ABUBUWA MASU MUHIMMANCI DA WADANDA SUKA FI SU MUHIMMANCI
1. Abu ne mai muhimmanci iya karanta Alqur'ani da haddace shi
Amma mafi muhimmanci shine iya karanta shi, sanin ma'anarsa da kuma aiki da shi.
2. Abu ne mai muhimmanci biyawa Iyaye bukatunsu na yau da kullum, kamar dauko musu masu yi musu hidimar wanki, cefane, girki da gyara musu makwanci
Amma kayi musu hidimar da kan ka shine mafi alkhairi da samun albarka duniya da lahira, Allah yayi mana albarka Amiyn summa Amiyn.
3. Tsafta abace mai muhimmanci saboda tana daga imani
Amma tsaftace harshe da zuciya yafi muhimmanci.
4. Sana'a tana da muhimmanci, tunda kowane Annabi yana da sana'a babu cima zaune a cikinsu
Amma sanin yaya Manzon Allah (SAW) ya koyar da kasuwancin, kuma idan an samu halal ta ina ake kashe ta, shine mafi muhimmanci
5. Aure abu ne mai muhimmanci kuma sunna ce ta Annabawa, akwai rufin asiri mai tarin yawa acikin aure
Amma nemo mace tagari da kyautata niyya da kuma daukar shi a matsayin ibada shine babbar ribar shi duniya da lahira.
6. Kyawawan dabiu da haba-haba da mutane abu ne mai kyau da muhimmanci suna kai mutum Aljanna
Amma yiwa mutane uzuri, yi musu kyakkyawan zato, fadar alkhairi akan su a gabansu da bayan idon su shine mafi muhimmanci.
7. Mai da hankali wajen ibada abu ne mai muhimmanci, domin yin ibada shine kwanciyar hankalin mumini duniya da lahira
Amma yin ibadar bisa koyarwar Annabi Muhammad (SAW) da kuma yin ta da Ikhlasi shine mafi muhimmanci.
8. Karanta wannan sakon abu ne mai muhimmanci, saboda zai sa ka tuna abubuwan alkhairi
Amma yada shi ga mutane domin tunatar da su, shine mafi muhimmanci saboda zai iya zamanto sadaqa jariyah

0 comments:
Post a Comment