Masu hikima sunce ?? (fitowa ta 34) dr.mansur ibrahim sokoto ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Wednesday, 2 August 2017

Masu hikima sunce ?? (fitowa ta 34) dr.mansur ibrahim sokoto

MASU HIKIMA SUN CE

Fitowa ta 34

LABARIN SARKIN MUSULMI MANSUR DA WANI BAWAN ALLAH A MASALLACIN MAKKA

Wata rana Sarki Mansur yana cikin dawafi a dakin Allah mai alfarma, sai ya ji wani bawan Allah cikin masu dawafin yana cewa: "Ya Allah na kai karar masu girman kai da barance-barance, da masu hana masu gaskiya gaskiyarsu, da marasa tausayi masu kwadayi don son kai ba bisa gaskiya ba, gare ka. Da jin wannan magana sai sarki Mansur ya firgita kwarai, ya koma waje daya ya ce a kira masa wannan bawan Allah. Da manzon Sarki Mansur yazo, sai wannan bawan Allah ya yi raka'a biyu ya sumabanci Hajarul Aswad, yana mai sallama da duniya. Da isarsa wajen Sarki Mansur sai ya yi gaisuwa, ya ce, Allah ya taimaki Sarkin Musulmi. Sarki Mansur yace, me na ji kana fada ne? Hakika maganarka ta firgita ni sosai. Wallahi ta cika kunnuwana da abin da kwashe mini hanzari. Wannan mutum ya ce, idan ka ba ni aminci sai in fada maka ainihin abin da nake nufi. Sarki Mansur ya ce, an ba ka mana.
A nan ne fa wannan bawan Allah ya saki baki yana cewa :  "Ya kai Sarkin Musulmi! Ya kai Sarkin Musulmi bawan da nake nufi da maganata sai kai. Wa ya yi girman kai, ya yi barance-barance, ya hana masu gaskiya gaskiyarsu saboda kwadayi in ba kai ba?" Sarki Mansur ya ce, kai kuwa yaya zanyi kwadayi, ni da nake mallakar komai da komai, ban da mulkin Ubangiji? Bawan Allah ya ce, "Af! Da akwai mai kwadayinka kuwa a duk duniyar nan? Ba kai ne Allah ya ba kiwon bayinsa, da dukiyoyinsu, da mutucinsu ba? Amma sai ka fita daga harkarsu ka buya bayan dogayen gine-gine, ka kuma sanya masu tsaro marasa imani a tsakaninka da su? Sa'annan ka tura ma'aikatanka masu tara dukiya, ka ce kar wanda ya shigo maka sai wane da wane. Cikinsu kuwa ba ka sa wanda aka zalunce shi, da mai bukata, ko mai yunwa ba? Alhali kuwa babu wanda ba ya da alhaki a dukiyarka. Da wadanda ka yardar musu suka ga yawan buyarka ga jama'a ba mai ganin ka sai sun ce wannan ya ci amanar Allah, me zai hana mu ci tasa! Ko da ba su furta haka da baki ba kuwa ai aikinsu ya nuna haka. Ya zamanto sai wanda suka ga dama. Ta haka mutane suka ji tsoron su suka sallama musu, su kuma suka hau dukiyoyinsu da motocinsu, mutane kuma suka yi ta ba su dukiyoyinsu don su kubuta daga sharrinsu. Hakika kasarka dai ta cika da zalunci, kai kana can a boye, ba a gan ka ba balle kasan abin da duniya ta ke ciki. In ko an ganka ma, wa ya isa yi magana da kai?

Littafin: Sheikh Baba Ahmad As-Shinkidi

Fitarwa da gyarawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

9/11/1438
2/8/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support