Assalamu alaikum
Wai shin Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) Umrah nawa ya yi kafin ya bar duniya? Ba fa aikin hajji ba❌ no! Umrah
AMSA:
*******
وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ
An karbo Daga Qataadah cewa Anas (Radiyallahu Anhu) ya fada masa cewa Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) yayi UMRAH SAU HUDU dukansu acikin watan Zhul Qi'dah banda Umrah da yayi tareda Hajjinsa:
(Yayi) Umrah daga Al-Hudaybiyah ko kuma a lokacin Al-Hudaybiyah acikin watan Zhul-Qi'dah, (ya sake yin) Umrah a shekarar data zagayo acikin watan Zhul-Qi'dah, kuma (yayi) Umrah daga Ja'raanah lokacin da ya raba ganimar yaqin Hunayn acikin watan Zhul-Qi'dah.
(Bukhaari, Al-Hajj, 1654. Muslim, Al-Hajj, 1253).
Ibn Al-Qayyim yace; (Manzon Allah) yayi Umrah sau hudu bayan hijrah, Umrah hudu dukansu acikin Zhul-Qi'dah.
Ta farko itace Umrah ta Al-hudaybiyyah kuma itace ta farko acikinsu, a shekara ta 6 bayan hijrah, Amma mushrikai sun hanashi yakai ga daki (Ka'abah). Ya soke rakumansa na layyah a hudaybiyyah bayan an tare masa hanyar shiga Makkah, shi da sahabbansa sun aske gashin Kansu sannan sun fita harami, sun koma Madinah acikin wannan shekara.
Umrah ta biyu cikakkiyar Umrah ce a shekara ta 7 bayan hijrah lokacin da ya shiga Makkah ya tsaya ciki har (kwana) 3 sannan ya fita bayan ya kammala Umrah.
Umrah ta uku itace Umrah da yayi tareda Hajjinsa
Ta hudu itace Umrah daga Al-Ja'raanah, lokacin da ya fita yaqin Hunayn sannan ya dawo Makkah yayi Umrah daga Al-ja'raanah.
IbnAl-Qayyim yace babu sabanin ra'ayin malamai akan cewa Umrah hudu ne yayi
Duba:
(Za'ad al-Ma’aad, Mujalladi na 2, shafi na 90-93)
Al-Nawawi yace:
Malamai sunce: Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) wadannan Umrah ne acikin waan Zhul-Qi'dah saboda ya nuna falalar watan Zhul-Qi'dah, ya kuma rusa ra'ayin zamanin jahiliyyah da suke tinanin yin Umrah cikin Zhul-Qi'dah yana cikin mafi munin mummunan aiki.
Saboda haka Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) yayi Umrah har sau hudu acikin watan Zhul-Qi'dah saboda wannan itace gamsasshiyar hanyar nuna halaccin yin Umrah a watan Zhul-Qi'dah, da kuma nuna cewa tinanin jahiliyyah akan watan Zhul-Qi'dah karya ne.
(Sharh Muslim, 8/235)
والله أعلم،
***********************************
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.
🌙Tambayoyin Musulunci🌙
WhatsApp Group
0 comments:
Post a Comment