SABUBBAN DAKE SA ALLAH YA RUFAWA BAWA ASIRI A GOBE QIYAMAH KO YA KUNYATA SHI
ألا تفضح مسلما ولا تفرح أبدا بفضيحته
Kada ka kunyata wani Musulmi kuma kada kayi farin ciki da kunyata shi.
لا تفرح بمصيبة أخيك فيرحمه الله ويبتليك.
Kada kayi farin ciki da musibar dan uwanka sai Allah yayi mishi rahama kai kuma ya jarrabeka da musibar(laifin).
ولا تسعى بأي طريقة فى فضيحة أحد وقع فى مصيبة.
Kada kayi gaggawa ta kowace hanya wurin kunyata wani da ya auka cikin musiba (sabo).
فباب التوبة مفتوح فلا تدري لعل الله يتوب عليه فيبقى عليك إثم نشر فضيحته.
Kofar tuba a bude yake, baka sani ba tuni shi Allah ya gafarta masa, kai kuma an lafta maka zunubin yada laifin sa.
فكلما استطعت أن تستر على مسلم فاستره.
A duk lokacin da ka samu damar rufawa musulmi asiri ka rufa masa.
Shiyasa Yazo cikin Sahihu Muslim hadisi na 2,590 daga Abu Hurairah (Allah ya kara masa yarda) cewa: Manzon Allah mai tsira da Aminci yace:-
لا يستر عبد عبدا فى الدنيا إلا ستره الله يوم القيامة.
Bawa ba zai rufawa wani Bawa asiri a duniya ba face Allah ya rufa masa asiri a gobe Qiyamah.
A hadisi na 2,699 cikin Muslim cewa Manzon Allah mai tsira da Aminci yace:-
ومن ستر مسلما ستره الله فى الدنيا والآخرة.
Duk Wanda ya rufawa wani Musulmi asiri to, Allah zai rufa masa asiri Duniya da Lahira.
Idan ka zama mai bibiyan laifukan mutane ko yada laifukan su to ga hadisi na 2032 cikin Sunan na Tirmizi, da Ibnu Hibban cikin Sahih hadisi na 5,763 cewa Manzon Allah mai tsira da Aminci yace:-
فإنه من يتبع عورة أخيه المسلم يتبع الله عورته، ومن تتبع الله عورته يفضحه.
Yadda lamarin yake duk Wanda ya bibiyi al'auran (laifin) dan uwansa Musulmi to shima Allah zai bibyi nashi al'auran (laifin), duk Wanda Allah ya bibiyi laifin sa to zai kunyata shi.
Allah ya rufa mana asiri gaba dayanmu Duniya da Lahira. Mankul.

0 comments:
Post a Comment