- An rahoto cewa jirgin shugaban kasa ya baro birnin Landan
- Tawagar labarai na shugaban kasar sun bayyana cewa basu da masaniya a kan wannan ci gaban
- A lokacin wannan rahoton babu tabbaci a kan tasowar jirgin
jaridar Vanguard ta rahoto cewa jirgin shugaban kasa dake Landan ya baro kasar a ranar 1 ga watan Augusta.
A cewar rahoton, baásan inda jirgin ya nufa ba wanda hakan ya janyo rudani a fadar shugaban kasar.
Fadar shugaban kasar ta karyata cewa bata da masaniya a kan wannan ci gaban kamar yadda hadiman shugaban kasa a shafukan labarai, Femi Adesina da Garba Shehu sukayi ikirarin cewa a dauki wannan labari a matsayin jita-jita.
Mista Femi Adesina wanda ya karyata cewa bashi da masaniya a kan haka a cewar Vanguard yace: “BBC ma ta kira ni sannan suka ce wai jirgin shugaban kasar ya tashi, na tabbatar da hakan. Nace masu aláda shine idan shugaban kasar zai dawo, zaá bukaci muyi sanarwa amma baá bamu wannan umurnin ba.
Vanguard ta kawo cewa “a daidai lokacin wannan rahoto a daren ranar Talata, babu tabbaci a kan cewa jirgin shugaban kasar ya bar Landan sannan kuma babu wani yunkuri a fadar shugaban kasar da zai tabbatar da jita-jitan”.

0 comments:
Post a Comment