*YANDA YA DACE MUSULMI YA FUSKANCI KWANAKI GOMA (10) NA FARKON WATAN DHUL-HIJJAH*
Fitowa ta 8
8. Ambaton Allah (zikiri). Daga cikin ayyukan alheri da mutum zai yawaita akwai yawaita Ambaton Allah.
Allah Ta'ala Ya na cewa: *_"Da masu ambaton Allah da yawa maza da masu ambaton Allah da yawa mata, Allah Ya tanada musu gafara da lada mai girma"_*. Suratul Ahzab 35.
Abdullahi Bn Umar, Radhiyallahu Anhu, ya ce; Manzon Allah, sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce: *_"Babu wasu kwanaki (yinnai) mafiya girma a wurin Allah kuma mafi soyuwa a gare shi kamar wadannan kwanaki goma, don haka ku yawaita fadin: LAA ILAAHA ILALLAAH, ALLAHU AKBAR DA ALHAMDULILLAHI a cikinsu"_* Imamu Ahmad ne ya ruwaito a cikin al-Musnad 2/75.
Kabbara abun so ne sosai a cikin wadannan kwanaki.
Abdullahi Bn Umar da Abu Hurairah sun kasance suna fita zuwa kasuwa a cikin wadannan kwanaki suna kabbara sai mutane su rinka yin kabbara da kabbaransu. A duba Sahihul Bukhari babin da ya yi magana akan Falalar Ayyamut tashreeq hadisi na 11.
Dangane da kabbarbari da ake yi na bayan kowace sallan farilla har zuwa karshen Ayyamut tashreeq, Sheikh al-Islam Ibn Taimiyyah ya ce: *_"Magana mafi inganci dangane da kabbarbari wanda Malamai magabata da Sahabbai suka tafi a kai ita ce: ana fara wannan kabbara daga asubahi na ranar Arafa har zuwa karshen Ayyamut tashreeq a bayan kowace sallan farilla"_* a duba Majmu' al-Fatawa 24/20.
Game da yanda ake kabbarorin kuwa babu wani hadisi ingantacce daga Manzon Allah, sallallahu 'alaihi wa sallama, dukkan abun da ya zo daga ayyukan Sahabbai ne, Allah Ta'ala Ya kara yarda a gare su baki daya.
Daga ciki akwai Abdullahi Bn Mas'ud, Radhiyallahu Anhu, ya kasance yana kabbara: *"ALLAHU AKBAR! ALLAHU AKBAR! LAA ILAAHA ILLALLAH, WALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD"*. A duba Irwaa'u al-Ghalil.
Hadisi ya tabbata daga Abi Musa al-'Ash'ari, Radhiyallahu Anhu, daga Manzon Allah, sallallahu' alaihi wa sallama, ya ce: *_"Misalin mai ambaton Ubangijinsa da wanda ba ya ambaton Ubangijinsa, kamar rayayye ne da matacce"_*. Bukhari ya ruwaito 6407 da Muslim 779.
9. Karatun al-Qur'ani. Lallai daga cikin mafiya girman ibadu da ake neman kusancin Allah da su akwai karatun al-Qur'ani, musamman a cikin wadannan kwanaki masu albarka.
Allah Ta'ala Ya ce: *_"Hakika wandanda suke karanta littafin Allah suka kuma tsayar da salla suka ciyar daga abin da Muka azurta su a boye da sarari, suna burin yin cinikin da ba zai yi tazgaro ba. Domin Ya cika musu ladansu Ya kuma kara musu daga FalalarSa. Hakika Shi Mai gafara ne Mai godiya"_*. A duba Suratu Fadir aya ta 29 - 30.
Abiy Umamah, Radhiyallahu Anhu, ya ce: Manzon Allah, sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce: *_"Ku karanta al-Qur'ani domin zai zo ranar al-Qiyamah yana mai ceto ga ma'abotansa"_*. Muslim ne ya ruwaito 1337.
Abdullahi Bn 'Amru, Radhiyallahu Anhu, ya ce: *_"Za a ce ga ma'abocin al-Qur'ani karanta ka hau (Aljanna) kuma ka kyautata karatu kamar yadda ka kasance kana kyautatawa a gidan duniya, matsayin ka na karshe zai kare ne a aya ta karshe da ka karanta"_*. Tirmizi ya ruwaito 2838.
10. Azumi. Daga cikin ayyuka da shari'a ta yarda a yi a wadannan kwanaki akwai azumi kuma Mustahabi ne mutum ya azumci wadannan kwanaki tara (9) ko abun da ya sawwaka a gare shi, saboda hadisin da ya zo a cikin Sunani Abi Dawud...
Mu hadu a fitowa ta 9 in sha Allahu Ta'ala
✍🏼Dan uwanku a Musulunci:
*_Umar Shehu Zaria_*
22/08/2017.
Daga: *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*
KARKU MANTA DA GAYYATO MANA ABOKANANKU ZUWA SHAFIN MUN GODE.

0 comments:
Post a Comment