KURAKUREN DR. GUMI GAME DA HADISIN UMMU SALAMAH NA ASKI DA YANKE FARCE GA MAI LAYYAH !! Minbarin malamai ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Thursday, 31 August 2017

KURAKUREN DR. GUMI GAME DA HADISIN UMMU SALAMAH NA ASKI DA YANKE FARCE GA MAI LAYYAH !! Minbarin malamai

KURAKUREN DR. GUMI GAME DA HADISIN UMMU SALAMAH NA ASKI DA YANKE FARCE GA MAI LAYYAH

Na ga wasu faifan bidiyo guda biyu wadanda a cikinsu Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi yake cewa: -wai- Hadisin A'isha (ra) ya soke Hadisin da Ummu Salamah (ra) ta ruwato Annabi (saw) ya hana yin aski da yanke farce ga mai yin layyah idan watan Zul- Hijja ya kama.

To bayan mun nazarci maganar Dr., mun fahimci lallai akwai kurakurai a cikinta, daga ciki:

1- Kafin a yi Da'awar Hadisi kaza ya soke Hadisi kaza sai an tabbatar da cin karo a tsakaninsu, saboda asali babu karo tsakanin Hadisan guda biyu, saboda Hadisin A'isha (ra) a kan Hadaya yake magana, Hadisin Ummu Salamah (ra) kuma a kan Layyah yake magana. Don haka maganar a ce: daya ya soke daya ma ba ta taso ba.

2- Kuma ko za a sallama a kan akwai karo tsakaninsu to sai mu tambayi Dr. Gumi mu ce masa: Me Dr. yake nufi da "sokewa", a inda ya ce: Hadisin A'isha (ra) ya soke na Ummu Salamah (ra)?

In "Naskhu" yake nufi, wato soke hukunci, to muna so Dr. ya tabbatar mana da Tarihin Hadisan guda biyu, ma'ana; lokacin da kowane Hadisi ya faru, saboda akwai bukatar sanin Tarihi. Saboda ba za a ce: Hadisin A'isha (ra) ya soke na Ummu Salamah (ra) ba har sai an tabbatar cewa; Hadisin Ummu Salamah (ra) ne ya fara zuwa a farko, daga baya kuma Hadisin A'isha (ra) ya biyo baya.

In kuma ba sokewa na "Naskhu" Dr. yake nufi ba, "Tarjihi" yake nufi, to sai mu ce: ai kafin a isa ga "Tarjihi" sai an yi kokarin yin "Jam'i"; a hada Hadisan guda biyu a yi aiki da su gaba daya, kamar yadda Malaman Malikiyya suka yi, suka hada Hadisan biyu suka ce: MUSTAHABBI ne kar a yi aski, kar a yanke farce, a maimakon su ce: Wajibi ne.
Su ba "Tarjihi" suka yi suka jefa Hadisin Ummu Salamah (ra) a Bola ba, kamar yadda shi Dr. ya yi.

A baya an bayyana wa mutane hakikanin Mazhabar Malikiyya game da wannar mas'ala, inda muka ga cewa: magana mafi rinjaye a Malikiyya ita ce: MUSTAHABBI ne nisantar aski da yanke farce, ma'ana; yin aski da yanke farcen MAKRUHI ne ga mai layyah a cikin kwanaki goma na Zul- Hijjah.

3- In kuma "Tarjihin" za a yi sai mu ce:

(1) Hadisin A'isha (ra) gamamme ne (Aam), Hadisin Ummu Salamah (ra) kuma kebantacce ne (Khaas), a bisa ka'idar Malaman Usulul Fiqh: ana dora gamamme ne a kan kebantacce. Don haka sai a ce: komai ya halasta ga mai layyah, amma ban da aski da yanke farce.

(2) Hadisin A'isha (ra) aiki ne, Hadisin Ummu Salamah (ra) kuma magana ne, a bisa ka'ida ana gabatar da magana ne a kan aiki.

(3) Hadisin A'isha (ra) ya zo da lafazi guda biyu; daya a sake Mutlaqi, an ce: komai, daya kuma an kayyade shi da kusanar iyali. Bukhari da Muslim sun ruwaito daga A'isha (ra):
«لقد كنت أفتل قلائد هدي رسول الله صلى الله عليه وسلم، فيبعث هديه إلى الكعبة، فما يحرم عليه مما حل للرجال من أهله، حتى يرجع الناس»
صحيح البخاري (7/ 103)

"Na kasance ina tufka alamomin hadayar Manzon Allah (saw), sai ya aika da hadayar tasa zuwa Ka'aba (Makka), amma babu abin da yake haramta a gare shi na abin da ya halasta wa maza GAME DA IYALINSA, har sai mutane sun dawo".

