MENENE SHARUDDAN YIN LAYYA? ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Sunday, 27 August 2017

MENENE SHARUDDAN YIN LAYYA?

*MENENE SHARUDDAN YIN LAYYA?*

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA:* Sharuddan layya guda shi dane.

Nafarko: Abunda za'ayi layyar dashi ya zama yana daka cikin dangin dabbobin ni'ima, Sune : *raqumi da saniya da awaki, tunkiya da akuya,*

Saboda fadin Allah madaukakin Sarki :

Kowacce Al'umma Mun sanya mata Abun yanka dansu Ambaci Sunan Allah Abisa Abunda ya Azurtasu dashi na dabbobin Ni'ima. *Suratul Hajji aya ta (43).*

Na Biyu: Abun layya ya zama yakai shekarun da aka iyakance ashari'a, ta kasance ta cika shekara daya idan akuyace ko taure, ko tacika shekara biyu idan tunkiyace ko rago, saboda fadin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam .

( Kada kuyanka layya sai wacce ta cika shekara saidai idan kunsamu quncin tattalin arziki saiku yanka jaz'ah daka jinsin tumaki.

*Muslim.*

Idan raqumine wanda ya cika shekara biyar zuwa sama.

Saniya wacce ta cika shekara biyu zuwa sama.

Tumaki ko akuyoyi wanda ya cika shekara guda.

Sharadi Na biyu dabbar layya ta Kubuta daka Aibuka wanda suke hana ayi layya da ita, guda hudune ga Sunan :

1- Harara garke wacce idonta daya yake akwai matsala, ko wacce idonta zai fari fat wanda ke nuna makanta qarara atare da ita.

2- Rashin lafiya bayyananniya, kamar zazzabi, wanda yake hana dabba kiwo, ko rauni qarara wanda yake lalata namanta, ko wanda yake da tasiri a lafiyarta, ko doguwar rashin lafiya da ta dade tanayi wanda yake mata tasiri a lafiyarta.

3- Gurguntaka mabaiyyaniya,

4- Wacce bata da Mai.

Wadannan Aibuka guda hudu sune suke hana ayi layya da dabbar da take da daya daka cikinsu.

Akwai wasu wadanda suke kamarsu koma suka fisu tsanani, layya bata halatta dasu ;

1- Makauniya wacce bata gani sam.

2-Wacce aka bata magani takecin Abunci sama da ikonta hartai qiba,

2-Wacce bata iya haihuwa da kanta.

4- Wacce ta fado daka saman wani abu ta samu illah,

5- Wacce bata iya tafiya, saboda cuta.

6- Wacce kafarta ta gaba ta guntule, ko ta baya.

Idan ka hada wadannan aibuka da guda hudun da suka gabata zakaga aibukan da suke hana layya da dabba sunkai guda goma.

Hakanan daka cikin sharuddan layya ta zama dabba mallakar mai layyace, ko kuma anyi masa izini yayi layya da ita,

Layya bata halatta da Abunda mutum bai mallakaba, kamar dabbar da akayi fashinta ko qwacenta, ko wacce aka sato, ko wacce akai qarya aka sameta, ko wacce akaiwa wani kirari na qarya ya bayar da ita, da maka-mantansu, domin bai halatta neman kusanci zuwaga Allah da sabo ba,

Layyar wanda aka baiwa kula da maraya tayi, idan yayita da dukiyar marayan, idan Al'ada ta zamto haka, kuma zuciyar marayan zata karaya idan ba'ayi layyar ba.

Haka layya ta hallata idan aka baiwa mutum wakilci, da dukiyar wakilin da izininsa,

Sharadi Na biyar : Kada Abun layya ya zama ya ta'allaqane da haqqin wani, layya bata halatta ga wanda akebi bashi, ya hana bashin yayi layya

Na Shida : Dole mai layya yayi layya a lokacin da aka iyakance, shine bayan sallar idi izuwa faduwar ranar uku ga Sallah.

Wanda ya yanka layyarsa kafin gama sallar idi, ko bayan faduwar ranar uku ga sallah, bashi da layya.

Amma Idan Wani uzurine yasa Mutum bai Samu damar yanka dabbar layyar saba har bayan faduwar uku ga sallah, Kamar wanda dabbarsa ta gudu batare da sakacinsa ba, bai sameta ba har bayan uku ga sallah,  ko wanda ya baiwa wani wakilcin yanka masa ya manta, babu laifi da wannan dan lokacin yin layyar ya wuce zaka yanka,

Qiyasi akan wanda yai bacci baiyi sallah ba koya manta Sallar, zai sallaceta idan yafarka ko ya tuna.

Ya Halatta yanka dabbar layyar cikin dare ko rana, yankawa da rana shine yafi, da kuma ranar idi bayan an sakko daka idin shine yafi falala..

Saboda gaggawa wajan aikata Alkairi.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*

KU KARANTA:- MECECE LAYYA SHIN WAJIBICE KO SUNNAH ??

Kuci gaba da kasancewa da wannan shafin www.duniyarfatawa.cf

KARKU MANTA DA GAYYATO MANA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.


Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support