BABU LAIFI GAME DA LAFUZAN DA AKE AMFANI DA SU CIKIN GAISUWAR IDI - Ibrahim jalo jalingo ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Saturday 26 August 2017

BABU LAIFI GAME DA LAFUZAN DA AKE AMFANI DA SU CIKIN GAISUWAR IDI - Ibrahim jalo jalingo

BABU LAIFI GAME DA LAFUZAN DA AKE AMFANI DA SU CIKIN GAISUWAR IDI
Daga Dr. Jalo Jalingo Abin da ke gudana a kan harsunan mutane na gaisuwar Idi, kamar: Allah maimaita mana, Allah nuna mana na shekara mai zuwa, Allah sa mu ga na badin-badada da kalmomi masu kama da wannan babu wani haramci a cikin yin hakan in sha Allahu Ta'ala; saboda hakan gaisuwa ce kawai tare da fatan alheri ita kuwa gaisuwa asalinta shi ne halacci; Allah Madaukakin Sarki Ya ce: (( ﻭﺇﺫﺍ ﺣﻴﻴﺘﻢ ﺑﺘﺤﻴﺔ ﻓﺤﻴﻮﺍ ﺑﺎﺣﺴﻦ ﻣﻨﻬﺎ ﺃﻭ ﺭُﺩُّﻭﻫَﺎ )) Ma'ana ((Idan aka gaishe ku da wata irin gaisuwa to ku yi gaisuwa da abin da ya fi ta kyau ko kuwa ku yi irinta)). Dilaalar wannan Ayar a fili take a kan abin da muka ce. Wannan shi ne ya sa a lokacin da aka tambayi Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah -kamar yadda ya zo cikin majmuu'ul Fataawaa 24/254- ((Ko abin da yake gudana cikin harsunan mutane na gaisuwar ranar Idi kamar cewa da suke yi: Idun Mubaarakun, da abin da ya yi kama da haka shin yana da asali cikin Shari'ah ko kuwa babu? Idan har yana da asali cikin Shari'ah to mene za a ce? Ku mana fatawa Allah Ya ba ku lada)). Sai Shaikhul Islam ya ba da amsa ya ce:- (( ﺃﻣﺎ ﺍﻟﺘﻬﻨﺌﺔ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪ ﻳﻘﻮﻝ ﺑﻌﻀﻬﻢ ﻟﺒﻌﺾ ﺇﺫﺍ ﻟﻘﻴﻪ ﺑﻌﺪ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪ : ﺗﻘﺒﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻨﺎ ﻭﻣﻨﻜﻢ، ﻭﺃﺣﺎﻟﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻚ، ﻭﻧﺤﻮ ﺫﻟﻚ ﻓﻬﺬﺍ ﻗﺪ ﺭﻭﻱ ﻋﻦ ﻃﺎﺋﻔﺔ ﻣﻦ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﺃﻧﻬﻢ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻳﻔﻌﻠﻮﻧﻪ، ﻭﺭﺧﺺ ﻓﻴﻪ ﺍﻷﺋﻤﺔ ﻛﺄﺣﻤﺪ ﻭﻏﻴﺮﻩ، ﻟﻜﻦ ﻗﺎﻝ ﺃﺣﻤﺪ : ﺃﻧﺎ ﻻ ﺍﺑﺘﺪﺉ ﺃﺣﺪﺍً، ﻓﺈﻥ ﺍﺑﺘﺪﺭﻧﻲ ﺃﺣﺪ ﺍﺟﺒﺘﻪ، ﻭﺫﻟﻚ؛ ﻷﻥ ﺟﻮﺍﺏ ﺍﻟﺘﺤﻴﺔ ﻭﺍﺟﺐ، ﻭﺃﻣﺎ ﺍﻻﺑﺘﺪﺍﺀ ﺑﺎﻟﺘﻬﻨﺌﺔ ﻓﻠﻴﺲ ﺳﻨﺔ ﻣﺄﻣﻮﺭ ﺑﻬﺎ ﻭﻻ ﻫﻮ ﺃﻳﻀﺎً ﻣﻤﺎ ﻧُﻬﻲ ﻋﻨﻪ، ﻓﻤﻦ ﻓﻌﻠﻪ ﻓﻠﻪ ﻗﺪﻭﺓ، ﻭﻣﻦ ﺗﺮﻛﻪ ﻓﻠﻪ ﻗﺪﻭﺓ . ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻋﻠﻢ )). Ma'ana: ((Amma gaisuwar ranar Idi watau sashinsu ya ce wa sashi idan ya hadu da shi bayan sallar Idi: Allah Ya karba mana Ya kuma karba muku, Ya kuma dawo mana da wannan yini shekara mai zuwa. Ko fadin wanin magana mai kama da haka, hakika an ruwaito daga sashin Sahabbai cewa sun kasance suna fadar hakan. Wani sashi cikin Shugabanni kamar Ahmad da wanin shi sun ba da damar fadin hakan, saidai Ahmad ya ce: ni ba zan fara gaya wa wani hakan ba, amma in wani ya gaya mini hakan zan amsa masa. Dalili kuwa a nan shi ne: Saboda amsa gaisuwa abu ne wajibi, amma fara gaida wani ba Sunnah ba ce da aka yi umurni da ita, ba kuma Sunnah ba ce da aka hana aikata ta. Saboda haka wanda ya yi irin wannan gaisuwar yana da Magabata da ya yi koyi da su, wanda kuma ya bar yin wannan gaisuwar shi ma yana da Magabata wadanda ya yi koyi da su. Allah Shi ne Mafi sani)). Allah Ya taimake mu har kullum. Ameen

Kuci gaba da kasancewa da wannan shafin www.duniyarfatawa.cf

KARKU MANTA GAYYATO MANA DA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support