NAU'O'IN TSARKI DA YADDA AKE YINSU
Da farko idan mutum zai shiga bandaki anso ya gabatar da kafarsa ta hagu sannan ya ce: " ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﺃﻋﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ ﺍﻟﺨﺒﺚ ﻭﺍﻟﺨﺒﺎﺋﺚ " “Bismillahi, Allahumma Inni a’uzu bika minal hubsi wal haba’isi” Ma'ana: "Da sunan Allah Ya Ubangiji ina neman tsarinka daga sharrin mazan aljanu da matansu". Sannan idan gayadi zai yi anso ya ja tufafinsa sosai sannan ya tsuguna akan kafarsa ta hagu ya saki duburarsa kada ya matseta kamar yadda Malam mai Risala yace: " ﻭﻳﺴﺘﺮﺧﻲ ﻗﻠﻴﻼ " “Wayastarhee Qalilan” Ma'ana: "Ya sassauta duburarsa kadan, to idan yagama biyan bukatarsa anso ya fara wanke bagirenda bawali yake fita, sannan ya kai ga wanke bagiren gayadi (duburarsa), anso yai amfani da hoge, wato dan karamin dutse ko wani abu mai kamadashi, kamar takarda wajen gusar da kazantar da take jikinsa kafin ya kai ga wankewa da ruwa. To bayan ya yi amfani da hogen kamar yadda aka ambata sai kuma ya bi da ruwa ya rika zubawa yana wankewa har sai ya tabbatar ya kawar da najasar dake jikinsa. Anan nema aka yi umarnin daya sassauta duburarsa don duk najasar da take boye ta fito don ya wanke ta baki daya. To bayan ya gama an so ya gabatarda kafarsa ta dama yayin fitowa daga bandaki yace: ( ﻏﻔﺮﺍﻧﻚ، ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺍﻟﺬﻱ ﺍﺫﻫﺐ ﻋﻨﻲ ﺍﻷﺫﻯ ﻭﻋﺎﻓﺎﻧﻲ " “Gufranaka, Alhamdu Lillahil Lazee Azhaba annil azaa wa’aafaanee” Ma'ana: "Ina neman gafararka ya Allah, godiya ta tabbata ga Allah wanda ya gusar min da abinda zai cutar dani ya warkar dani". ALLAH YASA MUDACE AMEEN
by: Hussaini Auwalu Ya'u. · 25 · August 25, 2017

0 comments:
Post a Comment