LABARIN UMMU 'AMMARAH (RTA) ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Saturday 19 August 2017

LABARIN UMMU 'AMMARAH (RTA)



LABARIN UMMU 'AMMARAH (RTA)
***********************************
Wata Jaruma ce Sadaukiya, Mai Qarfin Jiki da Qarfin Imani.. Ta ciri tuta atsakanin Matayen duniya.. Tayi abinda Mazaje da dama suka kasa yi.

Sunanta Nusaibah bintu Ka'ab Al-Ansariyyah (Allah shi Qara mata yarda). Ana yi mata alkunyah da "Ummu 'Ammarah".

An haifeta agarin Madeenah, Kuma tana daga cikin farkon wadanda sukayi Imani da Allah suka gaskata Manzonsa (saww).

Ta halarci Bai'atul Aqabah (Mubaya'ar yarjejeniya wacce mutanen Madinah Sukayi ma Manzon Allah kafin yayi hijirah zuwa garesu).

Ta halarci Bai'atur Ridhwan Mubaya'ar da Sahabbai Sama da Dubu goma sukayi ma Manzon Allah (saww) akarkashin wata bishiya. Wacce nan take Allah ya karba, yace ya yarda dasu kuma ya basu Aljannah.

Ta halarci Yaqin Badar da Uhudu tare da Mijinta Zaidu bn Amru da 'Ya'yanta Habibu da Abdullahi.. Kuma ta halarci Yaqin Yamaamah. Wato Yaqin da akayi da 'Yan Riddah (Mutanen Musaylamah) azamanin Khalifancin Sayyiduna Abubakrin (rta).

Aranar Yaqin Uhudu ne ta nuna Jarumtakar da kowa yake labari.. Jarumtakar da har abada duniya ba zata mance da ita ba..

Aranar Yaqin Uhudu lokacin da Kafirai suka zagaye Muminai suna ta shahadantar dasu, Mazaje sun warwatse amma Ummu Ammarah tana tare da Manzon Allah (saww) Ta rike Takobi da garkuwa tana doke kafirai masu son chutar dashi (saww).

Annabi (saww) ya bada Shaida gareta yana cewa : "BAN WAIGA GEFEN DAMA KO HAGGU BA, FACHE SAI NA GANTA TANA YAQI DOMIN KARENI".

Ibnu Abdil Barri ya ruwaito cewa aranar Yaqin badar Ummu Ammarah ta samu nasarar kashe kafirai da dama. Acikinsu har da wani Qaton kafiri Mahayin doki. Ya zaburo dokinsa ya taho aguje domin chutar da Ma'aiki (saww) amma nan take Ummu 'Ammarah ta sokeshida Takobinta ta aika dashi lahira..

Imamul Waqidiy yace Ummu 'Ammarah (ra) tayi jinyar Sahabban da sukaji rauni aranar Uhudu. Kuma ita kanta ma taji raunuka har guda goma sha biyu. Acikin wadannan raunukan har da wani ajikin wuyanta wanda sai da tayi Jinyar Shekara guda kafin ya warke.

Tana kwance bata gama warkewa ba, sai taji Mai Shelar Manzon Allah (saww) yana gayyatar Sahabbai zuwa Yaqin nan na "HAMRA'UL ASAD". Tana jin wannan shelar sai ta tashi ta 'daura 'Damararta ta fito aka tafi da ita (Radhiyallahu 'Anha).

Hakanan bayan Ma'aiki (saww) ya bar duniya sai Qabilun Larabawan Kauyuka suka rika komawa kafirci. Wasu kuma suka rika hana zakkah. Don haka Sayyiduna Abubakrin (rta) ya rika tura rundunoni domin Yaqi da masu riddah. To acikin wadannan rundunonin babu wacce aka fafata Yaqi kamar wacce aka tura yankin Yamaamah domin yaqi da Makaryacin nan mai suna Musaylamah L. A).

To acikin wannan rundunar akwai Sayyidah Nusaybah Ummu 'Ammarah (ra) ta dauki Takobinta da garkuwarta ta fafata yaqi. Tayi Qokari sosai wajen kashe kafirai. Acikin haka ne har wani kafiri ya sareta a hannunta, hannun ya cire daga jikinta, ga kuma raunuka. Amma Ummu Ammarah bata dena Yaqi ba. Har sai da aka ci nasarar kashe babban kafirin wato Musaylamah.

Ya Allah ka Qara yardarka bisa Sayyidah Ummu 'Ammarah. Ka saka mata da alkhairi bisa hidimar da tayi ma Annabinka (saww).

Don Allah daliban Zauren Fiqhu muyi kokari mu raya sunan wannan babbar Jaruma. Duk wanda ya haifi 'Ya Mace ya sanya mata "NUSAIBAH UMMU 'AMMÁRAH".

Ita ce ta biyu ajerin Jarumai Mata da muka kawo (Bayan Ummu Waraqah). Kuma in shaAllah zamu ci gaba da zakulo muku tarihin irin wadannan jarumai.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (18-08-2017 26-11-1438).

Karku manta da gayyato mana abokananku zuwa wannan shafin mun gode
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support