ﻳﺴﺘﺠﺐ ﻟﻲ.
*ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏(5865) ﻭﻣﺴﻠﻢ ‏(2735).*

_An karbo daga *Abu Hurayrah (R.A)* yace; *Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam)* yace: (Allah) yana karbawa dayanku (addu'arsa) matuqar baiyi gaggawa ba, (shine) yace nayi addu'a (amma har yanzu) ba'a amsamin ba._
_*(Bukhari, 5865.  Muslim, 2735).*_

Muna rokon Allah ya biya mana daukacin bukatunmu na alkhairi baki daya. Allah ka albarkaci al'ummar Musulmai a duk fadin duniya........Amin summa amin.



والله أعلم،

***********************************


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.


_*🌙Tambayoyin*_ _*Musulunci🌙*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_

Share:

SHIGAR BALAGAGGUN SAMARI GIDAJE KAI TSAYE BA TARE DA HIJABI BA

MUSIBA TA UKU:
SHIGAR BALAGAGGUN SAMARI GIDAJE KAI TSAYE BA TARE DA HIJABI  BA.
))))))))))))))))))))))))))))

YANA DAGA MUMMUMAN RASHIN SANIN CIWON KAI,  DA RASHIN KISHI , BARIN BALAGAGGUN SAMARI SHIGA GIDAN MATAN AURE.

WANI SANANNE MUTUM DANA YARDA DASHI YA BANI LABARI CEWA: WANI ABOKINSA YANA BARIN KANNENSA SUNA SHIGA GIDANSA KOWANE LOKACI,  BAYAN WANI ZAMANI SAI SAI YA KAMA MATARSA DA QANENSA SUNA ZANCEN SOYAYYA BASU SAN YANA JINSU BA!  HAR MA QANEN  YAKE CEWA. AI FATANA WANNAN YA MUTU IN AUREKI!!

TO IDAN QANE YAYIWA YAYANSA WANNAN CIN AMANAR,  YAYA KUMA WANDA BA DAN, UWA BA?.

AKWAI WANI ALMAJIRI DA YAKE YAN WANKE WANKE DA AIKACE AIKACE A WANI GIDA  , KULLUM DA SAFE ZAIJE GIDAN BAZAI TAFIBA SAI AZAHAR IN AN BASHI ABINCIN RANA,  SHI KUMA MAI GIDAN BA MAZAUNI BANE,  WATA RANA SAI MATAR GIDAN TA  SHIGA DAKI TAYI TSIRARA TA KIRASHI SAI YAJE BAYAN YAGANTA A YANAYIN DA BAI TABA GANINTA BA SAI YA RAZANA YA JUYO SAI TA KIRASHI TACE YAZO YA SAKA MATA RIGA WAI BATA DA LAFIYA!  SHI KUMA YARO YAQI,  SAI YA TONA MATA ASIRI SAI MAI GIDA YA SAKETA YA SAKE WANI AUREN.

TO SABODA YARDARSA DA YARON SAI YA BARSHI YACI GABA DA AIKI.

BAYAN WASU SHEKARU. YARO YA QARA GIRMA BALAGA TA FARA CINSA,  KAWAI MACE TANA BACCI SAI JINSA TAYI A KUSA DA ITA YA KWANTA YACE MUYI!

SAI TA KAMASHI TA. KURMA MASA IHU!!...

2. YAN GARUWA MASU KAI RUWA GIDA A LURA DASU MAFI YAWANSU SUNA ZUBA RUWA SUNA KALLON MATAN GIDAN KO YAN MATAN GIDAN,  DAN HAKA AYI TSARI KAR SU SHIGA SAI  ANCE SU SHIGO KUMA KAFIN A BASU IZINI MATA SU KOMA DAKI,  DOMIN WANI SA, IN ANA SAMUN YAN GARUWA FULANI MASU KYAWUN HALITTA KAGA IN MACE BA ME KAMUN KAI BACE SAI TA RINQA KALLONSA KODA SHI BA KALLA BA.!

3. KAFINTOCI MASU BUGA RAFTA  SUMA A LURA DASU KAMAR YANDA MUKA SANI DOKACE KAR SU HAU SAMA SAI SUN NEMI IZINI,  TO WANI SA'IN MATSALAR AWAJEN MATAN GIDAN TAKE ABIN HAUSHI MEMAKON DA AKA SANAR DASU , SU KOMA DAKUNA KOMA SU TAFI MAQWAFTA SAI AN GAMA SU DAWO,  KO SU SANYA HIJABAI IN LARURA TA SA ZASU FITO TSAKAR GIDA.  ABIN TAKAICI SAI KA GANSU SUNA YAWO A TSAKAR GIDA DA DAURIN QIRJI  GA KAFINTA KO. MAGINI A SAMA, KAGA HAKAN BA QARAMIN KUSKURE BANE.

