*_WANENE IBN TAIMIYYAH_*
➖➖➖➖4⃣➖➖➖➖
★ Ga masu bukatar page dinmu sai su shiga wannan link din suyi like https://free.facebook.com/إبن-تيمية-رحمه-الله-136792630155923/?_rdr
.
_Idan muna tare acikin rubutun da muka gabatar, muna bayani ne akan jarabawar da Ibn Taimiyyah ya gamu da ita kuma mukace, A shekarar 705H lokacin da farin jinin Ibnu Taimiyyah ya gama bayyana, bayan an ga rawar daya taka a yaqin da aka yi da Tattar, har kuma ya samu kusanci da hukuma abin daya bashi damar har aka kawar da wasu 6arnace-6arnace Nan take sai qurjin hassada ya sake 6allewa a zukatan wasu malamai daga cikin sufaye. Sai wani malami da ake kira Nasrul Mambiji da wani malami bamalike ana ce masa Ibnu Makhluf suka tafi hedikwatar sarauta da ke qasar Masar suka kai qarar Ibnu Taimiyyah suna tuhumar sa da gur6ata aqidun jama’a. Suka kafa hujja da littafinsa na Al-Aqidatul Wasid'iyyah. A nan ma sarki ya bada umurni aka zaunar dashi tare da manyan malamai inda aka karance littafin nasa, daga qarshe kuma aka barrantar dashi daga sa6a ma magabata. Sai ma a wannan karon ya samu takardar yabo daga Sarkin Musulmi._
.
_Wata d'aya bayan faruwar wannan, sai wad'annan malaman suka sa sarki ya rubuta masa wata takarda ana neman sa da zuwa Misra don ya bayyana a gaban sarki. A wannan karon da tuhumar yana neman sarauta! An dai zaunar dashi a gaban Ibnu Makhluf don ya yanke masa hukunci, abin da Ibn Taimiyyan yaqi yarda da shi, kasancewar shi ne abokin husumar da ya kai qararsa, Shekhul Islam sai da ya share wata goma sha biyu cur a gidan kaso kafin a nemi ya fita, in da shi kuma ya qi fita yace, sai an bayyana masa laifinsa, Daga qarshe ya fita daga kurkukun bayan ya cika wata goma sha biyar da sati biyu bisa ga nacewar wani basaraken garinsu._
.
_Wata bakwai bayan fitowarsa sai aka sake mayar da shi a cikin watan Shawwal na 707H saboda yaci gaba da zama a Masar mutane na amfana dashi. A wannan karon sai ya kasance mutane suna tururuwa a gidan kaso don gaishe shi da yin fatawa a wurinsa, abin da ya dad'a cinna wutar gaba a tsakaninsa da wad'anda ke biyar sa da baqar yad'iya. Bayan fitowarsa ma, Ibn Taimiyyah bai fasa abin da yake yi na karantarwa da fallasa miyagun aqidu ba. Wannan ya sa aka dauke shi daga Alqahira zuwa Iskandariyyah da nufin ya hadu da ‘yan dabar garin su kashe shi. Ana haka ne sai aka samu canjin gwamnati lokacin da sarki Muhammad dan Qalawun ya sake koma ma kujerar sarauta sai ya mayar da Shehul Islam zuwa hedikwatar ta Masar. Daga nan kuma suka fita a shekarar 712H da nufin yaqar kafiran Tattar, sai Allah ya mayar da maqiyan garuruwansu ba tare da an yi yaqi ba Don haka, sai Ibnu Taimiyyah ya koma gida Sham, in da ya hadu da tarbo wanda ba a ta6a ganin irinsa ba, bayan yayi shekara bakwai da sati bakwai a qasar Masar tun wancan kiran da akayi masa._
.
_Ko bayan komawar sa gida Shekhul Islam yaci gaba da samun matsaloli da malamai masu qaramin sani da taurin kai. Kamar yadda suka yi cah a kansa wai don yace, in mutum yayi rantsuwar saki kaffara kawai zai yi, aurensa na nan, Haka ma don cewar da yayi saki uku na komawa d'aya idan anyi su a zama guda. Wad'annan malamai basu samu sukuni ba sai da suka sa aka hana shi fatawa a shekarar 719H. Zamu dakata anan sai mun hadu a darasi nagaba_
.
*Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga*
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp
Karku manta da gayyato mana abokananku zuwa wannan shafin mun gode.

0 comments:
Post a Comment