KHUDBAR JUMA’A DAGA MASJID SALAFIYYA BIU BORNO STATE
Daga bakin 👇
SHEIKH ABUBAKAR BIN MUSTAFA BIU
Mai taken
DUKIYAR MARAYA GANIMAR WAWA
KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE
12/ZULQADAH/1438-HJRY
04/AUGUST/2017-MLDY
TOPIC= [DUKIYAR MARAYA-GANIMAR WAWA <4>]
¤¤¤¤¤ MABUDI ¤¤¤¤¤
Idan baku mantaba abaya mun gabatarda khudubobi guda 3 masu taken [DUKIYAR MARAYA-GANIMAR WAWA na <1> da na <2> da na <3>] inda muka ambato gabobi guda [[12]] yauma INSHA'ALLAHU zamu kawo kashi na <4> na khudubar inda zamu daura akanta=
[[13]] HANA CIN GADO:
Sabubban cin gado guda 3 (aure sahihi, dangantaka, waliccin 'yan tawa) da muka ambata akashi na (1) wadannan sabubban koda sun tabbata muddin in an sami sababi daya cikin sabubban hana cin gado guda 3 to fa babu cin gadon domin kowannensu yana iya rusa sababin gado,
((14)) SABUBBAN HANA CIN GADO GUDA 3 NE:
1- BAUTA: wani haline da mutum yake tsintar kansa aciki wanda bashida mallakar kansa ballantana yamallaki wani abu nasa, shi da abinda ya mallaka mallakar wanine, mai shi zai iya sayar dashi ko yakyautar dashi,
Shi kuma gado kamar yadda muka ambata akashi na <1> ALLAH ya kawoshi da harafin LAMUN ne don nuna mallakar abin ga wanda za'a bashi, shi kuwa bawa duk abinda kabashi ba mallakarsa bane mallakar ubangidansane, don haka idan aka bashi gado to an bawa bardene wato ubangidansa,
=daga dalilanda ke nuna bawa baya mallakannasa=
* ANNABI SAW yace "wanda yasayarda bawa alhali yanada dukiya to dukiyar tasa na mai sayarwanne sai in mai sayen ya sharɗanta" {BHR-2379 & MSLM-1543}
* Ya shahara wurin FUQAHA'U cewa= bawa da abinda hannunsa ya mallaka na shugabansane, wannan ya shafi kowane nau'in bawa.
2- BANBANCIN ADDINI: yana hana cin gadon juna,
* ANNABI SAW yace "kafiri bazai gaji musulmi ba hakama musulmi bazai gaji kafiriba" {BHR & MSLM}
* Hakama ALLAH ya Kore dangantakar jini tsakanin ANNABI NUHU A/S da kafirin ɗansa, ALLAH yace «YA NUHU lalle shi ɗannaka baya cikin iyalanka» (SRT HUD-46)
=Wannan shine MAZHABIN A'IMMAI guda 4- MALIK & SHAFI'I & ABU-HANEEFA & AHMAD RAHIMAHUMUL-LAAH sunyi aiki da zahirin wannan Hadisin,
* Wasu malamai kuma sun tafi akan cewa musulmi zai gaji kafiri amma shi kafiri bazai gaji musulmi ba, hujjarsu shine musulunci yana ɗaukaka ba'a ɗaukaka wani akansa, wannan shine Fahimtar SAHABI MU'AZ IBN JABAL R/A,
Amma maganarda yafi karfi shine maganar farko wato bazasu gaji junaba domin shine Hadisin ANNABI SAW ya nassanta karara kuma akanta JAMHURAN MALAMAI suke,
Amma MURTADDI wato musulminda yayi ridda- MALAMAI sunyi ijma'i cewa bazai gaji ɗan'uwansa musulmiba,
Amma shin shi musulmi zai gaji ɗan'uwansa da yayi ridda❓
* MALIKIYYA da SHAFA'IYYA da mafi ingancin magana a HANABILA= sunce wanda yayi ridda da ɗan'uwansa musulmi dukkansu bazasu gaji junaba tunda ya kafirta da riddansa kuma musulmi da kafiri baswa gadon juna, don haka dukiyar mai ridda ɗin FAY'U ne wato ganimane ga musulmai,
Wannan maganar shine zaɓin SHEIK TAQIYYUD-DEEN kuma yace- wannan ruwaya ce daga IMAM AHMAD kuma sanannene wannan daga SAHABBAI R/A,
* HANAFIYYA- AHNAAF= sun tafi akan dukiyar mai ridda na danginsa magada musulmai ne,
Wannan fahimtar an ruwaitota daga manyan SAHABBAI irinsu ABUBAKAR ASSIDDEEQ da ALIY IBN ABI ƊALIB da ABDULLAHI IBN MAS'UD R/A,
SHEIK MUH'D ALIY ASSABUNY yace- me yiwuwa wannan maganar shi yafi rinjaye don rashin samun tsararren Baitul Malin musulmai a wannan zamanin,
3- KISA: wanda yakashe makusancinsa kai tsaye ko shine sababin mutuwarsa to bazai gajeshiba,
