SHIN LAYYA WAJIBICE AKAN MAI AIKIN HAJJI? ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Wednesday 30 August 2017

SHIN LAYYA WAJIBICE AKAN MAI AIKIN HAJJI?

*SHIN LAYYA WAJIBICE AKAN MAI AIKIN HAJJI?*

الحمد لله سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA :*Malamai Sunyi sabani akan hukuncin layya akan mai aikin hajji, wasu sukace mustahabbice akan mai aikin hajji, wasu sukace babu layya akan mai aikin hajji..

Wadanda sukace babu layya akan mai aikin hajji sunyi sabani akan sababin rashin shar'antuwarta akansa abisa magan-ganu guda biyu:

Nafarko: Sukace mai hajji babu Sallar idi akansa, yankansa kuma shine hadayar tamattu'i, ko Qirani.

Na Biyu : Mai hajji matafiyine, layya kuma an shar'antawa mazaunin gidane, wannan shine maganar Abu hanifa, awajansa mai aikin hajji, idan dan cikin makkah ne shi ba matafiyi bane,  layya ta wajaba akansa.

Hanafiyyah sukace: Wajibice akan matafiyi da Mazaunin gida,  kamar yanda yazo  acikin *Al-Mabsuud (6/171).*

Yazo acikin *"Jauhara (5/285-286)"* Layya ba wajibi bace akan mai hajji matafiyi, amma wanda yake mazaunin makkah wajibice akansa koda zaiyi hajji.

Malikiyyah sukace: Babu layya akan mai hajji, saboda kasancewarsa mai hajji, ba saboda kasancewar sa matafiyi ba. Kamar yanda yazo acikin *Mudawwanah ( 4/101).*

Shafi'iyyah sukace: Layya Mustahabbice akan mai hajji

Imamu Shafi'i yace: Layya Mustahabbice akan mai hajji mazaunin makkah, da wanda ke kai kawo tsakanin gari zuwa gari, da Mazaunin gida,  da wajibice akan wasu banda wasu, da akan mai hajji zatafi zama dole, domin yankane, mai hajji kuma akwai yanka akansa, saidai bai halatta a wajabtawa mutane abuba saida hujja, babu ban-banci tsakaninsu.

*Al'Ummu (2/348).*

Ibnu hazam yace: Layya ga Mai hajji mustahabbice kamar yanda take akan wanda baije hajji ba, .

Wasu sunce babu layya akan mai hajji, Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya kwadaitar akan yin layyah, bai halatta a hana mai hajji falala da samun kusanci ga Allah ba, batare da wani nassi akan hakan ba.

*Al-Muhalla ta Ibnu hazam (5/314-315).*

Hanabila sukace:Layya ta halatta gamai aikin hajji.

Kamar yanda ibnu qudama acikin *Al-mugny (7/180)* Ya fada.

Hadisi yazo daka Aisha Allah yaqara mata yarda Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya yiwa matansa layya a mina ahajjin bankwana.

*Bukhari (5239) da Muslim (1211)* suka ruqaito.

Wasu malamai sunyi raddin hujja da wannan hadisin kamar ibnul qayyeem sukace: Abunda ake nufi da layya a hadisin shine hadaya.

Duba *zhadul Ma'adi (2/262-267)..*

Shaikul Islam da ibnul qayyeem sun zabi maganar masu cewa babu layya akan mai aikin hajji,.

Duba *Al'iqna'a (1/409) da Al-Insaaf (4/110)* Shaik Usaimeen ya rinjyar da wannan zancen..

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*


Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support