4. MASU RUQIYYA: SUMA A LURA DASU BE KAMATA BA ABAR ME RUQYA DAGA SHI SAI MACE YANA MATA KARATU,  WANI SA'IN AKAN SAMI MAHA'INTA.

5. SAMARIN UNGUWA: KUSKURE NE SABODA YARO DAN UNGUWANE KO SABODA TUN YANA QARAMI YAKE SHIGA GIDAN MUTANE,  KUMA BAYAN YA. ZAMA VALIGI A BARSHI YACI GABA DA SHIGA,  .

6. BARIN BUDURWA TSARON GIDA ITA KADAI A GIDA TARE DA CEWA SAMARI NA. KAI QAFA GIDAN.  WANNAN MUMMUNAR AL'ADACE DA TA ZAMO WATA HANYA MAI SAUQI WAJEN  BATA YAN MATA A GIDAN IYAYENSU.

7 DAN WA DA DAN. QANE : WANI SA'IN ZAKA SAMU A GIDA DAYA AKWAI YAYAN YAN UWA  WADANDA AKWAI AURE A TSAKANINSU AN SAKE SU SUNA ABINDA SUKA GA DAMA DA YAN MATAN GIDAN,  SU SHIGA DAKI SU  SU KADAI SU RAFI UNGUWA TARE TO WANNAN MA YANA. MATUQAR. WATSA  YAN MATA TA INDA IYAYE BASU SANI BA.

8 . DAUKAR MALAMI EXTRA LESSON A BARSHI SJI KADAI DA YAN MATA A WANI DAKI,  TO WASU LOKUTAN ANA SAMUN SAURAN BASA NAN SAI BUDURWA DAYA KO ITA DA QANANAN YARA YAU DA GOBE SAI SHAIDAN YA  SHIGA TSAKANINTA DA MALAMIN.

9. SHIGO DA SAURAYI ME NEMAN  AUREN YARINYA CIKIN GIDA  CIKIN SITROOM KO SORO  SU ZAUNA SU BIYU.
WANNAN. MA MUMMUNAR VARAKACE DA TAKE MISALTA RASHIN KISHIN. IYAYEN YARINYAR.  SAU DA YAWA HAKAN YAKAN KAI GA WASANNIN BANZA SAGA BISANI ZINA GA GIFTA.

10. BARIN ABOKI SHIGA GIDA TARE DA KAI KO SHI KADAI.      MATSALAR SHIGARKU TARE HAKAN ZAISA YAYI SABO DA IYALINKA  WANDA HAKAN ZAI IYA BAYUWA GA YA RINQA TSAYAWA SUNA TATTAUNAWA DA MATARKA A HANYA KO A WAYA DUK DA SUNAN MATAR ABOKINSA.

SHIGARSA GIDAN KA BAKA NAN,  WANNAN SHINE MAFI MUNI.  DOMIN HAKAN YAKAN KAI GA KWARTANCI,  MA'A-ZALLAH!.

A JUMLACE: WAJIBI NE MUYIWA GIDAJENMU TSARI MU DENA BARIN KOWA YA SHIGA GIDAN MU WANDA BA. MAHRAMIN MATAN GIDAN BA.  IDAN KUMA. LARURA TA KIRA TO SU SHIGA DAKI  SANNAN SU SANYA HIJABI,  IDAN ZASU FITO TSAKAR GIDA.

KAR KA MANTAN DAN UWA DA HADISIN DA MUKA KAWO CEWA MARAS KISHIN IYALINSA BAZAI SHIGA ALJANNA BA.

✍Abubakar Zubairu Abu Aisha
Share:

Saturday, 12 August 2017

bayani daga farko har karshe akan yadda ake sallar gawa!!!


​​​Assalamu alaikum
Malam Don Allah ina so ka yi mana bayani akan sallar gawa  domin gaskiya mutane da yawa bamu san yadda ake yin sallar ba illa muna tsaye ne kawai har a gama, abin yanada muni sosai ba kadan ba.​​​



​​AMSA:​​
*******

وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،


Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) da Sahabbansa (radiyallahu anhum) sunyi bayanin yadda ake yin Sallar Gawa. Ana yinta ne babu ruku'u babu sujuda. Kuma ana yinta ne kamar haka:

​1.​ Zakayi kabbara ta farko kace ​​Allahu Akbar​​ sannan kace ​​A'uzhu billahi minasshaydanir rajiim​​ sannan kace ​​Bismillahir rahmanirrahiim​​ sannan ka karanta ​​Suratul Fatiha​​ sannan ka karanta ​​gajeruwar Surah ko wasu ayoyi.​​

​2.​ Sannan kayi kabbara ta biyu kace ​​Allahu Akbar​​ sannan kayiwa Annabi salati, irin Wanda akeyi bayan tahiya cikin sallah.

