Kowane dan adam Yakan hadu da asarori guda biyu a rayuwarsa:Wato asarar dukiya da kuma asarar lokaci !! ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Wednesday 4 October 2017

Kowane dan adam Yakan hadu da asarori guda biyu a rayuwarsa:Wato asarar dukiya da kuma asarar lokaci !!

KOWANNE DAN ADAM YAKAN HADU DA
ASARORI GUDA BIYU ARAYUWARSA: WATO
ASARAR DUKIYA, DA KUMA ASARAR
LOKACI.


'Dan Adam yafi damuwa da asarar dukiya,
hankalinsa yafi tashi..
Gashi kuma ita
dukiya idan an rasa ta, ana iya samun wata
fiye da ita acikin Qankanin lokaci.
'Dan Adam bai damu da asarar lokaci ba,
alhali kuma ita ce asara mafi girma, wacce
har abada ba za'a iya mayar da gurbinta
ba.
Hakika lokaci shine babbar kadara mafi
muhimmanci wacce Mutum Mumini mai
hankali zai yi Qokarin cin ribarta aduk
bugun numfashinsa.
Tambaya???????????
Shin kina salloli ackn lokutansu?
Shin sau naya kike istigfari arana? (Remember Annabi <s.a.w> yana istigfari fiyeda sau 100 arana.
Shin sau nawa kikema Annabi (s) salati kullum? (Remember Allah da Mala'ikunsa babu wani second da suke hutawa wajen yima Annabi salati.
Shin kana kiyaye hakkin makota?
Shin kina yawan sadaka/zakka etc?
Shin kina tuna cewa duk tsawon zamani sai kabar duniya?
Yan uwa mu rage son duniya, domin mubada mahimmanci akan lokutanmu.
Allah yasa mu amfanu da lokutan wajen aikata ayyukan alkhairi domin samun tsira tun daga duniya zuwa lahira.
(ameen)


Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support