LABARIN WANI WALIYYIN ALLAH - Zauren fiqhu ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Friday 25 August 2017

LABARIN WANI WALIYYIN ALLAH - Zauren fiqhu

LABARIN WANI WALIYYIN ALLAH
***********************************
Wannan wata Qissah ce wacce take kunshe da darussa masu yawa. Musamman akan abinda ya shafi Ikhlasi. Wato tsarkake nufi zuwa ga Allah (SWT) acikin dukkan komai.

DON ALLAH A KARANTA DA NUTSUWA:

Abdullahi ibn Al-Mubarak (rah) 'daya daga cikin magabata na kwarai, yace :

"Watarana na shigo cikin garin Makkah sai na iske mutane suna cikin fari (wato tsananin rashin ruwan sama). Na tarar dasu suba ta rokon ruwa acikin Masallacin harami.

Ni kuma ina daga cikin mutanen dake daf da kofar nan ta Banu Shaibah. Chan sai ga wani Bawa, baqar fata ya taho yana sanye da wasu tsummokara guda biyu ajikinsa. Ya daura guda daya yayi Kwarjalle dashi. Dayan kuma ya yafa akan kafadarsa.

Sai ya taho zuwa wani waje boyayye agefena, na jishi yana addu'a yana cewa :

"Ya abin bautana! Yawan zunubai da munanan ayyuka sun 'bata fuskoki.. Kuma gashi ka hanamu ruwan sama ne don ka ladabtar da halittu da wannan".

"Ina rokonka Ya Mahakurci Ma'abocin rangwame! Ya wanda bayinsa basu san komai daga gareshi ba, sai dai abu mai kyawu!... Ina so ka shayar dasu ruwa yanzu yanzun nan".

Ibnul Mubaarak yace "Wannan bawan Bai gushe ba yana cewa "Yanzu yanzun nan, Yanzu yanzun nan" fache sai da sararin sama ya cika da hadiri (Gajimare). Sai ga ruwa ta kowacce kusurwa".

"Ya zauna anan inda yake, yana ta yin tasbeehi. Ni kuma sai na fashe da kuka (saboda ganin yadda wannan bawan Allahn ya samu yardar Allah din).

Da ya tashi mai na bishi a baya. Har sai da na fahimci wajen gidan da yake. Sai na yafi wajen Fudhayl bn Iyaadh (abokina).

Ya tambayeni mai yasa na ganka acikin damuwa haka? Sai nace masa "Wani ya rigamu samun kusanci da Allah! Harma gashi nan Allah ya jibinceshi banda mu".

Da ya tambayeni "Yaya akayi haka ta faru?" Sai na bashi labarin dukkan abinda na gani.

Daga jin haka sai naji Fudhaylu yayi Qara! Ya fa'di Qasa. Sai yace mun "Kaichonka ya kai Ibnul Mubaarak! Rike hannuna ka kaini gareshi".

Sai nace "Ai yanzu lokaci ya Qure. Amma dai zanyi bincike akan sha'aninsa. Yayin da gari ya waye, bayan na sallaci Asubah sai na tafi wajen gidan nan (in da naga bawan nan ya shiga). Sai naga wani Dattijo abakin kofar gidan anyi masa shimfida yana zaune.

Yayin da ya ganni ashe ya shaidani. Sai yace "Maraba da zuwanka ya Kai Baban Abdurrahman! Mecece bukatarka?".

Sai nace masa "Ina bukatar wani Bawa ne, Baqar fata". Sai yace "To ai akwaisu da yawa awajena. Ka zabi duk wanda kake so".

Sai yayi kira, wani bawa ya fito Kakkarfa dashi. Sai yace min "To kaga wannan zai yi kyakkawan karshe. Zanso shi gareka".

Sai nace "A'a ba wannan ne bukatata ba". Bai gushe yana fito min da bayin nan 'daya bayan 'daya ba, har sai da ya fito min da wancan yaron nan (na jiya).

Yayin da na ganshi sai idona yayi haske. Yace min "Shin wannan ne?" sai nace masa "Eh shine". Sai yace "In dai wannan ne, to ba zan iya sayar dashi ba".

Nace ''Saboda me?". Yace "Saboda na albarkatu da zamansa anan gidan. Domin shi ba ya 'dora min nauyin komai".

Sai nace "To ta ina yake samun abincinsa?" Sai yace "Yana samowa rabin dirhami ko Qasa da haka kullum wannan shine abincinsa. Kuma yara (bayi) sun bani labari daga gareshi cewa shi ba ya yin barcin tsawon dare, kuma ba ya chudanya da wani daga cikinsu. Shi dai ya shagaltu da kansa ne. Shi yasa zuciyata take sonsa".

