BAYANI AKAN MACE MAI TAKABA ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Thursday 24 August 2017

BAYANI AKAN MACE MAI TAKABA

*BAYANI AKAN MACE MAI TAKABA*

      DAGA ZAUREN
📕 *HISNUL-MUSLIM*📕

DARASI NA UKU 3

بسم الله الرحمن الرحيم

Alokacin da
mutun ya rasu, to zaibar iyalin shi a dayan
halaye biyu, kodai ta zama tanada Juna biyu ko
kuma bata da shi. Idan bata da juna biyu to
Takabarta itace "Wata hudu da kwana goma"
Kamar yadda Allah yace cikin Suratul-Bakara
"Kumma dukkanin mazan dake rasuwa daga
cikin ku subar matayansu, to matan zasu zauna
wata hudu da kwna goma" aya ta :234 To
amma idan ya rasu ya barta da juna biyu, a
wannan lokacin karshen Takabarta shine ta
sauke abinda take dauke da shi, koda ko ranar
da ya rasu ne, Misali ya rasu 7:00 na safe ita
kuma ta haihu 7:10 na safiyar, shi kenan ta
kammala takabarta, idan wani ya gani yace
yana so aka daura aure 2:30 na ranar aure ya
dauru(ana karbar gaisuwa ana daurin aure)
dalii kuwa shi ne. fadin Allah a cikin Suratut-
Talak aya ta 4 " Kuma dukkanin mata masu
juna biyu to lokacinsu shine su sauke abinda
suke dauke dashi" da kuma Hadisin Subai'a Al-
aslamiyyah, " Ita ta kasance tana auran Sa'ad
Dan Khaulah, shi kuma ya fito ne daga gidan
Amir dan Lu'ayy, yana daga cikin wadanda
suka halarci gwabzawar Badar, sai ya rasu
yabarta a hajin bankwana tana da juna biyu,
bata ko jima ba bayan rasuwar shi saita haihu,
a lokacin data kamma biki sai tai kwalliya, sai
Abu-Sanabil Dan Ba'akk yazo wurinta, shi kuma
ya fitone daga gidan Abduddar, sai yace da ita
" Lafiya naga kin cancara ado?

*zamu cigaba insha allah*

 DAGA DAN UWANKU
*ABDUL AZEEZ IBRAHIM*

*Masu buqatan shiga Wannan Zaure na hisnul Muslim   suyiwa daya daga cikin wadannan  number  magana ta whatsApp+2348065523065*
*+2348162067271*
    Domin Neman Karin bayani akan wata fatawa sai Ku kira wannan numbar↓
*+2347065588557*
سبانك اللهم وبحمدك، اشهد ان لا اله الا انت استغفرك واتوب اليك،
Kuna iya samun mu ta  facebook ta wannan link indanke Qasa
https://mobile.facebook.com/Hisnul-Muslim-667684316700356/?fref=none

KARKU MANTA DA GAYYATO MANA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support