* ANNABI SAW yace "wanda yayi kisa bashida komai daga gadon wanda yakashen"
* Akwai wata ƘA'IDAR FIQIHU dake cewa= <wanda ya gaggauta abu kafin lokacinsa- za'a masa uƙuba da hanashi abin> kunga shi wanda yayi kisan ya gaggauta cin gado ta hanyar kisa, sai adanashi gadon,
* A SURATUL BAQARA= wani a zamanin ANNABI MUSA A/S ya kashe baffansa don gado sai ALLAH yatona asirinsa sai yarasa gadon kuma yarasa ransa shima, (SRT BQR-55)
=HIKIMAR HAKA: Da ALLAH bai hana mai kisan kai gadoba- to da dayawa wasu zasu kashe iyayensu da makusantarsu masu dukiya don su gaje dukiyoyin, kunga hakan zai kawo barazana ga rayukan masu dukiya tsakaninsu da magadansu,
Kuma a gefe guda kisan kai babbar kyamatacciyar mummunar ta'addancine- kuma a shar'ance ko a hankalce bai dace ace ta'addanci ya zama silar samun ni'ima da dukiyaba, ta yadda har mai laifi zai mallaki dukiyar wanda yayiwa laifinba,
=NAU'IKAN KISAN DA MAGANGANUN MALAMAI AKAI:
* A MALIKIYYA= kisan ganganci kaɗai shi yake hana cin gado- amma koma bayansa baya hana cin gado, don haka wanda yakashe makusancinsa bisa kuskure zai biya diyya, sai araba gadon dukiyarda mamaci yabari abawa wanda yayi kisan gadonsa sai kuma araba gadon diyyar amma shi baza'a bawa wanda yayi kisan kwandala aciki ba,
Wannan shine maganar IBNUL-QAYYIM acikin I'ILAMUL MUWAQQI'EENA kuma yace- shine maganarda mukayi riko dashi- bayan ya kafa hujja da Hadisin ANNABI SAW cewa "idan ɗaya cikin ma'aurata yakashe abokin zamansa bisa kuskure- to zai ci gadon asalin dukiyarsa amma bazaici gadon diyyaba" {IBN-MAJAH}
Saidai BUSIRY da ALBANY sun raunata wannan Hadisin harma sunce MAUDU'I ne, Hakama IBNUL-JAUZY acikin ATTAHQEEQ da ABDU-HAQ acikin NASBUR RAYAH,
SHEIK SALIH UTHAIMEEN yace= inma za'ayi aiki da wannan ra'ayin tofa dolene asami hujja a fili da yake nuna kuskurene,
* A HANAFIYYA= kisanda yake hana cin gado shine kisan ganganci da mai kama da ganganci da na kuskure, domin sunyi aiki da ƙa'idar dake cewa= duk kisanda yake wajibtarda azumin kaffara zai hana cin gado, in bazai sa kaffara ba to bazai hana cin gado ba- shine kamar a kasheshi a matsayin ɗan fashi sauransu,
* SHAFI'IYYA= dukkan nau'ikan kisa suna hana cin gado, koda shaida yabayar akan tabbatarda hukuncin kisa kan wanda aka kashen to bazaici gadonsa ba, kamar misali= yana cikin shaidu 4 da suka tabbatarda shaida zina akan wani sai aka jefeshi akan hukunci da shaidunnan to bazaici gadonsa ba,
* HANMBALIYYA= duk kisanda yake lazimtarda kisasi ko diyya ko kaffara suna hana cin gado, amma koma bayansu baya hana cin gado,
SHEIK MUH'D ALIY ASSABUNY ya rinjayarda wannan cikin littafinnsa (ALMAWARITH)
* MALAMAN LUJNATUD DA'IMAH WAL BUHUTSUL ILMIYYATI WAL IFTA'I= wani ya tambaye su cewa yana tuka mahaifinsa acikin mota a wata dare sai gyangyaɗi yakamashi alhali yana kan tuki wanda hakan ya sabautarda juyawar motar da mirginuwarta wanda sakamakon haka nan take mahaifinnasa yarasu- shin shi dreban yanada kaso a gadon mahaifinnasane❓
LUJNATUH tace= in hakane bakada rabo a gadonnasa Saidai in magadan yazanto dukkansu sun mallaki daman tasarrufin dukiyar sukayi ittifakin baka dama araba gadon da kai tunda kayi sababin mutuwar babannakune acikin barci,
Dubi FATAWAR MALAMAN LUJNAH NA SAUDIYYA= fatawa mai lamba 3979,
ALLAHU A'ALAM,
RABBANA KASA MU RAYU RAYUWAR IMANI DA SA'ADAH,
KAKARƁI RANMU DA IMANI DA RAHAMA DA FUSKANTAR SA'ADA A KABARI DA ALJANNARKA A LAHIRA!
AMIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIN.
via Abubakar BN Mustafa Biu
Daga
ZAUREN FIQHUS SUNNAH

0 comments:
Post a Comment