Sai nace masa "To zan koma wajen su Sufyanuth Thawree da Fudhayl bn Iyaadh ba tare da biyan bukatar nan ba?".  Sai mutumin yace "Ai tahowarka zuwa gareni ma abin girmamawa ne. Don haka ka karbi wannan bawan ka bayar da abinda kaso".

Don haka na sayeshi. Mun taho wajen gidan Fudhayl bn Iyaadh,  sai bawan nan ya kirani "Ya Ubangidana". Sai na masa "Labbaika!" sai yace "Kar kace mun labbaika. Domin bawa ne yafi chanchanta yace ma Ubangidansa Labbaika".

Sai nace masa "Mecece bukatarka Ya kai abin Qaunata?". Sai yace "Ni fa mai raunin jiki ne (bani da Qarfi). Ba zan iya hidimta maka sosai ba. Kuma zaka iya zabar wani wanda ya fini. Gashi an fito maka da wadanda suka fini Qarfin jiki".

Sai nace "Ai ba zanso Allah ya ganni ina hidimtar dakai ba. Sai dai ni yanzu zan saya maka gida kuma inyi maka aure, Sannan ni da kaina zan rika yi maka hidima".

Daga jin haka sai ya fashe da kuka. Da na tambayeshi dalili sai yace "Kai baka aikata wannan gareni ba, fache sai da kaga wani abu daga irin kebantuwata da saduwata da Allah madaukakin Sarki. In ba haka ba, don me zaka zabeni atsakanin sauran bayi?.

Da nace masa "ai baka da bukatar sanin wannan dalilin". Sai yace "Ina maka magiya da Allah sai ka bani labarin yadda akayi".

Sai nace masa "(Na zabi in sayeka in 'yantar dakai ne) saboda yadda naga addu'arka tana karbuwa (wajen Allah)". Sai yace min "Naga kai in sha Allahu kamar mutumin kirki ne. Kuma hakika Allah yana da wasu zababbu acikin halittunsa wadanda ba ya bayyanar da sha'aninsu sai dai ga wanda yake so daga cikin bayinsa. Kuma ba ya bayyanasu sai ga yardaddunsa".

Sannan ya tambayeni "Zaka iya jirana kadan, domin akwai wasu raka'o'in da suka rage ban sallacesu ba, tun jiya".

Sai nace masa "Ai ga gidan Fudhaylu nan kusa damu". Sai yace "A'a nafi so inyita anan. Umurnin Allah ne bai kamata in jinkirta ba".

Sai ya shiga masallacin harami bai gushe yana yin sallah ba har sai da ya sallaci abinda ya nufa, sannan ya juyo gareni yace "Ya kai baban Abdurrahman, shi kana da wata bukata ne? Domin ni ina son komawa ne". Nace "Zuwa ina?". Yace "ZUWA LAHIRA".

Sai nace "Kar kayi haka. Kar barni in samu farin ciki dakai''.

Yace "Rayuwa tana yin dadi ne alokacin da Mu'amala ta zama tsakanina da Allah Ta'ala ne kadai. Amma yayin da ya zamanto har kai ka gane halin da nake ciki, to da sannu waninka ma zai ganoni. Ni kuma bani da bukatar haka".

Daga nan sai ya fa'di yayi sujadah yana cewa "YA UBANGIJINA, KA KARBENI ZUWA GAREKA YANZUN NAN, YANZUN NAN".

Yayin da nayi sauri na matso gareshi sai na tarar har ya rasu. Wallahi ban ta'ba tunowa dashi ba, fache sai bakin cikina ya tsawaita. Kuma sai duniya ta kaskanta a idanuna".

ADUBA :

UYOONUL HIKAYAT na Ibnul Jawzee.

ALMUNTAZAM juzu'i na 8, shafi na 223 zuwa na 225.

Hakika labarin nan yana karantar damu cewar Allah yana da bayinsa yardaddu da yawa acikin talakawa da mutanen da ake ganinsu kamar basu da wani muhimmanci.

Gashi dai wannan din bawa ne kuma bakar fata, amma duk da haka ya samu shiga cikin fadar Allah. Har ma manyan Maluma irin su Ibnul Mubaarak suna kwadayin zama dashi.

Allah yana cewa : "MAFIYA GIRMANKU AWAJEN ALLAH, SUNE MAFIYA TSORON ALLAHNKU".

Manzon Allah (saww) yace "Balarabe bashi da fifiko bisa wanda ba balarabe ba, sai dai da tsoron Allah".

'Yan uwa har yanzu fa Qofa abude take. In dai kaji tsoron Allah ka nemi kusanci gareshi to lallai zaka samu yardarsa acikin dukkan sha'aninka.

DAGA ZAUREN FIQHU (18-08-2016) (15-11-1437).

KARKU MANTA DA GAYYATO MANA ABOKANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.


Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support