>>GUZURIN MANIYYATA AIKIN HAJJI<<
wallafar Mallam Abdus-salam Ibrahim Abubakar Rahimahullahu
Rubutu na Biyu 02
السلام عليكم ورحمةالله وبركاته
A rubutu na 02 in baku manta ba mun tsaya wajen bayani ko Sharhi Akan hukunce hukunce da suka shafi barin wani rukuni daga rukunan hajji ko wani wajibi daga wajiban hajji, wayau zamu cigaba insha Allah.
ABUBUWA DA AKA HANA MAHAJJATA YNSU
1.Saduwa tsakanin miji da mata da abinda yake jawo saduwar
2. Neman aure da Daura Aure, ko Daurawa wani Auren.
3. farautar dabbar tudu ko taimakawa ga wanda zai farauceta ko koranta daga Inda take.
4.Sanya kaya dinkakku ga maza kamar Riga ko wando ko hula ko safa da makamantamsu.
5 . Rufe kai ga maza da abinda yake ta6a kai kamar hula da rawani da malafa da makamantamsu.
7.Sa turare a jiki ko a tufafi.
8.Aske gashi ko yanke qumba.
9.Rufe fuska ga mace da tafukan hannayenta kamar safar hannu ko nisabi.
QARIN BAYANI (TANBIHI)
Duk wanda ya aikata daya daga cikin wadannan Abubuwa da aka lissafa banda saduwa da Daura Aure da farauta, kuma yayi hakan cikin mantuwa koda rashin sani to babu komi a gareshi.
Inko da gangan ne to zaiyi fidiya yaciyarda miskinai shida ga ko wanne miskini Rabin sa'i wato mudunnabi biyu ko ya yanka tunkiya ya raba namanta ga miskinai a cikin Makkah ko a Inda yayi laifin.
Idon kuwa saduwa ne, in hakan ya faru ne kafin warware harami na farko to aikin hajjinsa ya 6aci. Kuma tilas ya soke raqumi ya rabawa miskinai, kuma ya cika aikin hajjinsa, kuma dole ya sake a wata shekara.
Idon ko ya rarune bayan warware harami na farko tilasne ya yanka tunkiya ya rabawa miskinai. Amma aikin hajjinsa yayi.
Amma Aure shi ba'a bada fidiya saidai a 6ata (warware) auren kawai domin bai inganta ba.
Amma wanda yayi farauta to tilasne yayi fansa da kwatankwacin dabbar da ya kashe daga cikin dabbobin gida watau Rakuma, Shanu, Tumaki, da Awaki
Alhamdulillah, anan zamu dakata sai rubutu na 04 zamuyi bayanin
ABUBUWA DA AKA HALASTAMA MAHAJJACI YINSU.
Daga Dan uwanku JAMEELU MASKA

0 comments:
Post a Comment