Duniya makaranta ! (fitowa ta 36) dr.mansur ibrahim sokoto ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Saturday, 5 August 2017

Duniya makaranta ! (fitowa ta 36) dr.mansur ibrahim sokoto

DUNIYA MAKARANTA

Fitowa ta 36

181. Tunaninka naka ne. Amma magana da zaran ka furta ta, to ta fita daga ikonka.

182. Duk wanda yake saurin amsa tambaya, lalle ne sai ya yi kuskuren bada amsa.

183. Duk wanda ya gudu daga aiki ya gudu daga hutu.

184. Kana da girma a idon mutane matukar ba ka nemi abin hannunsu ba. Da zzarar ka nema shikenan giramanka ya fadi.

185. Kudi ba su da amfani sai an kashe su. Idan an kashe su kuma ba za su dawo ba, sai dai a sake nemo wasu.

Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

11/11/1438
4/8/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support