*BUSAR QAHON TASHIN ALQIYAMAH*
**************************************
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*_
Hadisi daga Sayyiduna Abu Hurairah (ra) yace "Watarana Manzon Allah (saww) yana tare da wasu daga cikin Sahabbansa, sai yace:
*"Hakika yayin da Allah ya kammala halittar sammai da Qassai, Sai ya halicci QAHO sannan ya badashi ga Mala'ika Israfeel (as).*
*Ya rikeshi acikin bakinsa, kuma yana kallon Al'arshi da idanunsa, yana jiran lokacin da za'a bashi Umurni".*
Sai Abu Hurairah (ra) ya tambayi Manzon Allah (saww) _"Ya Rasulallahi menene ma'anar kalmar_ *'SUUR'?"*.
Sai Manzon Allah (saww) yace *"Wani Qaho ne".*
Sai yace "To yaya kamanninsa yake?".
Sai Annabi (saww) yace *"Qato ne (yana da girma sosai) ina rantsuwa da girman Ubangijin da ya aikoni da gaskiya, Girman bakin wannan Qahon yakai kamar fa'din Sammai da Qassai. Kuma zai yi Busa acikinsa ne sau uku".*
- Na farkon shine *BUSAR GIGICEWA* (Wato busar da zata razana dukkan wadanda suke raye alokacin har sai sun fita daga hayyacinsu).
- Ta biyun kuma ita ce *BUSAR MUTUWA* (wato busar da zata sumar da dukkan rayayyu sanna daga nan akarbe rayukansu).
-Ta ukun kuma ita ce *BUSAR TASHI* wato tashi zuwa ga Ubangijin dukkan Kasantattu.
(Da farko) Allah zai umurci Israfeel yayi busar farko. Zai ce masa *"YI BUSAR NAN TA GIGICEWA".* Nan take sai dukkan Halittun sammai da Qassai su gigice (idan suka ji sautinsa) sai dai wanda Allah yaso.
Allah zai umurceshi ya tsawaita busar ba tare da gajiya ba. Ita ce busar da Allah yayi maganarta acikin Alqur'ani inda yake cewa:
*"BA KOMAI SUKE JIRA BA, FACHE WATA QARA GUDA 'DAYA WACCE BABU DAKATAWA AGARETA".* _(Wato har sai kowa da komai sun hallaka, in banda Zatin Ubangiji)._
Duwatsu zasu rika yawo kamar gajimarai, Zasu zama tamkar auduga. Kuma Qasa zatayi girgiza da Ma'abotanta. Zata zamanto tamkar jirgin ruwa wanda tuddai na ruwa ke bugunta har sai ta kifar da mutanen cikinta. Kamar wata fitila ce wacce take rataye ajikin kujera. Haka Zata girgiza rayuka!
Ita ce wacce Allah yake cewa: *"RANAR DA ZATA GIRGIZA, MUTUKAR GIRGIZAWA. WATA BUSAR NA BIYE DA ITA, ZUKATA AWANNAN RANAR SUNA CIKIN FIRGITA".*
Qasa zata girgiza da Mazaunan cikinta. Duk wata Mace mai shayarwa sai ta manta da abinda take shayarwa. Kuma duk wata wacce take dauke da juna-biyu sai ta zubar da abinda take dauke dashi (Ba zata san lokacin da zai zube ba, saboda tsananin halin da take ciki).
Jarirai zasuyi furfura arannan. Mutane zasu rika gudu domin tserewa daga wannan firgitar (Amma babu wajen gudu, babu matsera ko mafaka daga wajen Allah sai gareshi... SUB'HANALLAH).
Mala'iku zasu riskesu, suna bugunsu akan fuskokinsu har sai sun juyo! Zasu juya suna gudu, Basu da mai kwatarsu daga Allah.
Wasu daga cikinsu zasu rika kiran wasu (suna neman matsera).
Suna cikin wannan halin sai Qasa ta tsage gida biyu, tun daga wannan gefen zuwa wancan. Zasu ga wani al'amari na tashin hankali wanda basu ta'ba ganin irinsa ba..
Saboda wannan ne zasu shiga firgita da gigicewa irin wacce Allah ne kadai yasan iyakarta.
Zasu 'daga kai su kalli sararin samaniya, awanan lokacin ta zama tamkar wani tafasashen dagwalon Mai, (wato kamar narkakkiyar dalma mai zabalbala).
Sannan sai a tsaga sararin samaniya, Za'a kifar da taurari awatsar dasu. Da rana da wata duk zasu Kisife (Wato za'a tafiyar da haskensu).
Manzon Allah (saww) yace *"Amma Matattu ba zasu san komai daga cikin wannan ba".*
_*Abu Hurairah yaci gaba da cewa: "Amma wadanda Ubangiji ya kebance acikin ayar da yake cewa_ *"DUK WADANDA SUKE CIKIN SAMMAI DA QASSAI ZASU FIRGICE SAI DAI WADANDA ALLAH YASO".* To wadannan sune Shahidai. Domin ita wannan firgitar zata riski rayayyu ne kawai. Su kuma shahidai rayayyu ne awajen Ubangijinsu.
Kuma ana azurtasu, Allah zai kiyayesu daga firgicin wannan ranar. Zasu zama amintattu.
Ita wannan firgitar, wata azabar Allah ce wacce yake saukar ma mafiya munin halittu (wato Mutanen karshen zamanin duniya, wadanda zasu rayu tsawon shekaru 100 babu mai bauta ma Allah acikinsu. Kuma babu sauran 'ya'yan aure sai dai 'ya'yan Zina saboda yawaitar zinace-zinace har akan tituna da tsakiyar hanya ma yi suke).
Dangane da wannan Allah yace :
*"YA KU MUTANE! KUJI TSORON UBANGIJINKU! HAKIKA GIRGIZAR NAN TA LOKACIN (ALQIYAMAH) WANI ABU NE MAI GIRMA.*
*RANAR DA ZAKU GANTA, KOWACCE MAI SHAYARWA ZATA MANTA DA ABINDA TAKE SHAYARWA, KUMA KOWACCE MAI DAUKE DA JUNA ZATA HAIFE ABINDA TAKE DAUKE DASHI, ZAKA GA MUTANE SUNA TANGA'DI ALHALI SU BASU SHA ABUN MAYE BA, SAI DAI KAWAI AZABAR ALLAH TANA DA TSANANI NE".*
*(Suratul Hajji ayah ta 1).*
Anan zamu tsaya, sai acikin kashi na biyu zamu ji Qarshen yadda zata kasance.
*_Wannan hadisin yana nan acikin AN-NIHAYAH FIL FITAN WAL MALAHIM na Ibnu Katheer._*
*_Allah ya kyautata karshenmu. Allah yasa mu cika da imani._*
*AN GABATAR DA WANNAN KARATUN NE A ZAUREN FIQHU WHATSAPP -3 ARANAR 24-05-2016.*
KARKU MANTA DA GAYYATO MANA DA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.
0 comments:
Post a Comment