IDAN IDI YA KASANCE A RANAR JUMA'A TO BABU WAJIBCIN SALLAR JUMA'A A RANAR:- Dr.Ibrahim jalo jalingo ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Saturday 26 August 2017

IDAN IDI YA KASANCE A RANAR JUMA'A TO BABU WAJIBCIN SALLAR JUMA'A A RANAR:- Dr.Ibrahim jalo jalingo


IDAN IDI YA KASANCE A RANAR JUMA'A TO BABU WAJIBCIN SALLAR JUMA'A A RANAR: Idan idi ya kasance a ranar Juma'a to babu wajibcin sallar Juma'a a ranar; wannan hukuncin ne za a iya fahimta in aka yi kyakkyawan nazari cikin hadithai biyar da suka zo cikin wannan babin, hadithan kuwa su ne kamar haka:- (1) Imam Abu Dawud ya ruwaito hadithi na 1,070 da Imam Ibnu Majah hadithi na 1,326 da isnadi sahihi daga Iyas Dan Abii Ramlah ya ce:- (( ﺷﻬﺪﺕ ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ ﺑﻦ ﺍﺑﻲ ﺳﻔﻴﺎﻥ ﻭﻫﻮ ﻳﺴﺎﻝ ﺯﻳﺪ ﺑﻦ ﺃﺭﻗﻢ ﻗﺎﻝ : ﺃﺷﻬﺪﺕ ﻣﻊ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻋﻴﺪﻳﻦ ﺍﺟﺘﻤﻌﺎ ﻓﻲ ﻳﻮﻡ؟ ﻗﺎﻝ : ﻧﻌﻢ . ﻗﺎﻝ : ﻓﻜﻴﻒ ﺻﻨﻊ؟ ﻗﺎﻝ : ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻌﻴﺪ ﺛﻢ ﺭﺧﺺ ﻓﻲ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ، ﻓﻘﺎﻝ : ﻣﻦ ﺷﺎﺀ ﺍﻥ ﻳﺼﻠﻲ، ﻓﻠﻴﺼﻞ )). Ma'ana: ((Na halarci Mu'awiyah Dan Abii Sufyaan yana tambayar Zaid Dan Arqam ya ce: Ko ka halarci Idi biyun da suka hadu a rana guda tare da Manzon Allah? Sai ya ce: Na'am. Sai ya ce: to yaya ya yi? Sai ya ce: Ya yi sallar Idin sannan ya rangwanta yin sallar juma'a, ya ce: Wanda ya so yin sallar sai ya yi sallar)). (2) Imam Ibnu Majah ya ruwaito hadithi na 1,329 da isnadi sahihi daga Sahabi Abdullahi Dan Umar ya ce:- (( ﺍﺟﺘﻤﻊ ﻋﻴﺪﺍﻥ ﻋﻠﻰ ﻋﻬﺪ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ، ﻓﺼﻠﻰ ﺑﺎﻟﻨﺎﺱ ﺛﻢ ﻗﺎﻝ : ﻣﻦ ﺷﺎﺀ ﺍﻥ ﻳﺄﺗﻲ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﻓﻠﻴﺄﺗﻬﺎ، ﻭﻣﻦ ﺷﺎﺀ ﺍﻥ ﻳﺘﺨﻠﻒ ﻓﻠﻴﺘﺨﻠﻒ )). Ma'ana: ((Idi biyu sun hadu a zamanin Manzon Allha mai tsira da amincin Allah, sai ya yi wa mutane salla sannan ya ce: Wanda ya so tafiya juma'a to sai ya je ta, wanda kuma ya so zaman gida to sai ya zauna)). (3) Imam Abu Dawud ya ruwaito hadithi na 1,073, da Imam Ibnu Majah ya ruwaito hadith na 1,327 da isnadi sahihi daga Sahaabii Abu Hurairah cewa:- (( ﺍﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ : ﻗﺪ ﺍﺟﺘﻤﻊ ﻓﻲ ﻳﻮﻣﻜﻢ ﻫﺬﺍ ﻋﻴﺪﺍﻥ، ﻓﻤﻦ ﺷﺎﺀ ﺃﺟﺰﺃﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ، ﻭﺍﻧﺎ ﻣﺠﻤﻌﻮﻥ )). Ma'ana: ((Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: Hakika Idi biyu sun hadu a wannan rana taku wanda ya ga dama (hakan) ya isan masa yin juma'a, amma lalle mu za mu yi sallar Juma'a)). (4) Imam Abu Dawud ya ruwaito hadithi na 1,071 da isnadi sahihi daga Ataa Dan Abi Rabah ya ce:- (( ﺻﻠﻰ ﺑﻨﺎ ﺍﺑﻦ ﺍﻟﺰﺑﻴﺮ ﻓﻲ ﻋﻴﺪ ﻓﻲ ﻳﻮﻡ ﺟﻤﻌﺔ ﺍﻭﻝ ﺍﻟﻨﻬﺎﺭ، ﺛﻢ ﺭﺣﻨﺎ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﻓﻠﻢ ﻳﺨﺮﺝ ﺇﻟﻴﻨﺎ، ﻓﺼﻠﻴﻨﺎ ﻭﺣﺪﺍﻧﺎ، ﻭﻛﺎﻥ ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ ﺑﺎﻟﻄﺎﺋﻒ، ﻓﻠﻤﺎ ﻗﺪﻡ ﺫﻛﺮﻧﺎ ﺫﻟﻚ ﻟﻪ، ﻓﻘﺎﻝ : ﺃﺻﺎﺏ ﺍﻟﺴﻨﺔ )). Ma'ana: ((Abdullahi Bin Zubair ya yi mana salla cikin wani idi a ranar juma'a a farkon yini, sannan sai muka tafi juma'a sai kuma (a matsayinsa na liman) bai fito zuwa gare mu ba, (saboda haka) sai muka yi salla kowa shi kadansa. (a lokacin) Ibnu Abbas yana Taa'if to da ya dawo sai muka gaya masa abin da ya faru, sai ya ce: (Abullahi Dan Zubair) ya dace da Sunnah)). (5) Imam Abu Dawud ya ruwaito hadithi na 1,072 da isnadi sahihi daga Ataa Dan Abii Rabah ya ce;- (( ﺍﺟﺘﻤﻊ ﻳﻮﻡ ﺟﻤﻌﺔ ﻭﻳﻮﻡ ﻓﻄﺮ ﻋﻠﻰ ﻋﻬﺪ ﺍﺑﻦ ﺍﻟﺰﺑﻴﺮ، ﻓﻘﺎﻝ : ﻋﻴﺪﺍﻥ ﺍﺟﺘﻤﻌﺎ ﻓﻲ ﻳﻮﻡ ﻭﺍﺣﺪ، ﻓﺠﻤﻌﻬﻤﺎ ﺟﻤﻴﻌﺎ، ﻓﺼﻼﻫﻤﺎ ﺭﻛﻌﺘﻴﻦ ﺑﻜﺮﺓ ﻟﻢ ﻳﺰﺩ ﻋﻠﻴﻬﻤﺎ ﺣﺘﻰ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻌﺼﺮ )). Ma'ana: ((Ranar juma'a da ranar karamar salla sun hadu a zamanin Ibnu Zubair, sai ya ce: Idi biyu sun hadu a rana guda, sai ya hada su gaba daya ya sallace su raka'a biyu da safe, bai kara wata salla a kan su ba har ya yi sallan La'asar)). In aka kyautata nazari cikin wadannan hadithai za a fahimci cewa a duk ranar da Idi ya kasance ranar Juma'a, to sallar Juma'ar wannan rana ba ta zamantowa wajiba a kan al'ummar Musulmi. Wannan shi ne abin da ya bayyana a garemu, muna kuma sane da tattaunawar da Malamai suka yi game da mas'alar. Allah Ya taimake mu. Ameen.
by: Abu,abdurrahman Assalafy kano · 227 ·
August 25, 2017

KARKU MANTA DA GAYYATO MANA DA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.

KUKARANTA WANNAN:- Sheikh ahmed yayi tir da tsarin shugaban kasa buhari.

Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support