Wadanne azkaar ne Akeyi bayan salloli na farillah wadanda sunnah ta koyar ?? ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Tuesday 1 August 2017

Wadanne azkaar ne Akeyi bayan salloli na farillah wadanda sunnah ta koyar ??

```Assalamu alaikum
Tamabaya ta anan shine Dan Allah wadanne Azkaar ne akeyi bayan salloli na farillah wanda sunnah ta koyar?```


_*AMSA:*_
*******

وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،


Allah madaukakin sarki ya umarce mu da ambatonsa bayan mun idar da sallah. Acikin Suratun Nisaa'i, ayah ta 103, Allah yana cewa:

ﻓَﺈِﺫَﺍ ﻗَﻀَﻴْﺘُﻢُ ﺍﻟﺼَّﻼﺓَ ﻓَﺎﺫْﻛُﺮُﻭﺍ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻗِﻴَﺎﻣﺎً ﻭَﻗُﻌُﻮﺩﺍً ﻭَﻋَﻠَﻰ ﺟُﻨُﻮﺑِﻜُﻢ.........
*(النساء، 103)*

_*Sa'annan idan kun kare sallah, to Ku ambaci Allah tsaye da zaune da akan sansanninku.......*_
_*(Nisaa'i, 103)*_

Ya tabbata a sunnah karanta wadannan azkaar bayan gama Sallar farillah ko ta nafilah, acikin masallaci ko a wajen masallaci.

Ga azkaar din kamar haka:

ﺃﺳﺘﻐﻔﺮ ﺍﻟﻠﻪ   (Sau uku (3.

ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺃﻧﺖ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻭﻣﻨﻚ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﺗﺒﺎﺭﻛﺖ ﻳﺎﺫﺍ ﺍﻟﺠﻼﻝ ﻭﺍﻹﻛﺮﺍﻡ‏

Sannan ya juyo zuwa ga mutane idan liman ne ya fuskance su da fuskarsa.


Sannan ya karanta wannan, har mamu da mai sallah shi kadai suma zasu karanta wannan:

ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ
ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ، ﻟﻪ ﺍﻟﻤﻠﻚ ﻭﻟﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻭﻫﻮ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﺷﻲﺀ ﻗﺪﻳﺮ.


لا ﺣﻮﻝ ﻭﻻ ﻗﻮﺓ ﺇﻻ ﺑﺎﻟﻠﻪ.


ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻻ ﻧﻌﺒﺪ ﺇﻻ ﺇﻳﺎﻩ ﻟﻪ ﺍﻟﻨﻌﻤﺔ ﻭﻟﻪ ﺍﻟﻔﻀﻞ ﻭﻟﻪ ﺍﻟﺜﻨﺎﺀ ﺍﻟﺤﺴﻦ.


ﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﺨﻠﺼﻴﻦ ﻟﻪ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻭﻟﻮ ﻛﺮﻩ ﺍﻟﻜﺎﻓﺮﻭﻥ.


ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻻ ﻣﺎﻧﻊ ﻟﻤﺎ ﺃﻋﻄﻴﺖ ﻭﻻ ﻣﻌﻄﻲ ﻟﻤﺎ ﻣﻨﻌﺖ ﻭﻻ ﻳﻨﻔﻊ ﺫﺍ ﺍﻟﺠﺪ ﻣﻨﻚ ﺍﻟﺠﺪ.


Sannan bayan Sallar magriba da Asuba zai karanta:

ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ، ﻟﻪ ﺍﻟﻤﻠﻚ ﻭﻟﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻳﺤﻴﻲ ﻭﻳﻤﻴﺖ ﻭﻫﻮ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﺷﻲﺀ ﻗﺪﻳﺮ.
Sau goma (10).


Sannan bayan haka sai yace:

ﺳﺒﺤﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ      (Sau 33)

ﻭﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ       (Sau 33)

ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ.         (Sau 33)

          Sannan ya cika na dari (100) da wannan

ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ ، ﻟﻪ ﺍﻟﻤﻠﻚ ﻭﻟﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻭﻫﻮ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﺷﻲﺀ ﻗﺪﻳﺮ.


Sunnah ne ga liman da Mamu da Mai sallah shi kadai su bayyana wadannan azkaar bayan kowace Sallar farillah bayyanawa kadan kadan ba tareda daga sauti ba.

Ya tabbata acikin *Bukhari da Muslim* Daga *Ibn Abbas (radiyallahu anhum)* cewa lalle daga sauti a zikiri garin juyowa a fuskanci mutane a Sallar farillah ya kasance a zamanin _*Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam).*_


Baya halatta bayyanawar sauti a tare (kamar yadda wasu ke taruwa suyi group suna zikiri a tare), A'a saidai kowa yayi nasa shi kadai acikin ransa banda tarayya da sautin zikirin na kusa dashi. Domin shi zikirin jam'i bidi'ah ne wacce batada asali acikin tsarkakakkiyar shari'ah.


An shar'anta karanta *AYATUL KURSIYYU* a asirce ga liman da mamu da mai sallah shi kadai bayan sun sallame.
آية الكرسي

Sannan a karanta wadannan surorin sau 1 a Sallar Azahar, La'asar da Isha'i

ﻗﻞ ﻫﻮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﺣﺪ

قل ﺃﻋﻮﺫ ﺑﺮﺏ ﺍﻟﻔﻠﻖ

قل ﺃﻋﻮﺫ ﺑﺮﺏ ﺍﻟﻨﺎﺱ


Bayan magriba da Asuba kuma ana karantasu sau uku (3).

 ﻗﻞ ﻫﻮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﺣﺪ          (Sau 3)

ﻗﻞ ﺃﻋﻮﺫ ﺑﺮﺏ ﺍﻟﻔﻠﻖ     (Sau 3)

ﻗﻞ ﺃﻋﻮﺫ ﺑﺮﺏ ﺍﻟﻨﺎﺱ   (Sau 3)

Sannan zamu iya rokon wani abu na amfani ga rayuwarmu da kuma Neman gafara.

Sannan yana cikin sharuddan inganci na karbar addu'a shine yin salati ga *Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam).*

Allah ya karba mana ibadunmu ya kuma kara mana imani da ikhlaasi mai karfi.


والله أعلم،

***********************************


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.


_*🌙Tambayoyin*_ _*Musulunci🌙*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_6"
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support