Ga lafazin Muslim kuma kamar haka:
«أنا فتلت تلك القلائد من عهن كان عندنا، فأصبح فينا رسول الله صلى الله عليه وسلم حلالا، يأتي ما يأتي الحلال من أهله، أو يأتي ما يأتي الرجل من أهله»
صحيح مسلم (2/ 958)

"Ni ina tufka alamomin hadaya daga auduga da muke da shi, sai Manzon Allah (saw) ya wayi gari a cikinmu yana cikin halasci (ba mai haramar aikin Hajji ba), yana aikata abin da wanda ba ya cikin harama yake aikatawa GAME DA IYALINSA, ko cewa ya yi: yana aikata dukkan abin da mutum yake aikatawa GA IYALINSA".

Ma'ana; iyali ne Annabi (saw) bai nisanta ba.

Don haka, a bisa ka'idar Malaman Usulul Fiqh, ana dora Mutlaqin Nassi ne a kan kayyadadde, a hade Hadisan guda biyu a yi aiki da su gaba daya.
Shi ya sa Imamu Tahawiy ya ce:
فكان في هذا الحديث القصد بالذي كان رسول الله صلى الله عليه وسلم لا يجتنبه هو ما كان يجتنبه من أهله مما يجب على المحرم اجتنابه من أهله في إحرامه، لا ما سواه من حلق شعره، ولا من قص أظفاره، وذلك لا يمنع ما في حديث أم سلمة الذي رويناه، ويكون تصحيح ما رويناه عن أم سلمة، وما رويناه عن عائشة: أن يكون حديث أم سلمة على منع من أراد أن يضحي , وله ما يضحي , عن حلق شعره، وقص أظفاره في أيام العشر حتى يضحي، وحديث عائشة على الإطلاق لما سوى قص الأظفار، وحلق الشعر، له من تلك الأيام، وأنه فيها بخلاف ما المحرم عليه في إحرامه في تلك الأشياء كلها، حتى تتفق هذه الآثار كلها، ولا يضاد بعضها بعضا.
شرح مشكل الآثار (14/ 141 - 142)

Haka babban Malamin Malikiyya Ibnu Rushd (Kakan) shi ma ya ce:
وقد جمع بين الحديثين بعض من ذهب إلى الأخذ بحديث أم سلمة بأن قال: معنى حديث عائشة أنه لم يحرم على رسول الله - صلى الله عليه وسلم - شيء مما أحل الله له من أهله حتى نحر الهدي على ما جاء في بعض الآثار عنها وحرم عليه ما سوى ذلك من حلق الشعر وقص الأظفار على ما جاء في حديث أم سلمة.
البيان والتحصيل (18/ 166 - 167)

Wannan bisa fahimtar wadanda suka tafi a kan wajabcin nisantar aski da yanke farce kenan.

4- Kuma abin da ya fi shi ne mu dauki fahimtar Malaman da suka ce: WAJIBI ne kar a yi aski da yanke farcen, saboda yana daga cikin ka'idoji na kubutar Addinin bawa, mutum ya fita daga tsakanin sabanin malamai, gara ka dauki fahimtar Malaman da suka ce WAJIBI ne, don kar ka aikata ka wayi gari ka aikata Haramun.

5- Sa'annan kuma wani abin mamaki da Dr. ya yi shi ne rushe Hadisin Ummu Salamah (ra) da Qiyasi, inda ya nuna cewa: in za a yi aiki da Hadisin Ummu Salamah (ra) to kamar yadda ba za a yi aski ba, ba za a yanke farce ba, to haka ma kar a shafa turare, kar a yi jima'i. Alhali Dr. ya manta cewa: Qiyasi ba ya rushe Hadisi, kamar yadda ba ya yi masa "Naskhu" ya goge shi, kuma kamar yadda ba a Qiyasi a tare da Nassi. Duk wani dalibin ilimi ya san haka, balle kuma kwararre a Usulul Fiqh.

Don haka in Dr. ya ce: don me ya sa ba ku sa turare, ba ku nisantar jima'i kamar yadda kuke nisantar aski da yanke farce?
Sai mu ce: saboda Annabi (saw) bai hana turare da jima'in ba, alhali ya hana aski da yanke farce.

6- Daga cikin abin da Dr. ya fada ya ce: "A cikin Littatafan Mazhab, babu wanda ya ce: in za ka yi layya ka tsaya cikin datti".

Wannar magana ba dadai ba ce, saboda maganganun Malaman Malikiyya da aka kawo daga littatafan Mazhabar a rubutun da ya gabata mai taken: "HUKUNCIN ASKI DA YANKE FARCE GA MAI LAYYAH A MAZHABAR MALIKIYYA" suna karyata wannar magana.

