KADA KA RUDU DA IHUN DAFTA !!! ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Sunday, 27 August 2017

KADA KA RUDU DA IHUN DAFTA !!!

KADA KA RUDU DA IHUN DAFTA !!!

KADA KA RUDU DA IHUN DAFTA (kashi na daya) (Hukuncin aski da yankan farce gameyin lacca) Babu shakka malamai sunyi sabani akan mas'alar yin aski da yanke farce ga wanda xaiyi layya a cikin wadannan kwanaki na farkon watan zulhijjah. Har ixuwa maganganu guda uku kamar haka :- 1- Haramun ne gaduk wanda xaiyi layya yayi aski ko yayanke farcensa (kumba) a cikin wadannan kwanaki,matukar watan zulhijjah ya kama,wannan shine ra'ayin maxhabar hanabilah (hambaliyya) da wasu daga cikin malaman shafi'iyya,kuma shine ra'ayin Ishaq bn Rahuwaihi da Rabi'atur ra'ayi,haka kuma shine ra'ayin Dawud Azzahiriy da Ibn Hazm da Abussauriy da Auza'i,kuma haka akarawaito daga Sa'id bn Musayyib. 2- Mustahabbi ne mutumin da zaiyi layya kada yayi aski ko yankan farce,wato anfiso yabari sai bayan yayi layya kafin yayi askin ko yayanke farcen,wannan shine ra'ayin Imam malik da shafi'i da wasu daga cikin malaman hannafiyya,kuma shine ra'ayin Imam Hasanul Basri. 3- Ya halatta mutum yayi aski ko ya yanke farce,kuma suka ce kinyin aski ko yankan farce a cikin wadqnnan kwanaki ba wajibi bane kuma ba mustahabbi bane,wannan shine ra'ayin hannafiyya,kuma ra'ayin Laisu bn Sa'ad da Ikrima da Ada'u bn Abi rabah da Salim bn Abdullahi bn Umar dasauransu. ko menene abinda ko wane bangare na wadanan malamai suka dogara dashi na hujjah? wace maganace mafi inganci daga cikin maganganunsu? muhadu a rubutu na gaba cikin yardar Allah. ABBA ABDALLAH GWALE
by: Abu,abdurrahman Assalafy kano ·
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support