​3.​ Sannan kayi kabbara ta uku, kace ​​Allahu Akbar​​ sannan kayiwa mamaci addu'a, wannan itace addu'ar da aka karbo daga Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) kuma itace tafi inganci:

​​​ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﺤﻴﻨﺎ ﻭﻣﻴﺘﻨﺎ ﻭﺷﺎﻫﺪﻧﺎ ﻭﻏﺎﺋﺒﻨﺎ ﻭﺻﻐﻴﺮﻧﺎ ﻭﻛﺒﻴﺮﻧﺎ ﻭﺫﻛﺮﻧﺎ ﻭﺃﻧﺜﺎﻧﺎ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻣﻦ ﺃﺣﻴﻴﺘﻪ ﻣﻨﺎ ﻓﺄﺣﻴﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻹﺳﻼﻡ ﻭﻣﻦ ﺗﻮﻓﻴﺘﻪ ﻣﻨﺎ ﻓﺘﻮﻓﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻹﻳﻤﺎﻥ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻪ ﻭﺍﺭﺣﻤﻪ، ﻭﻋﺎﻓﻪ ﻭﺍﻋﻒ ﻋﻨﻪ، ﻭﺃﻛﺮﻡ ﻧﺰﻟﻪ، ﻭﻭﺳﻊ ﻣﺪﺧﻠﻪ، ﻭﺍﻏﺴﻠﻪ ﺑﺎﻟﻤﺎﺀ ﻭﺍﻟﺜﻠﺞ ﻭﺍﻟﺒﺮﺩ، ﻭﻧﻘﻪ ﻣﻦ ﺍﻟﺨﻄﺎﻳﺎ ﻛﻤﺎ ﻳﻨﻘﻰ ﺍﻟﺜﻮﺏ ﺍﻷﺑﻴﺾ ﻣﻦ ﺍﻟﺪﻧﺲ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺃﺑﺪﻟﻪ ﺩﺍﺭﺍً ﺧﻴﺮﺍً ﻣﻦ ﺩﺍﺭﻩ ﻭﺃﻫﻼً ﺧﻴﺮﺍً ﻣﻦ ﺃﻫﻠﻪ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺃﺩﺧﻠﻪ ﺍﻟﺠﻨﺔ ﻭﺃﻋﺬﻩ ﻣﻦ ﻋﺬﺍﺏ ﺍﻟﻘﺒﺮ ﻭﻣﻦ ﻋﺬﺍﺏ ﺍﻟﻨﺎﺭ ﻭﺍﻓﺴﺢ ﻟﻪ ﻓﻲ ﻗﺒﺮﻩ ﻭﻧﻮﺭ ﻟﻪ ﻓﻴﻪ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻻ ﺗﺤﺮﻣﻨﺎ ﺃﺟﺮﻩ، ﻭﻻ ﺗﻀﻠﻨﺎ ﺑﻌﺪﻩ.​​​

   ​​“Allaahumma ighfir li hayyinã wa mayyitinã wa shaahidinã wa ghaa’ibinã wa sageerina wa kabeerinã wa zakarinã wa unthaanã.​​
   ​​Allaahumma man ahyaytahu minnã fa ahyihi alal-Islam wa man tawaffaytahu minnã fa tawiffahu alal-imaan.​​
   ​​Allaahumma ighfir lahu warhamhu wa aafihi wa a’fu anhu, wa akrim nuzulahu wa wassi’i madkhalahu wagsilhu bil-maa’i wal-salju wal-barad, wa naqqihi minal khaadaaya kamã yunaqqaal thawbal abyadu minal danas.​​
   ​​Allaahumma abdilhu daaran khayran min daarihi wa ahlan khayran min ahlihi.​​
   ​​Allaahumma adkhilhu al-jannah wa a’izhu min azaabal qabri wa min azaabin naar wa afsah lahu fi qabrihi wa nawwir lahu fihi.​​
   ​​Allaahumma laa tahrimna ajrahu wa laa tadillanaa ba’dahu."​​

Idan mutum yayi addu'a da wash kalmomi babu laifi a hakan. Kamar yace:

