```DA WANE HANNU ANNABI YA KASANCE YANA KIRGA TASBIIHI```
〰〰〰〰〰〰〰〰〰
*Zauren SA'ADATUL-MUSLIM*
.
_TAMBAYA:- السلام عليكم ورحمة الله ya malam don Allah tambaya ta itace da wane hannu Annabi صلى الله عليه وسلم ya kasance yana yin tasbiihi_
.
_AMSA:- وعليكم السلام ورحمة الله وبركاته to 'yar uwa Annabi صلى الله عليه وسلم ya kasance yana yin tasbiihi ne da hannun dama kadai! saboda hadisi ya tabbata dafa Abdillahi dan Umar رضي الله عنهما yace Naga Annabi صلى الله عليه وسلم yana kirga tasbiihi da hannun dama" (Iman Albany رحمه الله ya kawo wannan hadisin acikin sahih Sunan na Abu-Dawud hadisi na 1502)_
.
_Sannan Imam Nasirud-diinul Albany رحمه الله yana cewa "(Yin tasbiihi na hannun dama) shine sunnah domin haka shari'ar musulunci yazo dashi na shari'a daga gareshi, wato yana yin tasbiihi da hannun sa na dama kadai, don haka yi da hannun hagu ko kuma hannuwa biyu wato hagu da dama to wannan kakaf dinsu sa6a ma Annabi ne da kuma sa6a ma sunnah babu wani ingantaccen nassi da yazo da yake bayani akan wata falala dangane da wannan," (Duba Silsilatud-Da'eefah na Albani 1002)_
.
_Don haka dai yin tasbiihi da hannun hagu, ko kuma dama da hagu wannan bidi'a ce wofintatta wacce musulunci baisan da zaman taba, ayi da hannun dama kadai domin dacewa da Sunnah, Allah yasa mudace_
.
*Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga*
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp
0 comments:
Post a Comment