ILIMIN ABU HURAIRAH (RA)
****************************
Sayyiduna Abu Huraira (ra) yace : "Kuna cewa wallahi Abu Hurairah ya yawaita riwaya daga Manzon Allah (saww).
Kuma kuna cewa "Mai yasa Muhajirun (Mutanen Makkah) da Al-Ansaar (Mutanen Madeenah) basa ruwaito irin wadannan zantukan daga Manzon Allah (saww) ba?!."
Kuma Hakika Abokaina daga Almuhajiroon cinikayyarsu a kasuwanni ya dauke hankalinsu. Abokaina kuma daga Al-Ansaar, Lamarin gonakinsu da kuma kulawa da ita.
Ni kuwa mutum ne Miskeeni, nafi yawan zama tare da Manzon Allah (saww). Ina halartar wajensa yayin da su basu nan. Kuma nakan haddace abu yayin da su suka manta.
Kuma watarana Manzon Allah (saww) yana zantar damu sai yace "Duk wanda ya shimfida tufafinsa har na gama zancena sannan ya tattaroshi gareshi, ba zai ta'ba manta duk wani abinda yajishi daga gareni ba, Har abada".
Dpn haka sao na shimfida masa tufafina, (Ya zauna) ya zantar damu har ya tashi sannan na tattaroshi gareshi. To wallahi ban sake mantawa da duk wani abinda naji daga gareshi ba.
Hadisi ne Sahihi. Imamu Muslim da Baihaqiy ne suka ruwaitoshi.
QARIN BAYANI
***************
Lallai wannan Mu'ujizah ce mai girma daga cikin Mu'ujizozin Manzon Allah (saww), Kuma ta zama Karamah da girmamawa ga Abu Hurairah (rta). Domin kuwa duk cikin Sahabbai babu wanda ya kaishi yawan riwayoyi daga Manzon Allah (saww) duk da cewar zamansa agaban Manzon Allah (saww) bai wuce na shekaru uku ba.
Kuma alokacin daular Banu Umayyah, Marwan bn Alhakam ya ta'ba jarraba Abu Hurairah din (ra). Ya tambayeshi game da wasu Hadisai, Abu Hurairah din yana gaya masa. Ashe shi kuma ya sanya wani mutum ya rika rubutawa ba tare da sanin Sayyiduna Abu Hurairah din ba.
Sai bayan shekara guda sannan ya sake tambayarsa game da irin wadancan hadisan, Kuma ya sanya ana dubawa ko za'a samu kuskure daga yadda ya fadesu tun farko amma bai samu kuskuren ba.
Hakanan Sayyiduna Umar bn Al-Khattab (ra) shima ya jarrabashi ya tabbatar da Qarfin haddarsa.
Allah ya saka ma Sayyiduna Abu Hurairah (ra) da alkhairi. Hakika ilimai da yawa sun biyo ta hannunsa zuwa garemu, daga Manzon Allah (saww).
Lallai masu zagin Abu Hurairah (ra) da sunan wai addini sukeyi, to suna bisa kuskure mai girma. Domin Annabi (saww) ya bar duniya yana cikin yarda dashi. Kuma ya rayu amatsayin yardajje atsakanin sauran Sahabbai (ra) kuma Annabi (saww) yayi masa addu'a cewa Allah ya sanya soyayyarsa azukatan muminai.
Don haka Malamai suka ce duk wanda kaga yana Qin Abu Hurairah to ba mumini bane. Allah shi kiyayemu daga Qin Sahabban Annabi (saww) ko Ahlul Baiti (rta).
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (18-03-2017)

0 comments:
Post a Comment