_​​​ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﺤﺴﻨﺎً ﻓﺰﺩ ﻓﻲ ﺇﺣﺴﺎﻧﻪ، ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﺴﻴﺌﺎً ﻓﺘﺠﺎﻭﺯ ﻋﻦ ﺳﻴﺌﺎﺗﻪ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻪ ﻭﺛﺒﺘﻪ ﺑﺎﻟﻘﻮﻝ ﺍﻟﺜﺎﺑﺖ.​​​_

​​“Allaahumma in kaana muhsinan fa zid fi ihsaanihi wa in kaana musee’an fa tajaawaz an sayi’aatihi.​​
​​Allaahumma ighfir lahu wa thabbit-hu bil-qawlil-thaabit."​​

​4.​ Sannan kayi kabbara ta hudu kace ​​Allahu Akbar​​ sai kayi shiru na dan lokaci kadan, sannan saika sallame a gefenka na dama kace ​​Assalamu alaikum wa rahmatullahi.​​

Wannan shine takaitaccen abinda ya tabbata a Sunnah na Sallar gawa.

​Kitaab Majmu'ul Fataawa wa Maqaalaat Mutanawwi'ah li samaahatal Shaykh Abd al-Azeez ibn Abd-Allaah ibn Baaz (rahimahullah) Mujalladi na 13, shafi na 14}​



والله أعلم،

***********************************


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.


​​🌙Tambayoyin​​ ​​Musulunci🌙​​
            ​​WhatsApp​​ ​​Group​​
Share:

Friday, 11 August 2017

Wai shin Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) Umrah nawa ya yi kafin ya bar duniya?


​​​Assalamu alaikum
Wai shin Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) Umrah nawa ya yi kafin ya bar duniya? Ba fa aikin hajji ba❌ no! Umrah​​​


​​AMSA:​​
*******

وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ


​An karbo Daga ​Qataadah​ cewa ​Anas (Radiyallahu Anhu)​ ya fada masa cewa ​Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam)​ yayi ​UMRAH​ ​SAU​ ​HUDU​ dukansu acikin watan Zhul Qi'dah banda Umrah da yayi tareda Hajjinsa:​
​(Yayi) Umrah daga Al-Hudaybiyah ko kuma a lokacin Al-Hudaybiyah acikin watan Zhul-Qi'dah, (ya sake yin) Umrah a shekarar data zagayo acikin watan Zhul-Qi'dah, kuma (yayi) Umrah daga Ja'raanah lokacin da ya raba ganimar yaqin Hunayn acikin watan Zhul-Qi'dah.​
​​(Bukhaari, Al-Hajj, 1654. Muslim, Al-Hajj, 1253).​​


​Ibn Al-Qayyim​ yace; ​(Manzon Allah) yayi Umrah sau hudu bayan hijrah,​ Umrah hudu dukansu acikin ​Zhul-Qi'dah.​
​Ta farko itace ​Umrah ta Al-hudaybiyyah​​ kuma itace ta farko acikinsu, a shekara ta 6 bayan hijrah, Amma mushrikai sun hanashi yakai ga daki ​(Ka'abah).​ Ya soke rakumansa na layyah a hudaybiyyah bayan an tare masa hanyar shiga Makkah, shi da sahabbansa sun aske gashin Kansu sannan sun fita harami, sun koma Madinah acikin wannan shekara.
​​Umrah ta biyu cikakkiyar Umrah ce​​ a shekara ta 7 bayan hijrah lokacin da ya shiga Makkah ya tsaya ciki har (kwana) 3 sannan ya fita bayan ya kammala Umrah.
​​Umrah ta uku​​ itace Umrah da yayi tareda ​Hajjinsa​
​​Ta hudu itace​​ Umrah daga ​Al-Ja'raanah,​ lokacin da ya fita yaqin ​Hunayn​ sannan ya dawo Makkah yayi Umrah daga Al-ja'raanah.

​IbnAl-Qayyim​ yace babu sabanin ra'ayin malamai akan cewa ​Umrah hudu ne yayi​
Duba:
​​(Za'ad al-Ma’aad, Mujalladi na 2, shafi na 90-93)​​


​Al-Nawawi yace:​
Malamai sunce: Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) wadannan Umrah ne acikin waan Zhul-Qi'dah saboda ya nuna falalar watan Zhul-Qi'dah, ya kuma rusa ra'ayin zamanin jahiliyyah da suke tinanin yin Umrah cikin Zhul-Qi'dah yana cikin mafi munin mummunan aiki.

