*HUKUNCIN SALLAR QASRU!!!???*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Taken Lekca........
.
*SALLAR QASRU!!!!??*
.
.
_Muna farawa da godema Allah, muna neman taimakonshi da agajinshi, wanda Allah ya shiryar shine cikakken shiryayye, wanda yabata kuma babu me shiryar dashi***_
.
_Dubban salati marasa adadi zuwaga shugabanmu uban dakinmu Annabi muhammad (s.a.w), Shugaban Halittu, mijin zainab kuma baban zainab (S.A.W)***_
.
_Bayan haka, hakika yau itace ranar juma,a 4-02-1438 wacce tayi dai dai da 4-11-2016, itace ranarda zan iya cewa kwari ya karye, tunda yau dai gashi Allah cikin ikonsa yabani ikon fara rubuta wannan bayanin, wanda yau kusan watannin hudu kenan inata cewa zanyi bayanin, toh yau ga ranar Allah yayi zamu gabatarda takaitaccen bayani na musamman gameda sallar qasru****_
.
_Abinda ake cema *QASRU* shine takaitawa, atakace wani abu daga yanda yake cikakkenshi sai a takaitashi***_
.
_Ibnul munzur yace: Malamai sunyi Ijma'i akan cewa Qasru ababin sallah shine arage yawan raka'oin sallah me raka,a hudu amaida ita raka,a biyu wannan shine abinda ake cema qasru, kuma malamai sunyi ijma,i akanta****_
.
_Itadai Qasru Allah ya ambacetane acikin Surata hudu ayata 101, inda Allah ta,ala yace: *KUMA IDAN KUNYI TAFIYA ACIKIN QASA, TOH BABU LAIFI AKANKU KURAGE DAGA SALLAH IDAN KUNJI TSORON WADANDA SUKA KAFIRTA SU FITINEKU, LALLAINE KAFIRAI SUN KASANCE, AGAREKU MAKIYI BAYYANANNE****_
..
_dogaro da wannan ayar itace take nuna mana cewa lallai qasrun sallah shari,ar musulincine****Abinda kuma ake cema qasru shine rage tsawon sallah me raka,a hudu, amaidata raka,a biyu a halin tafiya, kokuma alokacin tsoro ko yaqi, wanda qasru alokacin yaki harma raka,a daya anayi toh wannan shine qasru, kuma wannan ayar itace kadai acikin qur,ani wacce tayi magana akan sallar qasru kaitsaye***_
.
_Toh ita wannan ayar malaman tafsiri sunyi sabani akanta, shin tana maganane akan kasrun sallah ta tafiya zuwa unguwa? Kokuwa tana nufin qasrunda akeyine afagen yaki wato sallar tsoro??_
..
_toh malamai dai sunyi sabani, wanda shikanshi Malam Abubakar gumi dayazo tarjamar wannan ayar acikin tarjamarsa ta hausa shima yace wannan ayar tana maganane akan qasrun sallah alokacin yaki wato sallar tsoro, malamanda suke kan wannan fahimtar tacewa sallar tsoro ake nufi, sunyi la,akarine da sharadin da yazo acikin ayar inda Allah yace *IDAN KUNJI TSORON WADANDA SUKA KAFIRTA SU FITINEKU****_
.
_Ibn jarir Addabary acikin tafsirinsa mujallad na 5 shafina 287 yakawo wata ruwaya daga Aisha (Ra) wai ita takasance tana cewa ahalin tafiya: Kucika sallarku: sai akace mata Aikuma manzon Allah (s.a.w) yakasance yanayin qasru ahalin tafiya, sai tace: Aishi yanayin hakane alokacin yaki, kuma yana halin tsoro, shin kuma tsoron kukeji??? Toh wannan ruwayar bata ingantaba daga Aisha***_
.
_akwai dai ruwayoyi dadama wayanda sukazo gameda hukuncin sallar qasru, inda wayansu suke ganin cewa lallai dai sallar qasrunda wannan ayar take nufi anayintane alokacin tsoro, wato ansamu wayansu malamai wayanda suke kore yin sallar qasru ahalin tafiyarda bata yakiba***_
.
_Imamu Dabari yakawo wata ruwaya daga Aliyu dan Abu dalib, wayansu mutane 'yan kasuwa sunzo wajen Annabi (s.a.w) suka tambayeshi, ya Manzon Allah: mun kasance munayin tafiye tafiye abayan kasa toh shin yaya sallarmu zata kasance?? Sai aka saukarda farkon wannan ayar inda Allah yace: *IDAN KUNYI TAFIYA ACIKIN QASA, TOH BABU LAIFI AKANKU KURAGE DAGA SALLAH* iyaka nan wajen aka saukar, ba,a cigaba ba***_
.
_bayan haka da shekara daya sai manzon Allah yayi yaki kuma ya sallaci azahar awannan yakin, sai mushirikai suka fara fadar wayansu maganganu gameda Annabi da sahabbai sunaso sukulla musu makirci idan la,asar tayi: toh shine sai Aka saukarda cikon ayar wato inda yace: *IDAN KUNJI TSORON WADANDA SUKA KAFIRTA SU FITINEKU* toh wannan ruwayar itama bata ingantaba tanada rauni***aduba tafsirin Dabary mujallad na 5 shafina 286****_
.
_Toh amma bari muji raba gardama kai tsaye daga Annabi (s.a.w) shin Qasrun sallah anayintane ahalin tsoro kawai kokuwa ana iya yinta koda ba,a halin tsoroba??_
.
_Imamul Qurdubi acikin Tafsirinshi ALJAMI,U LI AHKAMUL QUR'AN mujallad na 5 shafina 261 yakawo hadisin Ya'ala bin umayyah***_
.
_Ya'ala bin umayyah yace: nacema sayyadina umar, shin mene yasa mukeyin qasru alhalin bama cikin halin tsoro? Kuma gashi acikin qur,ani Allah yaimana sharadine cewa babu laifi mu takaice sallah idan muna halin tsoro, toh mukuma meyasa muke takaice sallar bayan kuma gashi muna cikin aminci? Sai umar yace: Kayi mamakin abinda nima nataba yin mamaki akansa, sai na tambayi manzon Allah (s.a.w) gameda hakan? Sai yace: Ai ita qasru sadakace wacce Allah yayimuku ita dan haka kukarbi sadakarda Allah yaimuku***Imamu muslim yaruwaito wannan hadisin (686)_
.
_kenan duba da wannan hadisin zamu fahimta cewa lallai anayin qasru ahalin tafiya koda kuwa babu tsoro acikin tafiyar***_
.
_Toh masu karatu inaso ku ajjemin wannan hadisin da ita waccan ayar seku biyoni cikin bayani nagaba insha Allah zamu cigaba sesu zamar mana sune ginshikai wayanda zamu gina bayananmu akansu insha Allahu***_
.
.
_Almajirinku kamar kullun_
.
```Jameel Alhassan Haruna Kabo```
_(Abu khausar)_
.
.
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
https:/t/m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
Subhanak Allahumma wabi hamdika nash hadu anla ila ha illah anta nastagfiruka Wanatubu ilaika
0 comments:
Post a Comment