Shiga nan ka karanta:
https://www.facebook.com/amyuguda/posts/1604515102945514?sw_fnr_id=3982568894&fnr_t=0

A ciki an kawo maganganun Malaman Mazhabar Malikiyya guda goma sha daya (11). Ga karin guda daya da ba a kawo a can ba. Al- Sawiy ya ce:
تنبيه: يندب ترك حلق الشعر من سائر البدن وترك قلم الأظفار في التسعة الأيام الأول من ذي الحجة لمن يريد الضحية ولو بتضحية الغير عنه
حاشية الصاوي على الشرح الصغير = بلغة السالك لأقرب المسالك (2/ 141)

"Fadakarwa: Mustahabbi ne barin aski a jiki gaba daya, da barin yanke farce a kwanaki taran farko na Zul- Hijjah ga wanda ya yi niyyar layya, ko da wani ne zai yi masa layyan".

Wannan shi yake nuna kuskuren maganar Dr. inda yake cewa; -wai- Fuqaha'u ba su yi aiki da Hadisin Ummu Salamah (ra) ba.
To a nan sai mu tambayi Dr. wadanne Fuqaha'un yake nufi?
Mu dai mun samu Malaman Malikiyya sun yi aiki da Hadisin, kai hasali ma Sahabbai (Salaf) sun yi aiki da shi kamar yadda Imamu Tahawiy ya ruwaito daga Qatada ya ce:
"إن كثير بن أبي كثير سأل سعيد بن المسيب: أن يحيى بن يعمر يفتي بخراسان - يعني كان يقول -: " إذا دخل عشر ذي الحجة، واشترى الرجل أضحيته، فسماها , لا يأخذ من شعره وأظفاره "، فقال سعيد: قد أحسن، كان أصحاب رسول الله صلى الله عليه وسلم يفعلون ذلك , أو يقولون ذلك".
شرح مشكل الآثار (14/ 142)

"Lallai Kathir bn Abi Kathir ya tambayi Sa'eed bn Al- Musayyab cewa; lallai Yahya bn Ya'amar yana fatawa a Khurasaan, yana cewa: {Idan kwanaki goman Zul- Hijjah sun shiga, mutum ya sayi layyarsa, ya ambace ta a matsayin dabbar layyah, to kar ya cire gashinsa ko farcensa}.
Sai Sa'eed ya ce masa: {Hakika ya kyauta, saboda Sahabban Manzon Allah (saw) sun kasance suna aikata hakan, ko cewa ya yi: suna fadan hakan}".

Don haka wannan yana karyata maganar Dr, kuma yana karyata fadinsa -wai- Sunna ba ta tafi a kan Hadisin ba.

Ta yaya za a ce: Sunna ba ta tafi a kansa ba, alhali ya tabbata daga Annabi (saw), Sahabbai sun yi aiki da shi, Malaman Fiqhun Mazhabobi sun aiki da shi in ban da Hanafiyya da Dr. Gumi?!

Saboda haka, alal akalli Malaman Malikiyya sun tafi ne bisa MUSTAHABBANCIN rashin yin aski da yanke farce a cikin wadannan kwanaki goma ga wanda ya yi niyyar yin layyah. Don haka mai so a bi Malikiyya a kan wannan ya kamata ya dora mutane.

Saboda haka, jama'a kar ku lura da maganar Dr. ku yi watsi da ita ku rike maganar sauran Malamai da suka ce MUSTAHABBI ne ko WAJIBI.

7- Sa'annan kuma siffanta wannan aiki na Shari'a, wanda aka shar'anta mana yinsa da cewa: "tsayuwa cikin datti" BABBAN KUSKURE NE, saboda in mun lura za mu ga rashin aski da yanke farce suna cikin aiyukan Hajji, aibanta wannan da kiransa da "tsayuwa cikin datti" yana lazimta aibanta aikin Hajji.

Sa'annan kuma me Dr. zai fadi game da Annabi (saw) da ya zauna ba aski ba yanke farce har tsawon kwanaki goma sha biyar (15), saboda ya yi harama a Zul- Hulaifa a ranar 24 ga watan Zul- Qa'ada. A'isha (ra) da Ibnu Abbas (ra) suka ce:
خرجنا مع رسول الله صلى الله عليه وسلم، لخمس بقين من ذي القعدة، لا نرى إلا الحج
صحيح البخاري (2/ 171) صحيح مسلم (2/ 876)

Annabi (saw) ya zauna cikin harami, babu aski ba yankan farce har zuwa ranar 10 ga Zul- Hijja ranar da ya yi aski, don haka za a ce: Annabi (saw) ya tsaya a cikin datti kenan?!

Saboda haka muna fatan Dr. zai zama mai lura da kalmomi da yake amfani da su yana sukan Hadisan Annabi (saw), "lawazim" dinsu munana ne matuka a Addini.

Allah ya kubutar da mu.
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support