Saboda haka ​Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam)​ yayi Umrah har sau hudu acikin watan Zhul-Qi'dah saboda wannan itace gamsasshiyar hanyar nuna halaccin yin Umrah a watan Zhul-Qi'dah, da kuma nuna cewa tinanin jahiliyyah akan watan Zhul-Qi'dah karya ne.
​​(Sharh Muslim, 8/235)​​



والله أعلم،

***********************************


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.


​​🌙Tambayoyin​​ ​​Musulunci🌙​​
            ​​WhatsApp​​ ​​Group​​
Share:

Tuesday, 8 August 2017

HUKUNCE-HUKUNCEN JININ HAILA:MEYE YA HARAMTA GA MAI JININ HAILA DA KUMA JININ HAIHUWA?

HUKUNCE-HUKUNCEN JININ HAILA
***************007*******************
MEYE YA HARAMTA GA MAI JININ HAILA DA KUMA JININ HAIHUWA?
***************************************
Kamar yanda nayi maku bayanin ababe guda biyu da basu halatta ga mace mai jinin haila ko jinin biiqi su aikata ba acikin bayanan mu na 006 kuma aciki na kawo abu na uku amma saboda kada rubutun ya tsawaita yawa sai nace zamu maimaita matsala ta uku kuma muyi cikakken bayani akan ta, don haka sai mu bada himma wajen kiyaye dokokin Allah madaukaki kafin yayi fushi damu,  "Babu masu kafirce wa ayoyin Allah (a lokacin da ayar tazo masu) sai dai fasikai" (Baqarah aya ta 99)
.
3:-   SADUWA DA MACE:- Haramun ne saduwa da mace alhali tana yin jinin haila ko jinin biiqi (haihuwa) kamar yanda mukace maku zamu kawo maku dalilai daga Littãfin Allah ta'ala da kuma hadisan da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yayi hani da kuma maganganun malamai (magabata) akan wannan matsalar in shaa Allah, muna rokon Allah madaukakin sarki yataimake mu,
.
(1):-   "KUMA SUNA TAMBAYAR KA GAME DA HAILA KACE, SHI CŨTA NE, SABÕDA HAKA KU NĨSANCI MÃTÃ A LOKACIN DA SUKE HAILA KUMA KADA KU KUSANCE SU SAI SUNYI TSARKI, TO IDAN SUNYI WANKA SAI KUJE MASU TA INDA Allah YA UMURCE KU, LALLAI NE ALLAH YANA SON MÃSU TŨBA KUMA YANA SON MÃSU TSARKAKẼWA"  (Baqarah aya ta 222)
.
'Yan uwa kunga wannan aya ce karara da take nuna Haramcin saduwa da mace alhali tana yin jinin haila ko jinin biiqi (haihuwa) karara Haramun ne babu wani sassauci matukar saduwa ne to Haramun ne 'yan uwa don haka sai mu rike wannan ka'idar ta haramcin da nassin Al-Qur'ani, amma kuma ba'a hana kaba cewa tasan yanda tayi ta biya maka bukatun ka ba amma dai banda saduwa, abinda nakeso nace maka shine komai ajikin ta ya halatta a gareka sai dai banda Jima'ei, dalili kuwa hadisi ya tabbata acikin Bukhari da Muslim daga A'isha Allah ya kara mata yarda tace, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kasance  Yana umurta ta da nayi Qunzugu sai ya rungume ni alhali ina haila " (Duba Sahihu Muslim hadisi na 293, Bulughul-Maram shafi na 71 hadisi na 156).
.
Kuma akwai hadisi acikin Sahihu Muslim Daga Anas Allah ya kara masa yarda yace, lallai su yahudawa sun kasance idan matar su ta kasance tana haila acikin su, basu cin abinci tare dasu (Basu cin abincin su) sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace  "Ku aikata komai tare dasu amma banda saduwa"  (Duba Sahihu Muslim hadisi na 302, Bulughul-Maram shafin da mukayi ishara dazu hadisi na 155, Fiqhul-Muyassir na Sa'ad Yusuf shafi na 56) Haka kuma dai har wayau akwai hadisi da yake acikin sunan na Abiy-Dawuda daga Ikramah yace, daga sashin matan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, lallai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kasance idan yana bukatar wani abu a wajen matarsa alhali tana yin jinin haila, yana umartan ta ta tayi Qunzugu"  (Duba Sunan na Abiy-Dawuda hadisi na 242, Fiqhul-Muyassir shafin da mukayi ishara dazu) kuma ba'a kyamatar mata idan suna haila, duk wanda ya kyamaci mace saboda tana haila to ya dauko al'adar jahiliyya ya kawo cikin musulunci, wato ina nufin ya dauko aqeedun maguzawa ya kawo cikin addinin musulunci, wanda kuma ya rike wannan siffar to yayi kama da yahudu, Allah ta'ala ya tsare mu,
.
Duk wanda ya sadu da matar sa alhali tana yin jinin haila ko jinin biiqi (haihuwa) to ya sa6a ma Allah kuma ya sa6a wa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, haka kema idan kika amince masa kin sa6a ma Allah kuma kin sa6a wa Manzon Allah, ki karkade kunnen ki kiji ni yake  'yar uwa idan kina under jinin haila ko jinin biiqi mijin ki yazo maki to anan gurin Haramun ne kiyi masa biyayyah, kamar yanda mal Sa'ad Yusuf acikin Littãfin sa Fiqhul-Muyassir shafin da mukayi ishara dazu, yace   "Baya halatta ga mace ta amince wa mijin ta ya kwanta da ita Alhali tana yin jinin haila ko jinin biiqi, (idan ya nemeta kada ta kuskura tayi masa biyayyah) domin kuwa babu yin biyayyah ga abokin halitta a wajen sa6a wa mahalicci",
.
Wannan shine abinda Allah ta'ala ya kaddara min na kawo maku akan haramcin saduwa da mace alhali tana yin jinin haila ko jinin biiqi (haihuwa) Allah ta'ala ya bamu ikon kiyaye dokokin sa kamar yanda ya shar'anta mana, don haka yake 'yar uwa kiyi kokari ki nemi rubutun da suka wuce a baya matukar baki samesu ba tun daga 001 har zuwa 006, domin tanan ne zaki iya fahimtar ina muka dosa, kaima dan uwa kada kayi kasa a gwiwa, Allah ta'ala yayi maku albarka, Allah ta'ala yayi mana jagoranci, wannan shine karshen kaset na 007 kuma da yardan Allah acikin kaset na 008 da zai zo nan gaba zamuyi bayani ne akan HUKUNCIN WANDA YA KWANTA DA MATAR SA ALHALI TANA HAILA, Allah ta'ala muke roko ya kar6a mana, Allah yasa Mudace, Assalamu Alaikum warahmatullahi wabarakatuh
.
Hussaini Haruna Ibn Taimiyyah Abu-Nabeelah Kuriga
.
                   **17/10/1438**
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp
Share:

