ABUBUWAN GUDA 24 DA RANAR JUMA'A TA KEBANTA DA SU AKAN SAURAN RANAKU ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Friday, 18 August 2017

ABUBUWAN GUDA 24 DA RANAR JUMA'A TA KEBANTA DA SU AKAN SAURAN RANAKU

_*⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖*_

_*ABUBUWAN GUDA 24 DA RANAR JUMA'A TA KEBANTA DA SU AKAN SAURAN RANAKU*_
➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖
_*1-Annabi s.a.w* ya kasance yana karanta: (ﺑﺴﻮﺭﺗﻲ ﺍﻟﺴﺠﺪﺓ ﻭﺍﻹﻧﺴﺎن ) Surar Sajada da Suratul Insan a sallar Asuba ta ranar Juma'a._

_2-Sallar Asubar Ranar Juma'a a Jam'I itace Sallah Mafificiya acikin Sallar mako._

_3-Mustahabbine Mutum ya yawaita yima *Annabi s.a.w.* Salati a daren juma'a da kuma yinin juma'a._

_4-Wajibancin Halartar Sallah juma'a acikin Masallacin juma'a da mutane suke haduwa dan yin Sallar juma'a._

_5-Yin Wankan juma'a sunnah ce mai karfi daga cikin sunnonin *Annabi s.a.w.*_

_6-Sanya Turare a ranar Juma'a yafi falala fiye da sanyawa a wata rana da ba itaba._

_7-Yin Aswaki a Ranar Juma'a Mustahabbancinsa yana kara karfi fiye da duk wata Rana da ba itaba._

_8-Halartar Sallar juma'a da wuri._

_9-Shagaltuwa da Karatun Alqurani da Zikiri da Addu'a._

_10-Wajibine Mutum yayi shiru dan sauraran Huduba. Domin magana lokacin da Liman yake Huduba yana iya sanyawa ka rasa ladar juma'a._

_11-Mustahabbine yin Sallar Gaisuwar Masallaci ga Wanda ya shiga Masallaci a Ranar juma'a koda Liman yana huduba ne._

_12-Mustahabbanci karanta daya daga cikin wadannan surorin ga Liman Lokacin Sallar juma'a:_
_*ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﻭﺍﻟﻤﻨﺎﻓﻘﻴﻦ ﺃﻭ ﺳﺒﺢ ﻭﺍﻟﻐﺎﺷﻴﺔ*_
_*Suratul: Juma'a ko Munafiqun ko Sabbi ko Ghashiyah.*_

_13-Ranar juma'a itace idi ta sati-sati. Dan haka yana da kyau bawa ya Girmama ta saboda Girman da *Allah* yayi mata._

_14-Mustahabbine mutum ya sanya tufafi mai kyau gwargwadon karfinsa, da kuma tsaftace masallaci da gyarasa._

_15-Mukaruhine Mutum yayi tafiyar barin gari bayan shigar lokacin Sallar juma'a. kuma lokacin Sallar juma'a yana shigane kafin zawali._

_16-Tafiya Masallacin juma'a da wuri kuma a kafa. Domin dacewa da ladar kowane taku zuwa Masallaci da kuma kankare zunubi._

_17-Ana kankare zunubai Ranar juma'a satin da yawuce da karin kwana Uku. kamar yadda Muslim ya Ruwaita._

_18-Acikin Yinin Juma'a akwai lokacin Amsa Addua na Musamman da babu wani bawa da zai roki *Allah* acikinsa face *Allah* ya amsa masa. Lokacin kuma shine bayan Sallar La'asar a zance mafi karfi._

_19-Ranar juma'a itace mafi alkhairin yini da rana take fitowa acikinsa. Acikinta ne *Allah* ya halicci *Annabi Adamu*. Kuma Acikinta ne Za'a tashi Alqiyama. Kuma kowace halitta tana razana a Ranar Juma'a in banda Mutum da Aljanni._

_20-Itace Ranar da *Allah* ya datar da wannan Al'umma ta *Annabi s.a.w* bayan sauran al'umma sun zabi wata ba itaba._

_21-Ana kyautata zato ga musulmin da ya rasu acikinta ko darenta. Domin yana samun kubuta daga tambayar qabari._

_22-Yin taku zuwa masallacin Juma'a yana daidai da Ibadar shekara guda da Azuminta da tsayuwar daranta._
_*@Saheehu Sunani Abu Dauda na Albany.*_

_23-Yawaita yin Sadaka._

_24-Gabatar da Sallar Juma'a da wuri._

_*✍🏼Mustapha Musa*_

KARKU MANTA DA GAYYATO MANA DA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support