>>GUZURIN MANIYYATA AIKIN HAJJI<<<
wallafar : Mallam Abdus-salam Abubakar Ibrahim Rahimahullahu
Rubutu na hudu 04
بسم الله الرحمن الرحيم
A darasin yau zamuyi magana ne Akan hukunce hukuncen da suka shafi mata kawai a cikin aikin hajji. In baku manta ba a rubutu na uku mun dasa aya ne Akan bayanin Abubuwa da aka halasta ma mahajjaci yinsu, yanzu Zamu dora insha Allah.
ABUBUWA DA SUKA KEBANCI MATA KADAI.
1.samun dan rakiya kuma dolene ya zama miji ko mahaifi ko danu'uwa na haramcin aure ko tawaga amintatta.
2.Idon hajjin nafila ne to dole ne ta nemi izinin mijinta.
3.Ya halatta mace ta wakilci namiji wajen aikin hajji da umura hakanan ma namiji zai iya wakiltan mace.
4 . Idon jinin haila ya zama mace tana kan hanya zuwa aikin hajji to zata cigaba da tafiyarta koda ya sameta ne bayan harama zata cigaba da haramanta tayi dukkan ayyukan hajji banda dawafi, shikan sai tayi tsarki hakanan ma jinin haihuwa.
5.Ya halatta mace ta sanya turare a jikinta kafin harama. Wanda qanshinsa ba mai tsananiba.
6.A wajen yin niyyar harama dole ne mace ta cire niqabinta da burka'a da makamantansu.
7.Ya halasta mace ta sanya ko wane irin kaya da ko wane irin launi. Saidai ba mai bayyana tsiraici ba. Kuma ba mai ado ba.
8.Ya wajaba ga mace ta sassauta muryarta a wajen dawafi kuma ta nesanci cunkoson maza musamman wajen hajarul aswad da rukunul yamman, yin dawafin ta nesa da maza shi yafi idon hakan ya samu.
9. Sunnah ne mace ta dinga yin talbiyya gwargwadon yadda zata diyarda kanta, bazata daga muryarta ba kamar maza.
10.Dawafim mace da sa'ayinta duka tafiya ne ba sassarfa a ciki.
11. Idon mace tayi dawafi bayan ta gama sai jinin haila ya zomata ko na haihuwa, to zatayi Sa'ayi tsakanin safa da marwa, ba saita jira tsarki ba.
12.Ya halasta ga mata da tsoffi da yara da sauran masu rauni subar wurin Muzdalifa bayan Rabin dare domin suje suyi jifa don gudun cunkoson Jama'a.
13.wajen aski ko saisaye, mace zata rage gashin kanta ne gwargwadon kan dan yatsa, bazatayi aski ba ko saisaye.
14.Idon mace ta fara jinin al'ada bayan dawafin ifada to zatayi Sa'ayi idon akwai bashin Sa'ayin a kanta, shikenan saita tafi matuqar bai tsaya ba har zuwa lokacin zuwa gida bazatayi dawafin bankwana ba, kuma hajjinta yayi.
Anan zamu dasa alqalami InshaAllah a rubutu na biyar zamuyi bayani akan LOKACIN YIN HARAMA DA AIKIN HAJJI. da sauran mats'alolinda suka shafi harama
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.
Daga dan uwanku JAMEELU MASKA

0 comments:
Post a Comment