Shin A goman farko watan zulhajj da ba'a aski da yankan farce harda wanda bazaiyi layya ba ??

​​​Asalamu alaikum​​​
​​​A goman farkon watan zulhajj da ba'a aski da yakan farce harda Wanda bazaiyi layya ba?​​​


AMSA:
*******

ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ


Idan watan Zul-hijja ya fita, haramun ne ga duk wanda yake da niyyar yin layya ya aske gashinsa ko yanke farcensa a kwana goma na farkon watan.

An ruwaito daga ​Ummu Salama (radiyallahu anha)​ cewa ​Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam)​ yace:
​Idan kunga jinjirin watan Zulhijja, kuma dayanku yana nufin yin layya, to kar ya cire gashinsa kuma karya yanke farcensa.​
​​(Muslim 1977).​​

Wannan hukuncin yana aiki ne akan Wanda zaiyi layya kadai.
Baya aiki ga matarsa ko 'ya'yansa ko abokan aikinsa ko wani makusancinsa.
​​(Fataawa al-lajnah al-daaimah 11/397-398).​​

​Ibn Qudaamah​ yace:
Idan watan Zulhijja ya tabbata, to Wanda zaiyi layya kar ya aske gashinsa ko yanke farcensa ko cire wani abu daga fatarsa.
       Idan mutum ya aikata hakan to ya memi afuwar Allah kuma yayi istigfari.
​​(Al-Mughni 9/346).​​



والله أعلم،

***********************************


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.


​​🌙Tambayoyin​​ ​​Musulunci🌙​​
            ​​WhatsApp​​ ​​Group​​
Share:

Sunday, 6 August 2017

Menene hukuncin matar da tasha maganin tsaida al'ada alokacin aikin hajji ??

