RANAR ARFAT ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Wednesday 30 August 2017

RANAR ARFAT

*RANAR ARFAT*

Babu wata RANA a wajen Allaah da tafi Wannan Rana ta *Arfa.*

A wannan rana ne Allaah Zai kusanto ga zuwa duniya, kuma zai zama yana alfahari da bayinSa na duniya wanan ranar.

An karbo Hadisi daga Ibn Hibban (RA), Cewa, ANNABI (SAW) ya ce, Allaah  Madaukaki, yakan saukowa saman duniya (sama ta 1), a ranar Arfa yana mai alfahari da bayinSa,
sai ya cewa mala'iku ku kalli bayiNa sun zo daga sassa na duniya daban-daban don su amsa kiraNa.

Sai Allaah (SWT) Ya tambayi mala'iku ya ce, me ku ka ji suna rokoNa game da shi? Sai mala'iku su ce mun ji suna rokon Aljannarka Ya Ubangiji.

Sai Allaah (SWT) ya ce dasu, shin sun ga Aljannar tawa ne? Sai su ce a'a ba su riga sun ganta ba, sai dai sun yi imani da cewa akwai ta.

Sai Allaah (SWT) Ya ce, ya ya ku ke gani inda a ce sun ganta? Sai su ce ya Ubangiji inda sun ganta da sun tsananta wajen neman Ka shigar da su cikinta.

Sai Allaah (SWT) Ya sake tambayarsu, me kuma ku ka ji suna neman na tsare su daga gareta? sai su ce, mun ji suna neman Ka tsaresu daga wutarKa Ya Ubangiji.

Sai Ya ce shin sun ga wutar ne? Sai su ce ba su ganta ba Ya Ubangiji, sai ya ce ya ya ku ke tsammani idan da a ce sun ganta?

Sai su ce Ya Ubangiji in da sun ganta da za su tsananta wajen neman Ka tsare su daga gareta. Sai Allaah (SWT) Ya ce, ina mai shaida muku cewa na gafarta musu.

 (Abu Ya’la, Ibn Khzayma, Al-Bazzar da Ibn Hibban).

A wannan Rana shaidan yake Raina kansa, a wannan rana cike zuciyarsa (Shaidan LA) take da bakin ciki.

Abu Ad-Darda ya rawaito Manzon Allaah (SAW) yana cewa babu ranar da Shaidan ya tsana kamar ranar Arfah, saboda a ranar ne yake raina kansa da kansa, an kaskantar da shi da ringa jin haushi. Dalilin jin haushin Shaidan kuwa a wannan rana shi ne saboda Ubangiji yana ‘yanta bayinSa da dama a wannan rana, babu wata ranar da ta kai wannan ‘yanta bayi sai dai ranar yakin Badr, wanda Ubangiji ya ‘yanta bayinSa da dama a wannan ranar, wannan ya sa Shaidan yake kasance cikin kunci a wannan rana.

★ Mafificiyar addu’ar da Mutum zaiyi a ranar Arfa ita ce:

ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ ،ﻟﻪ ﺍﻟﻤﻠﻚ ﻭﻟﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻭﻫﻮ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﺷﻲﺀ ﻗﺪﻳﺮ

LA’ILAHA ILLALLAHU WAHADAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI’IN KADEER.

Fassara:-
Babu abin bautawa da gaskiya sai Allaah, Shi Kadai, babu abokin tarayya a gare Shi.. Mulki nasa ne Shi Kadai, yabo ma nasa ne Shi Kadai, kuma Shi Mai iko ne akan komai.

Akwai azumi a ranar arfa, wanda Manzon Allaah SAW ya ce: azumin yana zama sanadiyar Allaah SWT Ya sharewa mutum zunubin shekara 2,

Kuma ana kar6a addu'a a wanan ranar

NB; Arfat zata fado ne a ranar lahadi 09/12/1438 daidai da 31/08/2017 in-shaa-Allaah

Ya Allah kasa mu dace da Alkheran da ke cikin Wannan Rana ta Arfat.

*© Dausayin Mutanen Kirki*


Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support