HUKUNCE-HUKUNCEN JININ HAILA:MEYE YA HARAMTA GA MAI JININ HAILA DA KUMA JININ HAIHUWA? ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Tuesday, 8 August 2017

HUKUNCE-HUKUNCEN JININ HAILA:MEYE YA HARAMTA GA MAI JININ HAILA DA KUMA JININ HAIHUWA?

HUKUNCE-HUKUNCEN JININ HAILA
***************007*******************
MEYE YA HARAMTA GA MAI JININ HAILA DA KUMA JININ HAIHUWA?
***************************************
Kamar yanda nayi maku bayanin ababe guda biyu da basu halatta ga mace mai jinin haila ko jinin biiqi su aikata ba acikin bayanan mu na 006 kuma aciki na kawo abu na uku amma saboda kada rubutun ya tsawaita yawa sai nace zamu maimaita matsala ta uku kuma muyi cikakken bayani akan ta, don haka sai mu bada himma wajen kiyaye dokokin Allah madaukaki kafin yayi fushi damu,  "Babu masu kafirce wa ayoyin Allah (a lokacin da ayar tazo masu) sai dai fasikai" (Baqarah aya ta 99)
.
3:-   SADUWA DA MACE:- Haramun ne saduwa da mace alhali tana yin jinin haila ko jinin biiqi (haihuwa) kamar yanda mukace maku zamu kawo maku dalilai daga Littãfin Allah ta'ala da kuma hadisan da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yayi hani da kuma maganganun malamai (magabata) akan wannan matsalar in shaa Allah, muna rokon Allah madaukakin sarki yataimake mu,
.
(1):-   "KUMA SUNA TAMBAYAR KA GAME DA HAILA KACE, SHI CŨTA NE, SABÕDA HAKA KU NĨSANCI MÃTÃ A LOKACIN DA SUKE HAILA KUMA KADA KU KUSANCE SU SAI SUNYI TSARKI, TO IDAN SUNYI WANKA SAI KUJE MASU TA INDA Allah YA UMURCE KU, LALLAI NE ALLAH YANA SON MÃSU TŨBA KUMA YANA SON MÃSU TSARKAKẼWA"  (Baqarah aya ta 222)
.
'Yan uwa kunga wannan aya ce karara da take nuna Haramcin saduwa da mace alhali tana yin jinin haila ko jinin biiqi (haihuwa) karara Haramun ne babu wani sassauci matukar saduwa ne to Haramun ne 'yan uwa don haka sai mu rike wannan ka'idar ta haramcin da nassin Al-Qur'ani, amma kuma ba'a hana kaba cewa tasan yanda tayi ta biya maka bukatun ka ba amma dai banda saduwa, abinda nakeso nace maka shine komai ajikin ta ya halatta a gareka sai dai banda Jima'ei, dalili kuwa hadisi ya tabbata acikin Bukhari da Muslim daga A'isha Allah ya kara mata yarda tace, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kasance  Yana umurta ta da nayi Qunzugu sai ya rungume ni alhali ina haila " (Duba Sahihu Muslim hadisi na 293, Bulughul-Maram shafi na 71 hadisi na 156).
.
Kuma akwai hadisi acikin Sahihu Muslim Daga Anas Allah ya kara masa yarda yace, lallai su yahudawa sun kasance idan matar su ta kasance tana haila acikin su, basu cin abinci tare dasu (Basu cin abincin su) sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace  "Ku aikata komai tare dasu amma banda saduwa"  (Duba Sahihu Muslim hadisi na 302, Bulughul-Maram shafin da mukayi ishara dazu hadisi na 155, Fiqhul-Muyassir na Sa'ad Yusuf shafi na 56) Haka kuma dai har wayau akwai hadisi da yake acikin sunan na Abiy-Dawuda daga Ikramah yace, daga sashin matan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, lallai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kasance idan yana bukatar wani abu a wajen matarsa alhali tana yin jinin haila, yana umartan ta ta tayi Qunzugu"  (Duba Sunan na Abiy-Dawuda hadisi na 242, Fiqhul-Muyassir shafin da mukayi ishara dazu) kuma ba'a kyamatar mata idan suna haila, duk wanda ya kyamaci mace saboda tana haila to ya dauko al'adar jahiliyya ya kawo cikin musulunci, wato ina nufin ya dauko aqeedun maguzawa ya kawo cikin addinin musulunci, wanda kuma ya rike wannan siffar to yayi kama da yahudu, Allah ta'ala ya tsare mu,
.
Duk wanda ya sadu da matar sa alhali tana yin jinin haila ko jinin biiqi (haihuwa) to ya sa6a ma Allah kuma ya sa6a wa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, haka kema idan kika amince masa kin sa6a ma Allah kuma kin sa6a wa Manzon Allah, ki karkade kunnen ki kiji ni yake  'yar uwa idan kina under jinin haila ko jinin biiqi mijin ki yazo maki to anan gurin Haramun ne kiyi masa biyayyah, kamar yanda mal Sa'ad Yusuf acikin Littãfin sa Fiqhul-Muyassir shafin da mukayi ishara dazu, yace   "Baya halatta ga mace ta amince wa mijin ta ya kwanta da ita Alhali tana yin jinin haila ko jinin biiqi, (idan ya nemeta kada ta kuskura tayi masa biyayyah) domin kuwa babu yin biyayyah ga abokin halitta a wajen sa6a wa mahalicci",
.
Wannan shine abinda Allah ta'ala ya kaddara min na kawo maku akan haramcin saduwa da mace alhali tana yin jinin haila ko jinin biiqi (haihuwa) Allah ta'ala ya bamu ikon kiyaye dokokin sa kamar yanda ya shar'anta mana, don haka yake 'yar uwa kiyi kokari ki nemi rubutun da suka wuce a baya matukar baki samesu ba tun daga 001 har zuwa 006, domin tanan ne zaki iya fahimtar ina muka dosa, kaima dan uwa kada kayi kasa a gwiwa, Allah ta'ala yayi maku albarka, Allah ta'ala yayi mana jagoranci, wannan shine karshen kaset na 007 kuma da yardan Allah acikin kaset na 008 da zai zo nan gaba zamuyi bayani ne akan HUKUNCIN WANDA YA KWANTA DA MATAR SA ALHALI TANA HAILA, Allah ta'ala muke roko ya kar6a mana, Allah yasa Mudace, Assalamu Alaikum warahmatullahi wabarakatuh
.
Hussaini Haruna Ibn Taimiyyah Abu-Nabeelah Kuriga
.
                   **17/10/1438**
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support