​​​Assalamu alaikum​​​
​​​Tambayata itace menene hukuncin matar da ta sha maganin tsaida Al'ada alokacin aikin hajji.​​​


​​AMSA:​​
*******

وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،


Da farko dai dawafin ifaadha rukuni ne acikin rukunnan aikin hajji, baya faduwa ga mace mai haila ko waninta. Amma mace mai haila bazata yi zagayen dakin ka'aba ba (dawafin dakin ka'abah) har sai idan tayi tsarki (Abin nufi shine idan jinin haila ya dauke mata kuma tayi wankan tsarki). Saboda fadar Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam);

ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻟﻌﺎﺋﺸﺔ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ﺣﻴﻦ ﺣﺎﺿﺖ ﻓﻲ ﻋﻤﺮﺓ ﺣﺠﻬﺎ - ﻭﻛﺎﻧﺖ ﻣﺘﻤﺘﻌﺔ:- ‏(ﺍﻓْﻌَﻠِﻲ ﻛَﻤَﺎ ﻳَﻔْﻌَﻞُ ﺍﻟْﺤَﺎﺝُّ ﻏَﻴْﺮَ ﺃَﻥْ ﻻ ﺗَﻄُﻮﻓِﻲ ﺑِﺎﻟْﺒَﻴْﺖِ ﺣَﺘَّﻰ ﺗَﻄْﻬُﺮِﻱ).
​ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏(1650‏) ﻭﻣﺴﻠﻢ ‏(1211‏).​

​​Annabi (sallallahu alaihi Wa sallam)​ yace da Uwar Muminai Aisha (radiyallahu anha) a lokacin da take haila a Umrah ta hajjinta - kuma hajjin tamattu'i ne, "Ki aikata duk abinda mahajjata ke aikatawa saidai banda dawafin daki sai idan kinyi tsarki".​
​​(Bukhari, 1650. Muslim, 1211)​​

An fada acikin ​​Al-Mawsuu'ah Al-Fiqhiyyah (18/320)​​ cewa babu sabanin ra'ayi a tsakanin malamai akan cewa haila baya hana mace aikata kowane irin aiki na hajji saidai dawaafi. Saboda ​Manzon Allah (sallallahu alaiho Wa sallam)​ yace da ​Aisha​ ​"Ki aikata komai na hajji amma banda dawaafin dakin ka'abah".​

Babu laifi mace tasha maganin da zai dakatar da zuwan al'adarta ko ya takaita lokacinta domin ta samu tayi dawaafi.

An tambayi ​Sheikh Abdul-Azeez bin Bazz (rahimahullah)​ cewa ​​​"Meye hukuncin matar da ta sha maganin hana al'ada a ranakun aikin hajji?" ​​​

Sai ya Amsa da cewa:
        Babu laifi a hakan, domin acikin hakan akwai fa'idah da maslaha, saboda ta samu damar yin dawafi tareda mutane kuma batareda tasa abokan tafiyarta sun tsaya jiranta yin dawafi ba.
​​Fataawa Al-Islamiyyah (2/185).​​

​Abdurrazzaq (rahimahullah)​ ya ruwaito acikin ​​Musannaf (1/318)​​ cewa an tambayi ​Ibn Umar (radiyallahu anhu)​ gameda mace wacce jinin al'adarta yake daukar lokaci mai tsawo yana zuwa mata, tana so tasha magani domin jinin ya tsaya, ​Ibn Umar​ baiga laifi ba a yin hakan, sannan ya nuna yin amfani da ​ruwan Araak​ (yace tayi amfani da ruwan Araak a matsayin maganin tsayar da jinin haila). ​Mu'ammar​ yace naji an tabayi ​Ibn Abi Nujayh​ akan hakan, kuma (shima ​Ibn Abi Nujayh​) baiga wani laifi ba akan hakan.

Wannan shine ra'ayin ​Shaikhul Islam Ibn Taimiyyah​ da ​Ibn Qayyim​ da ​Bin Bazz​ da ​Ibn Uthaimin​ kuma shine ra'ayin ​Malaman Al-lajnatu al-da'imah​ na kasar Saudiyyah.




والله أعلم،

***********************************


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.


​​🌙Tambayoyin​​ ​​Musulunci🌙​​
            ​​WhatsApp​​ ​​Group​​
Share:

Guzurin maniyyata aikin hajji (fitowa ta 06)

ISLAMIC SUNNAH

​>>GUZURIN MANIYYATA AIKIN HAJJI<<<​

Wallafar :- ​Mallam Abdus-salam Ibrahim Abubakar​ Rahimahullahu

   Rubutu na shida 06


بسم الله الرحمن الرحيم

Assalamu Alaykum, barka da war haka Mai karatu, Zamu tafi kai tsaye wajen bayaninda mallam ya mana akan abubuwa da ake buqatar mahajjaci yayi su a yayin haramar aikin hajjinsa.


​ABUBUWA DA AKE BUQATAR MAHAJJACI YA YISU YAYIN HARAMA.​

1.Yanke qumba idon akwai buqatar hakan.

