MECECE LAYYA SHIN WAJIBICE KO SUNNAH? ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Sunday, 27 August 2017

MECECE LAYYA SHIN WAJIBICE KO SUNNAH?

*MECECE LAYYA SHIN WAJIBICE KO SUNNAH?*

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA:* Layyah : Itace Abunda ake yankawa na dabbobin ni'ima, a ranakun idi, saboda idin dan neman kusancin Allah, tana daka cikin Sha'a'ir Alamomin Musulunci, Alqur'ani da Hadisi duk sunzo da shar'antuwarta, da Ijam'in musulmi.

Allah madaukakin Sarki yace: Kayi Sallah don Ubangijinka, Kayanka abun layyar ka, dan shi...

A Sunnah, an karbo Daka Anas Bin malik Allah yaqara yarda dashi yace: Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yayi layya, da raguna guda biyu qosassu, wadanda ya yankasu da hannunsa ya Ambaci Sunan Allah yai kabbara,.

*Bukahri (5558) da Muslim (1966).*

Daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: Wanda ya yanka layyarsa bayan Anyi sallar idi, haqiqa yankansa ya cika, ya dace da Sunnar musulmai, .

*Bukhari (5545).*

Malamai Sunyi Sabani akan layya Dolece ko Sunnah ce.

Jamhur din malamai suntafi akan Sunnah ce mai qarfi, Masu wannan ra'ayin sune: *Shafi'iyya, da Malik, da Ahmad* a'abunda shine yafi shahara awajansu.

Wasu suntafi akan wajibice, Masu wannan ra'ayin sune *Mazhabar Abu hanifa a daya daka cikin ruwaya da'a samu daka gareshi,*

Shaikul Islam Ibnu taimiyyah ya zabi wannan magana, yace: shine daya daka cikin zantuka biyu a mazhabar Malikiyyah, ko shine zahirin Mazhabar imamu Malik.

Duba risala akan layya da zakkah ta Shaik Usaimeen rahimahullahu.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*

KARKU MANTA DA GAYYATO MANA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.


Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support