Amfanin ruwan kokwamba guda 5 a jikin dan Adam ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Saturday, 12 August 2017

Amfanin ruwan kokwamba guda 5 a jikin dan Adam

Masana kiwon lafiya sun bayyana nau'ukan amfanin ruwan kokwamba a jikin dan Adam
Ruwan kokwamba ya zama sanannen ruwan sha ga ma su son gyaran jiki, amma ba hakan ya ke ba a wajen gama garin mutane sanadiyar rashin sanin fa'idar ruwan wajen kiwon lafiya managarciya.


Ga hanyoyi biyar da ruwan kokwamba zai amfani jikin dan Adam
1.Yalwar ruwa a jikin dan Adam
Ruwa wani muhimmin jigo ne wajen gudanar da al'amuran jikin dan Adam, ta yadda idan babu ruwa a jikin mutum zai tagayyara ya lalace. Adadin ruwa da ya kamata ace mutum ya sha a kullum ya na danganta ne da yanayin jiki zuwa jiki. Kofi 6 zuwa 8 na ruwan kokwamba zai samar da wadatacciyar lafiya a jikin dan Adam, duk da sanin cewa ruwa wani abu ne da ya ke gundurar mutum da zarar ya koshi, amma ruwan kokwamba zai sanya mutum ya yi ta neman kari saboda dandanon shi da ya banbanta da na ruwa.

2. Hana nauyin jiki
Ga duk wani mai son rage nauyin jikin shi, yin amfani da ruwan kokwamba ya na matukar taimakawa wajen inganta hanyoyin narkar da maiko a jikin dan Adam. Sau tari mutum zai rasa gane cewa yunwa yake ji ko kuma kishi, ta yadda mutum zai gane haka shine, ya samu kofi daya na ruwan kokwamba mai sanyi ya fara sha, idan yunwar ta gushe to daman kishirwa ce kawai amma idan yunwar ba ta gushe ba to lallai mutum zai gane cewar yunwa ce ke damun sa kuma sai ya nemi abinci.

3. Hana yaduwar cutar daji (kansa)
Kokwamba tana taimakawa wajen hana kamuwa da cutar daji sandiyar sunadaran cucurbitacins da lignans
wanda su ke hana kamuwa da cutar kansa wanda wasu ke kiranta cutar daji. Amfani da ruwan kokwamba yana rage yaduwar cutar kansa da ta ke kama 'ya'yan maraina na mazakutan namiji.

4. Rage hawan jini
Yin amfani mai yawa da gishiri wanda ya ke kunshe da sinadarin sodium ya na assasa gamuwa da cutar hawan jini. Ita kuwa kokwamba ta na dauke da sinadarin potassium
wanda yake wanko duk wani sinadarin na sodium
daga cikin kodar mutum wadda daman ita ce mai rarraba amfani na duk wani nau'in abinci da mutum ya ci. saboda haka shan ruwan kokwamba ya na kara sunadarin potassium a jikin dan Adam wanda yake taimakawa wajen hana samun cutar hawan jini.

5. Gyaran fata.
Ruwan kokwamba ya na sanya fata ta yi kyau fyas-fyas domin ga mai shan ruwan kokwamba to a koda yaushe jikin sa zai zama cikin wadaceccen ruwa don daman bushewar fat ita ke sanya fatar dan Adam ta lalace. Ruwan kokwamba ya na hankado duk wani dafi ko gubar da take jikin fata dan Adam kuma kokwamba ta na da sinadarin 'vitamin B-5' wanda ya ke magance kurajen fuska.
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support