DUNIYA MAKARANTA
Fitowa ta 34
171. Mutane uku ne suke kewaye da kai:
a. Mai son ka tsakani da Allah. Wannan ka mutunta shi.
b. Da makusancinka amma yana kyashin ka. Wannan ka yi hattara da shi.
172. Mai wa'azi ba shi yake hisabi ba, amma yana tuntar da kai cewa akwai hisabi a gaban ka.
173. Kada ka bayyana muranar ka a gaban wanda yake cikin damuwa. Kada ka fadi "yawan dukiyarka a gaban talaka. Kula da damuwar jama'a yana cikin alamun Imani.
174. Idan kana cikin jira, lokaci zai yi tsawo. Idan kana jin tsoro lokaci zai yi sauri. Idan kana ciwo lokaci zai yi nauyi. Idan kana cikin nashadi lokaci zai gajarta. Lokaci da yanayi a tare suke tafiya.
175. Abu uku ba su da amfani idan aka rasa abu uku:
a. Rayuwa idan babu lafiya
b. Da kudi idan ba a kyauta
c. Da magana idan ba aiki.
Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto
9/11/1438
2/8/2017
» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743

0 comments:
Post a Comment