YANZU-YANZU: Jirgin Shugaba Buhari na nan tafe gida Nigeria ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Saturday 19 August 2017

YANZU-YANZU: Jirgin Shugaba Buhari na nan tafe gida Nigeria

Bayan rahoton da aka smau cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai dawo gida yau, APC landan ta saki bidiyo da ke nuna jirgin gwamnati tana kokarin tashi
Da safiyar yau mun samu rahoton cewa shugaba Buhari zai dawo Najeriya yau Asabar, 19 ga watan Agusta.
Mun samu wannan rahoto ne daga bakin mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ta shafin ra’ayi da sada zumuntarsa na Facebook inda yace:
“ Shugaba Muhammadu Buhari zai dawo yau bayan ganawa da likita a Landan. Shugaban kasan ya bar kasa ranan 7 ga watan Mayu ne bayan mike ragamar mulki ga mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, wani ya zauna a matsayin mukaddashin shugaban kasa.
Ana sa ran shugaba Buhari zai yi magana da yan Najeriya misalign karfe 7 na safe ranan Litinin, 21 ga watan Agusta,2017."
Ya mika godiyarsa ga yan Najeriya wadanda suka sanya shi cikin addu’a tun lokacin da Allah ya jarabesa.
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support