2.Aski ko gyaran fuska ko saisaye amma banda aske gemu.

3.Aske gashin gaba dana hammata

4.Yin wanka da ruwa Mai tsarki.

5.Cire dukkan kaya dinkakku ga maza.

6.Cire niqabi da burka'a ga mata

7.Cire warwaro da dukkan kayan kwalliya ga mata.

8.Anfi son namiji ya sanya fararen kaya, mayafi da gyauto.

9.Bayan wanka ya halasta maniyyaci ya shafa turare a jikinsa kadai kafin yayi harama.

10.Mace zata sa turare itama amma mara qamshi sosai.

11.Anaso harama ta zama bayan sallar nafila idon ba lokacin sallar farilla bane, mustahabbi ne maniyyaci yayi sallar nafila raka'a biyu Sannan yayi harama.

Wayannan sune abubawa da ake buqatar mahajjaci yayi yayin harama kuma zamu dasa alqalami anan insha Allah, Darasi na gaba zanzo mana da bayani akan NAU'O'IN AIKIN HAJJI


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.


Daga Dan uwanku ​JAMEELU MASKA​

Islamic sunnah facebook
www.facebook.com/Islamicsunnah

Islamic Sunnah WhatsApp
+2348060618481

Instagram: Jameelumaska
E-mail: Jameelmaska@gmail.com
Share:

Guzurin maniyyata aikin hajji (fitowa ta 05)

​​>>GUZURIN MANIYYATA  AIKIN HAJJI<<<​​

wallafar :  ​Mallam Abdus-salam Abubakar Ibrahim​ Rahimahullahu

  Rubutu na biyar 05

بسم الله الرحمن الرحيم

​LOKACIN YIN HARAMA DA AIKIN HAJJI​

Lokacin yin harama da aikin hajji Yana farawa ne tun daga daya da watan Shawwal har I zuwa Tara ga watan zulhajj. Wanda yayi harama Kamin wannan lokacin to hajjinsa baiyi ba.

Wanda yayi harama da aikin hajji a safiyar Tara ga watan zulhajj Kuma ya samu tsayuwan arfa koda gwargwadon sa'a guda to hajjinsa yayi amma da sharadin asamu wani yankin dare a ciki


​WURAREN YIN HARAMA​

1 zulhulaifa :- wurinda akafi Sani a yanzu da abiyaru Aliyu, wannan Shine mikatin mutanen madina da Wanda suka biyo ta hanyar su.

2 Juhufa :- Shine mikatin mutanen Yamma da Misra da Shaam da wadanda suka biyo ta hanyar su.

3 Yalamlam :- Shine mikatin mutanen Yemen da Wanda suka biyo ta hanyar su.

4 Karnulmanazil :- Shine mikatin mutanen najadu da Wandanda suka biyo ta hanyar su.

5 Zatu'irkin :- Shine mikatin mutanen Iraqi da Wandanda suka biyo ta hanyar su.


​KARIN BAYANI (TANBIHI)​

1 Ga mazaunin cikin saudiya wanda gidansa bai kai mikati ba to Zaiyi harama ne a gidansa, saidai idon in gidan nasa yana cikin makka ne, watau cikin harami anan zai fita ne can hillu wato wajen makka ko kuma wajen harami sannan yayi haramar sa ta umara banda hajji.

2 Ga mazauna magrib da misira, da Shaam da sauran kasashen afirka to idon sunjeda Wuri sai su biyo ta madina domin suyi harama a zulhulaifa.

3 Ga wadanda suka makara zasuyi harama ne a jirginsu a yayinda akazo daidai mikati na Juhufah domin domin mikatin yana cikin ruwa ne a yanzu, idon akwai yuwa zasu yi wanka ne a cikin jirgi sannan su sanya ihirami, idon hakan bata samu ba su cire rigarsu sai subar wando sai sun sauka jirgin sannan su cire sai susa gyauto sannan su cire rigar da suka yafa a kafadunsu saisu yafa ihirami.

4 Duk wanda yayi harama a jidda to sai yayi fidiya ciyarwa ko ya yanka dabba ko yayi azumi, Domin yabar wajibi Daga cikin wajiban aikin hajji saboda jidda ba mikati bane, Duk da cewa akwai masu ganin cewa jidda mikati ne amma a hakikanin gaskiya basuda hujja a sunnah.

Anan zamu dakata insha Allah rubutu na shida Zaiyi bayanin ABUBUWA DA AKE BUKATA YAYIN HARAMA


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.

Daga dan uwanku ​ ​JAMEELU MASKA​​
Share:

Archive

Unordered List

Support