Shin wacce addu'a ce idan karoki Allah da ita yake gaggawar amsawa ??? ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Monday 14 August 2017

Shin wacce addu'a ce idan karoki Allah da ita yake gaggawar amsawa ???

```ASSALAMU ALAIKUM
Tambaya ta itace wacce addu'a ce idan karoki Allah da ita yake gaggawar amsawa.```



_*AMSA:*_
*******

وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،


A iya karamin ilimin mu bamu san wata kebantanciyar addu'a ba wacce *Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wa sallam)* ya koyar a karanta domin samun biyan bukata Cikin gaggawa. Sannan kuma bai halatta ga musulmi yayi addu'a yace yana son Allah ya biya masa da bukatarsa nan take, ko kuma a lokaci qayyadadde. Saboda Shi Allah ba'a sanya masa lokaci a biyan bukatar mai addu'a.

Amma mutum zai duqufa yana rokon Allah ya biya mass bukatunsa na alkhairi.

Addu'a itace makami mai kaifi da mumini/mumina zai/zata yi amfani wajen yanke duk wata matsala dake a gabansu.

Allah madaukakin sarki yana cewa acikin Al-qur'ani:

ﻭَﻟِﻠَّﻪِ ﺍﻷَﺳْﻤَﺎﺀُ ﺍﻟْﺤُﺴْﻨَﻰ ﻓَﺎﺩْﻋُﻮﻩُ ﺑِﻬَﺎ.

_*Allah yanada sunaye kyawawa Ku rokeshi dasu.*_

Manzon Allah ya koyar damu yadda zamu roki Allah da sunayensa kyawawa.  Kamar yadda yazo a ingantaccen hadisi kamar haka:

ﺃﺳﺄﻟﻚ ﺑﻜﻞ ﺍﺳﻢ ﻫﻮ ﻟﻚ ﺳﻤﻴﺖ ﺑﻪ ﻧﻔﺴﻚ، ﺃﻭ ﺃﻧﺰﻟﺘﻪ ﻓﻲ ﻛﺘﺎﺑﻚ، ﺃﻭ ﻋﻠﻤﺘﻪ ﺃﺣﺪﺍً ﻣﻦ ﺧﻠﻘﻚ ، ﺃﻭ ﺍﺳﺘﺄﺛﺮﺕ ﺑﻪ ﻓﻲ ﻋﻠﻢ ﺍﻟﻐﻴﺐ ﻋﻨﺪﻙ

Akwai wasu lokuta idan bawa yayi addu'a Allah na karba masa kai tsaye. Misali kamar sulusin dare na karshe kamar yadda ya tabbata a hadisi.

Yana daga cikin sharadin addu'a musulmi ya kasance *babu haram* a cikinsa (baici abincin haram ko abin sha na haram ba), musulmi ya kasance *bai yanke zumunta ba,* ya kasance *baiyi gaggawa ba,* kuma ya kasance ya *zabi kyakkyawan lokacin yin addu'a,* sannan ya nisanci *Neman gaggawar karbawa.* ya tabbata a hadisi cewa;

عن أبي هريرة قال، ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ: ﻳﺴﺘﺠﺎﺏ ﻷﺣﺪﻛﻢ ﻣﺎ ﻟﻢ ﻳﻌﺠﻞ، ﻳﻘﻮﻝ: ﺩﻋﻮﺕ ﻓﻠﻢ ﻳﺴﺘﺠﺐ ﻟﻲ.
*ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏(5865) ﻭﻣﺴﻠﻢ ‏(2735).*

_An karbo daga *Abu Hurayrah (R.A)* yace; *Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam)* yace: (Allah) yana karbawa dayanku (addu'arsa) matuqar baiyi gaggawa ba, (shine) yace nayi addu'a (amma har yanzu) ba'a amsamin ba._
_*(Bukhari, 5865.  Muslim, 2735).*_

Muna rokon Allah ya biya mana daukacin bukatunmu na alkhairi baki daya. Allah ka albarkaci al'ummar Musulmai a duk fadin duniya........Amin summa amin.



والله أعلم،

***********************************


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.


_*🌙Tambayoyin*_ _*Musulunci🌙*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_

Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support