YANDA YA DACE MUSULMI YA FUSKANCI KWANAKI GOMA (10) NA FARKON WATAN DHUL-HIJJAH (fitowa ta 9) ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Wednesday 23 August 2017

YANDA YA DACE MUSULMI YA FUSKANCI KWANAKI GOMA (10) NA FARKON WATAN DHUL-HIJJAH (fitowa ta 9)

*YANDA YA DACE MUSULMI YA FUSKANCI KWANAKI GOMA (10) NA FARKON WATAN DHUL-HIJJAH*

Fitowa ta 9

10. Azumi. Daga cikin ayyuka da shari'a ta yarda a yi a wadannan kwanaki akwai azumi kuma Mustahabi ne mutum ya azumci wadannan kwanaki tara (9) ko abun da ya sawwaka a gare shi, saboda hadisin da ya zo a cikin Sunani Abi Dawud daga Hunaid Bn Khalid daga Iyalinsa daga daya daga cikin Iyalan Manzon Allah, sallallahu 'alaihi wa sallama, ta ce: *_"Manzon Allah, sallallahu 'alaihi wa sallama ya kasance yana azumtar kwanaki tara (9) na watan Dhul-Hijja da ranar Ashura da kwanaki uku (3) na kowane wata da Litini na farkon wata da Alhamis"_*. A duba Abu Dawud 2437 kuma Sheikh Muhammad Nasirudden Albani ya inganta wannan hadisi a Sunani Abi Dawud 2129.

Wannan hadisi na cewa ya halatta a yi azumi tara tun daga farkon wannan wata ita ce fatawar Sheikh Bn Baz da Sheikh Muhammad Saleh al-Uthaimeen, Allah Ta'ala Ya yi musu rahama kuma ita ce fatawar Sheikh Abbaad, Hafizahullah da Lajnatud Daa'imah.

An karbo hadisi daga Abi Sa'id al-Khudriy, Radhiyallahu, Manzon Allah, sallallahu 'alaihi wa sallama ya ce: *_"Babu wani Bawa da zai yi azumin rana daya domin Allah, face a wannan rana Allah Ya nisanta fuskansa daga wuta na tsahon shekaru saba'in"_*. Muslim ne ya ruwaito 1153.

Nana A'isha, Radhiyallahu anha, ta ce: *_"A duk fadin shekara babu ranar da na fi son azumtar shi kamar ranar Arafa"_*. Baihaqee ya ruwaito a Sha'bu al-Iman 3475.

11. Sadaka. Allah Ta'ala Ya yabi masu yin sadaka da dukiyoyinsu a fili da boye.

Allah Ta'ala Ya ce: *_"Masu ciyar da dukiyarsu da dare da yini a fili da boye, to suna da sakamakonsu a wurin Ubangijinsu kuma ba su tsoro kuma ba su da bakin ciki"_*. Suratul Bakara aya ta 274.

Hadisi ya tabbata daga Abu Hurairah, Radhiyallahu Anhu, ya ce: Manzon Allah, sallallahu 'alaihi wa sallama ya ce: *_"Allah Ta'ala Ya ce: Ya kai Dan Adam!, ka ciyar da dukiyarka Ni ma zan ciyar da kai"_*. Bukhari ne ya ruwaito 4407 da Muslim 993.

Sannan kar mu manta daga cikin mutane bakwai da Allah Ta'ala Zai musu inuwa da al-Arshi ranar alkiyama akwai mutumin da ya ciyar da dukiyar shi domin Allah.

12. Layya.

Mu hadu a fitowa ta 10 in sha Allahu Ta'ala

✍🏼Dan uwanku a Musulunci:
*_Umar Shehu Zaria_*
22/08/2017.

Daga: *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

KARKU MANTA DA GAYYATO MANA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support