1- Shugaban ya yaba da kokarin da Ministan watsa labarai da al'adu da kuma 'yan jarida sukeyi
2- Ya kuma yi magana akan lafiyarsa
3- Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya koyi bin Umurni yanzu
4- Sannan kuma yayi godiya ma 'yan Nijeriya kan Addu'ar da suke masa na samun lafia
5- Shugaban kasar yayi magana akan abinda akayi a Kasar Gambia
Shugaban kasa a yau ya sadu da mambobi na rukunin kafofin yada labaru,a jagorancin ministar tarayyar ma'aikatar watsa labaru da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, a gidan Abuja,London
Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yaba da kokarin da Ministan watsa labarai da al'adu Lai Muhammed da 'yan jarida sukeyi a kasar.
Shugaban Kasar ya ce:"Ina ganin ku a ko'ina ko a cikin jarida, yana da kyau sosai. Yana nufin cewa 'yan jarida da ma'aikatan watsa labarai suna aiki".
Bayan anyi masa tambaya akan lafiyar sa kuma ya shaida cewa ya ji sauki kuma zai iya dawowa yaci gaba da yin aikin da ya bari.A cikin bayanan sa:"Yanzu na ji sauki kuma ina jin zan iya dawo wa ziga zuwa kasata, amma na koyi bin umarni tunda ya zama dole nayi biyayya ga abin da likitoci suka fada mani.
Lokacin da aka fada masa game da addu'o'in da ake yi masa a ciki da wajen Nijeriya, shugaba Muhammadu Buhari a cikin farin ciki yayi godiya.
Ya kuma yi magana cewa "Abin da muka yi a Gambia a farkon wannan shekara ya kawo mana farin ciki a kan nahiyar Afirka.
Tawagar masu ziyaran sun kashe kimanin sa'a daya suna labari tare da shugaban kasar a kan matsalolin lafiyarsa da sauran al'amurran da suka shafi al'ummomi.
0 comments:
Post a Comment