YANDA YA DACE MUSULMI YA FUSKANCI KWANAKI GOMA (10) NA FARKON WATAN DHUL-HIJJAH (fitowa ta 7) ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Monday, 21 August 2017

YANDA YA DACE MUSULMI YA FUSKANCI KWANAKI GOMA (10) NA FARKON WATAN DHUL-HIJJAH (fitowa ta 7)

*YANDA YA DACE MUSULMI YA FUSKANCI KWANAKI GOMA (10) NA FARKON WATAN DHUL-HIJJAH*

Fitowa ta 7

3. Zina. Wannan laifi ne mai girma da ya kamaci dukkan musulmi ya nisance shi a dukkan rayuwar shi ballantana a wadannan kwanaki masu albarka.

Allah Ta'ala Yana cewa: *_"Kuma kada ku kusanci zina, hakika ita mugun aiki ce kuma hanya ce wadda ta munana"_*. Suratul Israa'i aya ta 32.

Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce: *_Mai yin zina ba zai yi zina ba alhali yana mai imani, kuma barawo ba zai yi sata ba alhali yana mai imani, mai shan giya ba zai sha giya ba alhali yana mai imani"_*. Bukhari ya ruwaito 6772 da Muslim 57.

4. Sha ko siyar da kayan maye.

Hadisi ya tabbata daga Abid Dardaa'i, Radhiyallahu Anhu, ya ce: Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce: *_"Kar ku sha giya (duk wani abu mai bugarwa), domin ita ce mabudin dukkan sharri"_*. Muslim ne ruwaito 107.

Kuma Manzon Allah, Sallallahu' alaihi wa sallama, ya ce: *_"Duk wanda ya sha giya a duniya, to an haramta masa shan na lahira"_*. Bukhari ne ya ruwaito 5575 da Muslim 2003.

6. Nisantan zalunci. Daga cikin abubuwa da ya kamata mutum ya kula da su a wannan kwanaki shi ne nisantan zalunci.

Allah Ta'ala Yana cewa: *_"Kuma Azzalumai ba su da wani Majibinci kuma ba su da Mai taimako"_*. Suratush Shuraa aya ta 8.

Kuma Manzon Allah, sallallahu 'alaihi wa sallama, ya hane mu da zalunci inda yake cewa: *_"Zalunci daffai ne ranar al-Qiyamah"_*. Bukhari ne ya ruwaito 2447 da Muslim 2579.

7. Umurni da kyakkyawan aiki da hani da mummuna. Wannan siffa ce ta salihan bayi kuma aiki ne da Allah Ta'ala Ya fifita wannan al'umma da shi.

Khuzaifah, Radhiyallahu Anhu, ya ce: Manzon Allah, sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce: *_Ina rantsuwa da wanda raina ke hannun Shi ko dai ku yi umurni da kyakkyawan aiki kuma ku yi hani da mummuna ko ya yi kusa Allah Ya aiko da ukuba a kanku, sannan ku roke Shi ba zai amsa muku ba"_*. Tirmizi ya ruwaito 2199.

Manzon Allah, sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce: *_"Duk wanda ya yi kira zuwa ga alheri, yana da kwatankwacin lada na dukkan wanda ya bi shi, ba tare da range komai daga ladansu ba"_*. Muslim ne ya ruwaito 2674.

8. Ambaton Allah (zikiri). Daga cikin ayyukan alheri da mutum zai yawaita akwai yawaita Ambaton Allah.

Allah Ta'ala Ya na cewa:...


Mu hadu a fitowa ta 8 in sha Allahu Ta'ala

✍🏼Dan uwanku a Musulunci:
*_Umar Shehu Zaria_*
21/08/2017.

Daga: *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*


KARKU MANTA DA GAYYATO MANA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support